Sarki Muhammad Sharada

Sarki Muhammad Sharada Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sarki Muhammad Sharada, Publisher, Nom. 1104 Sharada Phase one, Kano.

29/10/2023

MAI TACECCEN FARI ﷺ

Ya Allah kayi salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu Mai taceccen farin fatar jiki, ma'abocin yalwatattun idanuwa masu kyawu da kwarjini da hasken fuska, Mai mutukar farin cikin idanu da baqin kwayar cikinsa tare da ratsina ja wanda ke nuna alamar Qarfin jiki da zuciya tare da jarumtakarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin yalwataccen gashin kai, gashin nasa baqi ne mai sheqi kuma yayi liflif akan kafadunsa. Mai yalwataccen goshi tare sissiran karan hanci, da mayalwacin gashin gira masu kyawu da kwarjini.

Mai fararen hakora jerarru, ga wushirya mai fidda haske da Qamshi yayin da yake magana. Kwarjini ya lullube murmushinsa, ga tawadhu'unsa ya mamaye dukkan lamarinsa (saww).

Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin Manyan damatsu mai zara-zaran yatsu, mai yalwar tafin hannu bisa ma'ana da zahiri. Mai Madaidaicin ciki ne shi tare da yalwar Qirji. Cikinsa da Qirjinsa sun daidaita da juna, kuma akwai wani jerarren baqin gashi wanda ya taho daga Qirjinsa zuwa cibiyarsa ﷺ.

Ya Allah yi salati da tasleemi gareshi gwargwadon matsayinsa awajenka, sau adadin gudanuwar lamarinka da zartuwar Qudurarka bisa dukkan halittunka..

Ya Allah ka sanya wannan salatin ya zama silar shakuwar ruhinmu da ambatonsa, kuma ya zamo silar nutsewar zukatanmu acikin kogin sonsa, da tausuwar gabobinmu cikin biyayya gareshi.

Ya Allah ka sanya tunanin wannan Annabin da ambatonsa ya zamanto abincin ruhinmu da nutsuwarmu ta zahiri da buya. Amin

22/07/2021
Ya Gafuru! Muna Neman Gafararka Akan Dukkan Abunda Muka Sani, Kai Ne Masani, Babu Mai Sani Sai Kai, Kayi Mana Mafita, Ka...
13/04/2021

Ya Gafuru! Muna Neman Gafararka Akan Dukkan Abunda Muka Sani, Kai Ne Masani, Babu Mai Sani Sai Kai, Kayi Mana Mafita, Ka Karbi Ibadunmu, Kajiqan Magabatanmu.ya Allah. Barkanmu da Shan Ruwa

Talata,Ramadan.01

*ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏”ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ“.```{ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘ...
04/12/2020

*ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏”ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ“.
```{ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ}`

_An Ƙarɓo Daga Ibn Umar Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Mafi Alkhairin Sallah a Wurin Allah, Itace Sallar Asubar Ranar Juma'a a Cikin Jam'i”.
{Baihaqi Ya Ruwaitoshi}

Assalamu alaikum.Ankarbo Hadith daga Abi-Hurairah Allah ya kara yarda a gare shi. Yace; Manzon Allah (SAW) Yace "Kalmomi...
25/11/2020

Assalamu alaikum.
Ankarbo Hadith daga Abi-Hurairah Allah ya kara yarda a gare shi. Yace; Manzon Allah (SAW) Yace
"Kalmomi biyu abin so ne wajen Allah, masu sauki ne a kan harshe, kuma masu nauyi ne a kan mizani, *Subhanallahi wa bihamdihi, Subhanallahil Azeem
((كلمتان حبيبتان إلى الرحمن، خفيفتان على اللسان، ثقيلتان في الميزان سبحان الله وبحمده، سبحان الله العظيم)).

Bukhari ne ya ruwaito.

Naku Sarki Muhammad Sharada Sen Muhammad Mujtafa Sani

Salam alaikum Barkanmu da asuba da fatan wayi garin Talata lafiya,Allah kaji kan iyayenmu da yan, uwanmu,Yaya ibada alla...
24/11/2020

Salam alaikum Barkanmu da asuba da fatan wayi garin Talata lafiya,Allah kaji kan iyayenmu da yan, uwanmu,Yaya ibada allah ya karbe ibadarmu ameen.Ya dan,uwa dake yar,uwa akwai abinda muke jira wanda ya zama dole ga duk mai rai wannan aba itace mutuwa.Mutuwa itace babban wa'azi ga mai hankali da tunana Mutuwa itace abu na farko wanda idan mutum ya tuno zai rage buri a rayuwarsa.Mutuwa itace tazama dole dukan mai rai saiya dandanata koya naso ko bayaso.Mutuwa itace dukan mai imani baya kwanciya bacci saiya tunata.Mutuwa itace bakuwar da bata sallama sai kawai tazo tatafi da mutum akan aikin alhairi kona sharri.Mutuwa itace komai kudinka komai mulkinka idan lokacin zuwanta gareka yayi sai tazo tatafi da kai daga kai sai halinka ba kudi ba mulki.Ya kai maaddininmu da zaka zama gawa.Mai ya kaika danne hakkin wani kuma mai ya kaika hassada,mai ya kaika girman kai mai ya kaika aikata alfasha.Mai ya kaika cin amana kaida za'a sakaka a kabari daga kai sai likafani sai aikinka na alkairi.Allah kasa muyi kyakyawan karshe da kalmar laa ilaaha Illallaah,Allah ka tsare mutuncinmu da addininmu da imaninmu ameen.Barkanmu da safiyar Talata.

14/07/2017

Agobene 15.07.2017 insha allahu masarautar matasan sharada zata fara zama domin gudanarda shirye shiryen zagayen hawan sallah.

Address

Nom. 1104 Sharada Phase One
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarki Muhammad Sharada posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category