WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU

WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU Na bude wannan shafi ne don tarawa da adana Rubutattun Wakokina tare da takardu da na rubuta kan Rub

KA CIYAR A CISHE KADaga: Nasiru G. AhmadYawan ba da khairi arziƙinka yana daɗo,Yawan naɗe hannu aibu ne ba shi kyautuwa....
12/10/2022

KA CIYAR A CISHE KA
Daga: Nasiru G. Ahmad

Yawan ba da khairi arziƙinka yana daɗo,
Yawan naɗe hannu aibu ne ba shi kyautuwa.

Matse hannuwa bai sa wadata ta dawwama,
Ka zam basuwa in Rabbi ya ba ka ɗan uwa.

Bahili marowanci a kul ka zamo ka shi,
Ka ba mabuƙaci in ya zo ma da damuwa.

Talauci ka bar tsoron sa don ka yi kyautayi,
Ka san arziƙi Allah kaɗai shi ka basuwa.

Allah ne ya cancanci a tsoraci je masa,
Da hali na rowa don garai ba shi karɓuwar.

Ka san arziƙi yau gunka ne gobe gun wani,
Ka bayar a yau gobe ga kai za a basuwa.

A don haka in mai damuwa ya taho maka,
Ka bar ɗaure fuska ko batu mai tsanantuwa.

Ka san mawadaci mai yawan ba da taimako,
Abin son mutane har du'a'i suna yiwa.

Amma mawadaci wanda bai taimakon wani,
Kamar matsiyaci ne abin ƙi da ƙyamuwa.

A ya Rabbi ba mu arziƙi mai tabarraki,
Mu ci mu yi bayarwa gare ka mu bautuwa.

Muhammadu Nasir Ahmadu ya yi baitukan,
Cikin Hausa don ni har da ku mui faɗakkuwa.

09/09/2022

MUTUM

Daga
Nasiru G. Ahmad 'Yan awaki

1. Tsarki ya tabbata gun Rabbana,
Makagin mutum ya aje ban kasa.

2. Ya zam daukaka shi bisa khalkihi,
Dukan karramawarsa ya yi masa.

3. Ya saukar shari’a ta kyan rayuwa,
Ta gun Manzani da ya aiko masa.

4. Cikin dabi’unsa abin kyamata,
Kushe da son kai da nuna isa.

5. Da son shugabanta a duk lamari,
Nasa da naka ka zam bi nasa.

6. Duk yadda za ka yi sai ya musa,
Ya nuna ba haka ne so nasa.

7. In ka zamo mai shiga jama’a,
Zai ce kana shisshigi a kasa.

8. Da ka kebu ka kaurace rigima,
Zai ce kana kin mutane nasa.

9. In kai dariya sai ya ce ka nutsu,
Hawaye da ya zo ya ce murmusa.

10. In kai murmushi sai ya ce kai riya,
Da ka murtuke ka yi nuna isa.

11. Idan kai shiru sai ya ka gaza,
Ka yo magana sai ya ce ya isa!

12. In kai hakuri sai ya ce matsoraci,
“Ya rama mana in fa har ya isa!”

13. In ka ki bari har ta kwan sai ya ce,
Dukan lamura hankuri anka sa.

14. Ka ce a’a sai ya cane muskili,
Ka ce to ya ce bai da ra’ayi nasa.

15. Na tabbata yadda duk za ka so,
Yardar mutane fa ba ka isa.

16. Duk yadda za ka yi ba kubuta,
Zargin mutane na nesa kusa.

17. Abin duk da kai amanar haka ne,
Ka zartar abi naka kar ka gusa.

18. Muddin bai zamo shi abin hanuwa,
Wurin Rabbana da ka bauta masa.

19. Shi ke jaza’i ga bauta tasa,
Dukan arzikinmu yana gu nasa.

20. Shi ko mutum sai batu ya iya,
Da neman aza ka ga son rai nasa.

21. Ba duka anka zamo daya ba,
Akwai managarci a nuni nasa.

22. Wato aminin kwarai sadiki,
Mai son ka har zuci ba nakasa.

23. Wannan abin shawaranta yake,
Cikin lamura a bi zance nasa.

24. Sai dai fa samun sa kwai wahala,
Cikin zamanin yau a dukkan kasa.

25. Sai addu’ar Rabbi yai agaji,
Gare mu mu dace ga samu nasa.

26. Allah ya h**e mana sahibai,
Masoya gare mu da zati nasa.

27. Wadanda a ran tsayuwar mahsahari,
Mu samu rabauta da inwa tasa.

28. Albarkacinsa Abul Kasimi,
Mai son zumunci ga umma tasa.

29. Nasiru G. Ahmad yai batun,
Halin mutane fahimta tasa.

30. Baiti talatin a ran Alhamis,
Agustan Dubu Biyu sha Tara sa.

21, Zulhajji, 1440 (H)
22, Agusta, 2019

SHIRIN TAFIYA Daga Nasiru G. Ahmad 1. Tsarki ya tabbata gun Tabara Ubangiji, Ya Rabbi salli alaihi Manzon tsira. 2. Manu...
26/08/2022

SHIRIN TAFIYA
Daga
Nasiru G. Ahmad

1. Tsarki ya tabbata gun Tabara Ubangiji,
Ya Rabbi salli alaihi Manzon tsira.

2. Manufa ga baitoci tunatarwa ga mu,
Tafiyar da ke a gabanmu babu matsera.

3. Ya ɗan uwa mai ruɗuwa zam tuntunin,
Tsayuwar ƙiyama wadda ke da haɗurra.

4. In Nura (haske) ke kiran ka a duniya,
Kar ka sake gobe ka zam ba nura.

5. An yi hanin ka giya da cewa kar ka sha,
Ka bi umarnin har ka ce ban ƙara.

6. Amma fa kai tatul kana mayen giyar,
Zaluntakar bayi kana ta gadara.

7. Ba ka sha ta kwalbaye giya a ciki naka,
Ka maƙare shi da cin haram da ka tara!

8. Shin me ka shirya faɗi idan ka wai gari,
Ƙabari gaba naka Munkarin da Nakira?

9. Shin me ka shirya faɗi idan an tsai da kai.
Ƙasƙance nan a gaban Gwani Jabbara.

10. Domin hisabin ayyukan da ka aikata,
Mai kyau da dukkan sharrukan da ka ƙera?

11. Ga masu haƙƙoƙi da kai zaluntaka,
Sun zo biɗa ba za su bar maka zarra!

12. Ba za ka samu abin biya sai ayyuka,
Na ƙwarai da kai ko zunubansu ka ƙara.

13. Da ka mace an zam ƙabarce ka zamo,
Kai kai kaɗai sai ayyukan da ka tara.

14. Duk masu bin ka suna yabo da hidimtuwa,
Sun bar ka can ba wanda zai maka kara.

15. Ranar mutum zai gwammace bai shugaban-
ci ba idan ya ga nauyukan da ya tara.

16. Bayan zamowa mai isa mai ɗaukaka,
Rami abin ƙunci cikinsa ka tura.

17. Ya tashi ran tsayuwar ƙiyama zigidir,
Mai damuwar loton da ya yi asara.

18. Shin za ka yarda rayuwarka a ɗaukake,
Haske na zuci ya tafi ba saura?

19. Wato ya zam bautar jiki aiki naka,
Wannan da tsutsa za ta ci a ƙaburra!

20. Shin za ka yarda waninka ne zai ɗaukaka,
A cikinta Aljanna da matan Hura.

21. Kai ko kana can a ƙuƙumce Zabaniya-
wa na bugu a cikin wuta mai rura?

` 22. Tun fari nan hujja da za ka riƙa zuwa,
Gaban Ilahu don ka san yin tsira.

23. Tsafce abincinka ya zam na halaliya,
Da abin hawanka gida tufar da ka ɗaura.

24. In kai haka sai addu’arka ta karɓuwa,
Ba shamaki ga Ilahu lailu nahara.

25. Zam ba da haƙƙoƙin dukan mai haƙƙuwa,
A kanka zaluntar su kadda ka fara.

26. Fara gidanka ka sauke dukkan nauyuka,
Ka sanar da su Tauhidi don su yi tsira.

27. Haƙƙi na Allah za ya yafe in ya so,
Haƙƙin mutane bai barin ko zarra.

28. Duba Izazul can zuwa ƙarshe nata,
Domin shirin riskar abin da ka ƙera.

29. Ka kyauta hanyoyin biɗarka a kowashe,
Sai Rabbi yai albarkatar su ya ƙara.

30. Kyauta ginin ɗakin da za ka yi kwanciya,
Bayan fitar ruhi jiki bai shura.

31. Yawaita yin Istingifari kowashe,
Zikiri a koyaushe da kyauta ɗahara.

32. Kafin ka tsaftace gaɓɓuwa ya ɗan uwa,
Tsarki na zuci ya kamata ka fara.

33. Tsafce zukata daga dukkan hassada,
Yi da mutane ba shi kai ka ga tsira.

34. Nufi Ilahu da ayyukanka kar ka nan,
Yardar mutane za ta ja ka asara.

35. In ka yi aiki don mutane sui yabo,
Ladanka ke nan gobe ba ka da saura.

36. Allah nufe mu da kyauta aiki ba riya,
Sai don biɗar yardarka ya Gaffara.

37. Allah tsare mu da sharrukan a’ada’u,
Maƙiyanka Rabbi Yahudu har da Nasara.

38. Sanya Shahada ta zamo furucinmu,
Ran tafiyar ruhi da babu matsera.

39. Darajar Rasulu abin yabo albarkacin,
Ƙur’ani wanda muke tila mui tsira.

40. Nasiru G. Ahmad wani almajirin,
Ilimi a kullum baitukan ga ya tsara.

41. Ashirin da ɗai baiti da ƙarin Ashirin,
Ran Juma’a don ni da ku mu yi mora.

Alhamdu lillahi.

21ga Muharram, 1444 (B.H.)
19 ga Agusta, 2022

ADALCI GADON BARCIDagaNasiru G. Ahmad Kisra sarki na Farisa ya,Ziyarci Madina yai jewa.Amirul Muminina Umar,Ya je domin ...
17/08/2022

ADALCI GADON BARCI
Daga
Nasiru G. Ahmad

Kisra sarki na Farisa ya,
Ziyarci Madina yai jewa.

Amirul Muminina Umar,
Ya je domin su ganawa.

Bai iske fankacen bene,
Na sarki har da fadawa.

Domin haka nan ya saba gani,
Sarakan Fursu na yiwa.

Ya tambayi shin ina fadar,
Sarki Umar mu ganawa?

An ce ya wuce masallaci,
Yana can ya yi kwantawa.

Ya iske shi bisa rairai,
Yana barci da juyawa.

Bai iske masu gadi ba,
Tsumman riga ya ɗaurawa.

Mamaki ya cika masa rai,
Da tsoro har da ruɗewa!

Wannan shi ne ya cinye su,
Da yaƙi bai yi janyewa.

Sai al'amarin sarakansu,
Na girman kai da holewa,

Ya zam a idonsa shirme ne,
Domin ƙarshensa taɓewa.

Ya dubi Umar ya ce lallai,
Ka yo barci tsanakewa.

Ba tsoron kar a shammace,
Ka sharri gunka ai yowa.

Domin ka tsai da adalci,
Talakka ba ka cutarwa.

Halifan Ɗaha ya Umar,
Ka zarta sa'a ga kyautawa.

Tutar adalci ka yi ɗaga,
Dimkuraɗiyya abar sowa.

Allahu ya kyauta kwancinka,
Cikin rahama da yarjewa.

Salati da sallama izuwa,
Rasulu ba za mu dainawa.

Nasir Ahmad ya tsaro ta,
Ga mu domin tunatarwa.

17 ga Agusta, 2022

WAƘAR KUƊIDaga Nasiru G Ahmad1. Rabbi ban iko na tsara,    Baituka kar nai gazawa.2. Yau batu zan kan nuƙudu,    Ko ko m...
01/08/2022

WAƘAR KUƊI

Daga
Nasiru G Ahmad

1. Rabbi ban iko na tsara,
Baituka kar nai gazawa.

2. Yau batu zan kan nuƙudu,
Ko ko money ba sakewa.

3.Mallakar su tana da daɗi,
Duniya ba mai musawa.

4. Laƙani na farin jini ne,
Ba ƙiyayya sai biyewa.

5.Maganin huce takaici,
Duniyar ga kana sakewa.

6. Duk batunka abin yabo ne,
Aibukanka suna ɓacewa.

7. Kai da Sarki har su gwamna,
Sai abota ba rabewa.

8. Dukka faɗin duniyar nan,
Za ka je lale anai wa.

9. Dukka yare za ka ji shI,
Don ko Naira ta iyawa.

10. A gida ba babba sai kai,
Duk batunka ba a ƙiyawa.

11. 'Yan uwa su taho gare ka,
Lamarinka suna yabawa.

12. Fa'idojin ba su ƙirgo,
In da money ka hayewa!

13. Aibuka zan bayyana su,
Don dukanmu mu zam kulawa.

14. Kar ka manta akwai hisabi,
Kan abin da ka mallakawa.

15. Shin ta yaya kab biɗe su?
Haka yadda ka zan kashewa.

16. In ka tara sai ka koma,
Fargabar su zamo ɓacewa,

17. Ga ɓarayi na fakon ka,
Ko ina ka yi ba sakewa.

18. Hankalinka yana gare su,
Ko da yaushe kana tunawa.

19. "Ga kuɗina can ga wane,
Gobe haja za ta zowa."

20. To ina nutsuwar ibada,
Gun Tabaraka mai iyawa?

21. Ƙoƙarin tsare dukiya na,
Sa ralala ai biyewa.

22. Sai ka ga an kai ga tsafi,
Sihiri an rungumewa.

23. Har a kai shirka da Allah,
Dukiya don ai tsarewa.

24. Son da kowa ke gare ka,
Ka sani ƙarya sukewa.

25. Don a samu abin riƙa ne,
In fa babu suna bajewa.

26. In ka so ka farar dabara,
Hidimar dini ka yowa.

27. In halal ce dukiyarka,
Rabbi zai karɓa yabawa.

28. Ba a ba Allah haramun,
Ɗayyibun yake bai riƙawa.

29. Don haka mu biɗi halali,
Don haram ba ta daɗewa.

30. Dukiya ta halali za ai
Wa hisabi ran tsayawa.

31. In haram ce sai uƙuba,
Ga Jahannama ke direwa.

32. Dan uwa gode wa Allah,
Lafiya da yake ta baiwa.

33. Sana’arka riƙe da kyawu,
Ƙwadagonka zamo kulawa.

34. Kar ka raina abin riƙawa,
Na halal shi ke daɗewa.

35. Zam ƙana'a kar ka damu,
In asiri yai rufewa.

36. Nemi albarkar Ilahu,
Godiya ka yi zai daɗawa.

37. Ko da yaushe mu roƙi Allah,
Mu yi kyan ƙarshe gamawa.

38. ‘Yan uwa da ka jarrabe su,
Dukiyarsu ta yi yalwa.

39. Rabbi sa su bisa tafarki,
Mustaƙim ba kangarewa.

40. Ba su ikon taimakawa,
Da halal mai tsarkakewa.

41. Mu talakkawa ka ba mu,
Hakuri da kaɗan mu yowa.

42. Zan tsaya haka ‘yan uwana,
Baitukan nai kammalawa.

43. Nasiru G. Ahmadu ne,
Ya yi waƙar don tunarwa.

Alhamdu lillahi.
28 / 4 / 2014

B  I  K  I DagaNasiru G. Ahmad   1.  Ya Rabbi ban hikima na yo,       Waƙar biki da ake yiwa. 2.  Ba na nufin shagalin b...
17/07/2022

B I K I

Daga
Nasiru G. Ahmad

1. Ya Rabbi ban hikima na yo,
Waƙar biki da ake yiwa.

2. Ba na nufin shagalin biki,
Murna nishaɗi ai rawa.

3. Zan yo batuna ne akan,
Tsari na ba da gudummawa.

4. Yin taimakon juna halal,
Jigo na kyautata rayuwa.

5. Allahu sarki ne ya ce,
Mu yi don mu zam daɗa shaƙuwa.

6. Tsarin zaman jama’a duka,
Na ƙarfafar haka ‘yan uwa.

7. Kan ɗakuna domin zama,
Da hannu guda bai ɗaguwa.

8. Sai an yi gayya an haɗu,
An cicciɓa yaka ɗoruwa.

9. Miya ƙazama anka ce,
Maganinta hannu da yawa.

10. Lamari idan hidima yake,
so babba sai an taruwa.

11. Kowa ya ba da gudummawa,
Wada zai iya ba matsuwa.

12. Harka ta aure haihuwa,
Su anka fi wa bukukuwa.

13. Mata a nan su ne gaba,
Gun taimakon junansuwa.

14. Kaya na barkar haihuwa,
Su kowashe ke basuwa.

15. Haka in bikin aure ake,
Ba sa sake da gudummawa.

16. Wannan abin kyau ne kwarai,
Shari’a yana tabbatuwa.

17. Amma fa sai an yi bisa,
Zuciya guda zai karɓuwa.

18. Ba kyau a ba da gudummawa,
Da nufin a karɓi mafi yawa.

19. Wato a ba ka Ɗari Biyar
Ka biya dubu a gudummawa.

20. Wannan ake ce wa biki,
Bashi fakaice bisa ruwa!

21. Ya zam jiki haka nan ake,
Ba mu san da bai shar’antuwa.

22. Allahu ya ce kar ka yi,
Kyauta ka nemi mafi yawa.

23. Mu karanta surar “Muddasir,”
Ayar Shida don hanuwa.

24. Kin bin umarnin Rabbana,
Shi ke saka mu a ɗimuwa.

25. Ai sai da iko za a yi,
Taimako da ba da gudummawa.

26. In babu hali ta sarai,
Ba dole ko tilastuwa.

27. Ku mu tsarkake niyya wajen,
Kyautarmu ba don ramuwa.

28. In babu hali sai mu yi,
Addu’a ta khairi mai yawa.

29. Haka Musdafa ya cane mana,
Ku mu bi shi don mu ni’imtuwa.

30. Nan zan tsaya Nasir nake,
G. Ahma sai mun saduwa.

Alhamdu Lillah.

13 ga Safar,1428 (BH)
2 ga Maris, 2007

KARIMCIDagaNasiru G. AhmadAllah ƙaran dubun hikima,Nasiha za na bayarwa.Mutane za su zam su da kyau,Muddin da akwai Mutu...
06/07/2022

KARIMCI

Daga
Nasiru G. Ahmad

Allah ƙaran dubun hikima,
Nasiha za na bayarwa.

Mutane za su zam su da kyau,
Muddin da akwai Mutuntawa.

Ganin ƙima cikar ƙawari,
Sanin khairin da ke yowa.

Tsananta lokacinta kaɗan,
Hakan nan ma wadacewa.

A koyaushe sukan yi gushe,
Bayan kuka a darawa.

Karimi wanda ya zamto,
Mutum na ƙwarai gwanin baiwa.

Wannan da buƙatuwar jama'a,
Ta hannunsa ka samawa.

A kul ka naɗe su hannunka,
Wajen ihsani miƙawa.

Muddin ka samu ikon yi,
Kana da abin na bayarwa.

Kwanukkan rayuwar ga suna,
Yawan saɓa da juyawa.

Idan yau ka yi bayarwa,
Wata ran kai za a zam ba wa.

In ko yau kai ake ba wa,
Wata ran kai za ka bayarwa.

Ka gode Ilahu wanda ya sa,
Buƙatu gunka samarwa.

Ya sa jama'a su zo gunka,
Halifansa ka zamtowa.

Kada ka buƙaci sui gode,
Domin wasu ba su godewa.

Allah da ka yi a domin sa,
Zai gode ma ya ƙarawa.

Da dama sun tafi ƙabari,
Alherinsu ya wanzewa.

Yana nan bai mace ba ana,
Ta amfana da godewa.

Wasu ko ga su nan raye,
Matattu sunka zamtowa.

Ba khairinsu da anka gani,
B***e a faɗa a godewa.

Allah sa mu cikin wanda,
In kwananmu ya ƙarewa,

Farin aikinmu zai wanzu,
Mai amfani ya zamtowa.

Ya Allah sanya ƙarshenmu,
Shahada mui ta furtawa.

Darajar Ƙur'an da Manzonka,
Sahabbai nasa na sawa.

Nasir Ahmad ya tsarowa,
Baitocin don tunatarwa.

6 ga Yuli, 2022

HADIƘATUL ƘUR'ANIDagaNasiru G. Ahmad1. Da sunan Rabbi zan buɗe,Wannan lambu na Ƙur'ani.2. Salati da sallama izuwa,     M...
17/06/2022

HADIƘATUL ƘUR'ANI

Daga
Nasiru G. Ahmad

1. Da sunan Rabbi zan buɗe,
Wannan lambu na Ƙur'ani.

2. Salati da sallama izuwa,
Manzo da ka bai wa Ƙur'ani.

3. Ƙasida ce kaɗan zan yo,
A bisa matsayi na Ƙur'ani.

4. Gare mu dukan musulmin du-
niya mu kula da Ƙur'ani.

5. Mu dage kan karatun sa,
Domin mu cika da imani.

6. Ƙur'ani gobe zai ceton,
Makarantanai ga Rahmani.

7. Ashe koyon karatun sa,
Lallai a gare mu ikhwani.

8. Ko da miliyan ta Naira ne,
Mu biya mu laƙanci Ƙur'ani.

9. Ku san salla ba za tai ba,
Sai an fa karanci Ƙur'ani.

10. Karatu nai ibada ne,
Mai kyauta ilahirin sha'ani.

11. Dukkan harafi na kalmarsa,
Goma lada babu nuƙusani.

12. Idan ka ce "Alif-Lam-Mim"
Goma sau uku babu wani zanni.

13. Wato lada Talatin ne,
Ga "Alif-Lam-Mim" ta Ƙur'ani.

14. Zance ne shi na Allahu,
Ga dukan kowa cikin kauni.

15. Ba zai canza ba har abada,
Don yai nisa da shaiɗani.

16. Duk san da ka zo karatun sa,
Iblis kam ba shi gun zauni.

17. Sai dai fa mala'ikun Rahama,
Dama za su taho da ma hauni.

18. Ahalin Allah a banta ƙasa,
Su ne ahali na Ƙur'ani.

19. Idan za mui karatun sa,
Tsarki ya zamo ga ku har ni.

20. Mu zauna tsaf cikin nutsuwa,
Hankali mu haɗa ga Kur'ani.

21. Tunanin duniyar nan duk,
Ku mu bar shi mu doshi Rahmani.

22. Mu zamo niyyar idaba gun,
Allah da ya ba mu Ƙur'ani.

23. Ta hakan nan za mu samu irin,
Ladan da ka ce ga Ƙur'ani.

24. Dalibai ku tsaya ku daddage,
Nazarin sa cikin dare da wuni.

25. Siraɗul mustaƙima ku san,
Shi ne mu kula da Ƙur'ani.

26. Mumini na ƙwarai ba zai sanya,
Ba gun nazari na Ƙur'ani.

27. Ya Allah taimake mu duka,
Mu zamo ahali na Ƙur'ani.

28. Lahira gobe ya cece mu,
Darajar jika na Adnani.

29. In an ce wa ya shirya ta,
Wannan waka ta Ƙur'ani.

30. Muhammadu Nasiru Ahamd,
Burinsa riko da Ƙur'ani.

20 ga Maris, 1996

JAHILCI MUGUN CIWODagaNasiru G. Ahmad 1. Ilahi makagi da ke da sani,    Na komai da ke ba da dukkan sani,        Ka tsar...
25/05/2022

JAHILCI MUGUN CIWO
Daga
Nasiru G. Ahmad

1. Ilahi makagi da ke da sani,
Na komai da ke ba da dukkan sani,
Ka tsarshe mu jahalu ka ba mu sani.

2. Salati ga Manzo da ya fid da mu,
Duhun jahalu Nuru ya fid da mu,
Abin taƙamarmu a yau ilimi.

3. Batuna a yau jahili zai nufa,
Da ma jahilancinsa ba zan rufa,
Domin ya tashi ya zam rarrafa.

4. Haba ɗan uwa me kake ta jira,
Da ba ka biɗar ilmu kai hattara,
Sai dai yawan ci ba ka haƙura?

5. Ka tashi maza riƙi alƙalami,
Ka je ko'ina ka biɗo ilimi,
Don fid da kanka cikin zulumi.

6. Ina gimbiyar kyau gwanar shakara?
Wajen ilimi babu ko saɗara,
Sai ji-da-kai tafi can amara!

7. A yau ba a yayin ku ke jahila,
Mai kyan ɗabi'a ka so adila,
Mai ilimi da yawan hattara.

8. Ki tashi ki nan ilimi kin jiya,
Ya zam "Make-up" naki duk safiya,
Abin taƙamarki da yin sangaya.

9. A yau ba ka zamto abin fahari,
Gidanku da dangi da ma duk gari,
Sai ka yi ilimu kana nazari.

10. A yau ba ka zamto ka mai unguwa,
Ko kansila har ka zam zaɓuwa,
Sai ka yi ilimu kake karɓuwa.

11. Rashin ilimi shi ka sa ɗimuwa,
A duk lamuran yau ka zam damuwa,
Dukan izgili daɗa kai za a wa.

12. Rashin ilimi shi ka sa kibru,
Da zagin iyaye da yin sihiru,
Da duk ayyukan Iblis makiru.

13. Akwai sad da matar wani jahili,
Ta ɗebo takardunsa jingim tuli,
Ta tura wuta ta dafe dankali!

14. Takardun gidajensa ne dukkani,
Kaza kwangila wadda zai ta gini,
Cakinsa na banki ya kone tuni!

15. A dole ya dauki asara haka,
Rashin ilimi ne ya jawo haka,
Jaahilu kam bai ganin ɗaukaka!

16. Idan jahili yai batu a gwale,
Wurin sanya hannu ko sai dangwale,
Lamurransa za ka ga sun dagule.

17. Cuta mafi munana jahalu,
Da ke sa mutum tsakiyar wahalu,
Da dumbin takaici ga mai hankalu.

18. Kaɗai maganinta biɗar ilimi,
Na boko da Arbi wurin malami,
Domin fita daga duk zulumi.

19. Akwai makarantu mataki-mataki,
Na yara da manya domin a dauki,
Darussa na ilmu bisa ga tafarki.

20. Nan 'yan uwa zan zamo diga aya,
Allah ya ba mu zama lafiya,
Da haske na ilmu a duk safiya.

21. Nasiru Ahmadu ne ya yi ta,
Domin a bar jahilanci ɓata,
A nemo sani ne kawai mafita.

22. Baiti guda sha ɗaya sau biyu,
Ya Rabbi salli ala An-Nabiyyu,
Da ya zo da dinin ƙwarai muka shiryu.

5 ga Mayu, 2002

JUYIN RAYUWADaga: Nasiru G. AhmadDa sunan Rabbi mai baiwa gare mu,Da jin daɗi wahalta duk mu ɗauka.Cikar imani ke nan ya...
11/05/2022

JUYIN RAYUWA
Daga: Nasiru G. Ahmad

Da sunan Rabbi mai baiwa gare mu,
Da jin daɗi wahalta duk mu ɗauka.

Cikar imani ke nan yau da gobe,
Juyi nasu gare mu kar mu koka.

Kada ka zamo cikin damo da ƙunci,
Bisa juyi na ranakku gare ka.

Ka miƙa wuya idan yau ta ƙiye ka,
Fa gobe tana zama ran dariyarka.

Musibu duk tsanantarsu da kaifi,
Ba za su ba dawwamewa nan gare ka.

Ka zam ka mutum dakakke kodayaushe,
Wajen cika alƙawurra ai sanin ka.

Idan aibobikanka sun yawaita,
Ka so ɓoye su kar a zamo tsanar ka.

Mayafin lulluɓe su yawaita "Ungo,"
Idan baki ya ci ba za shi tanka.

Ka bar raina magauta sharri nasu,
Abin neman tsari in sun gare ka.

Ka bar kwaɗayin abin hannun la'imi,
Marowanci ka san ba za shi ba ka.

Ta ya za kai zaton samun ruwan sha,
Cikin tsakiyar hamada babu gunka.

Rabonka ba za ya ƙi zowa gare ka,
Idan ka kyautata hanyar biɗarka.

Hakan nan ba shi ƙaro in ka zam bin,
Baƙar hanya kana wahalar da kanka.

Wadata ba ta daumewa hakan nan,
Ƙuncin rayo idan ya diro gare ka.

Idan ajali ya zo shi ba matsera,
Yawan mabiya ba zai amfanuwar ka.

Dukan girma da faɗin duniyar nan,
Da tarin masu yin ƙauna gare ka.

Idan ƙadara ta sauka sai ka gan ta,
Matse komai ko tarin dukiyarka.

Ka bar ruɗo da ƙawar duniyar nan,
Mayaudariya batun ta kar ka ɗauka.

Idan ajali ya zo ba maganin sa,
A dole ka je ga Allah khaliƙinka.

Idan an tambayi mai tsara waƙar,
Nasir Ahmad abokin rayuwarka.

BARKA DA SALLADagaNasiru G. AhmadBarka da salla 'yan uwa,Allah ya ba mu amintuwa.Mun yi ibadar azumi,Na wata guda ba yan...
02/05/2022

BARKA DA SALLA
Daga
Nasiru G. Ahmad

Barka da salla 'yan uwa,
Allah ya ba mu amintuwa.

Mun yi ibadar azumi,
Na wata guda ba yankuwa.

Mun bar abinci da shan ruwa,
Ga Ilahu don mu kusantuwa.

Zikiri na Allah mun ta yi,
Ƙur'ani mun yi karantuwa.

Nafilfilu a cikin dare,
Don hasanarmu ta ƙaruwa.

Zakka ta Kono mun fitar,
Mun ba wa masu buƙatuwa.

Salla ta Idi mun zuwa,
A cikin ado da nishaɗuwa.

Mun ɗebi girki ba nawa,
Murnarmu ba ta misaltuwa.

Duk wanga baiwa ce daga,
Allah da ta ci a goduwa.

Wasunsu an fara da su,
Sun tafi ba ran komuwa.

Wasunmu na kwance gida,
Da asibbiti ba waluwa.

Sun so a yo murnar da su,
Cuta ga su tai hanuwa.

Ƙalubale da yake ga mu,
Ga Rabbi mui ta shukurtuwa.

Kyawu na aiki kar mu bar,
Kullum ya rinƙa gudanuwa.

Zumunci mui sadar da shi,
Domin mu zam daɗa shaƙuwa.

Domin idan tafiya ta zo,
Mu san abin yin riƙuwa.

Ya Rabbi sa dukkan iba-
dojinmu gunka su karɓuwa.

Ka jiƙan waɗanda sun tafi,
A cikin watan ka yi afuwa.

Dukkan marassa lafiya,
Sa lafiyarsu ta komuwa.

Mu ma ka sanya lafiya,
A gare mu tai ingantawa.

Ya 'yan uwa nai gaisuwa,
A gare ku mai yin ƙamsuwa.

Barka da salla ƙarama,
Ga maza da mata na yiwa.

Allah ya maimaita mana,
Ta baɗin baɗi ba yankuwa.

Mu zamo da ƙoshin lafiya,
Domin ga Rabbi mu bautuwa.

Darajar Rasulu abin biya,
Ya zamo da mu zai cetuwa.

Nasiru G. Ahmad nake,
Mai son ku babu nifaƙuwa.

١ من شوال، ١٤٤٣م
2 ga Mayu, 2022

Address

Zoo Road
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category