20/11/2025
Masussuka: Budaddiyar Wasika zuwa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda.
Kiyaye Hakkin Shaik Masussuka-Ambasadan Zaman Lafiya, tare da damar gudanar da Addini dai dai fahimta da 'Yancin fadin Albarkacin baki.
______________
Ya Mai Girma Gwamna.
Ina fata wannan wasikar tawa za ta sameka a cikin kwanciyar hankali da ingantaciyyar lafiya. Na rubuta maka wannan wasikar ce, domin na jawo hankalinka kan damar da kowane dan kasa ke da ita na damar yin addininsa kamar yadda yayi imani da 'yancin fadin albarkacin baki.
A 'Yan kwanakin nan Shaik Masussuka wanda aka ba shi matsayin Ambasadan zaman lafiya saboda salonsa na waazin zaman lafiya yana samun matsi da barazana daga gungun wadansu Malamai saboda kawai bambanci fahimta na addini. Akwai rade-radin da ke nuni da cewa wadancan Malamai sun matsa maka lamba, ko dai ka sa Shaik Masussuka ya daina wa'azi, ko kuma ka Kai shi Gidan Kurkuku.
Kamar yadda ka sani ya mai girma gwamna, sashen kundin tsarin mulkin Najeriya mai lamba 38 (1) a cikin baka ya bada dama ga kowane dan kasa yayi Addinin da ya ga dama ba tare da wani yayi masa katsalandan ba.
Haka kuma, sashe na 39 (1) cikin baka ya bayyana cewa kowane Dan kasa na da 'yancin yin addinin da ya ga dama, da fadin albarkacin bakinsa ba tare da wani ko wasu sun tsangame shi ba, ko su tilasta masa Ajiye raayinsa don ya koma na su. Wadannan dokoki sun bawa kowane Dan kasa cikakkiyar dama na yi addininsa yadda ya ke so.
Anan, da girman kujerarka ya Mai girma Gwamna, Ina ba ka shawara kamar haka.
1. Ka bada kariya ga Shaik Masussuka kamar yadda tsarin mulki ya tanada da kowace irin tsangwama, da ba shi goyon baya wajen waazinsa na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da hadin kai tsakanin musulmi da wadanda ba Musulmi ba.
2. Kada ka yarda da matsin Lamba, na kowane bangare na addini wajen kokarin ingizaka na amfani da Karfin mulki domin dakushewa da hana 'yancin mutum na bayyana raayinsa na addini. Domin masu kokarin sai an yi haka, suma raaayoyinsu suke bayyanawa
3. Ka manta da su ka cigaba da ayyukan kyautata rayuwar Jama'ar Jihar Katsina, musamman halin da Jihar ta ke ciki na 'yan ta'adda, yaki da talauci da ayyukan kyautata rayuwa a Jihar Katsina da zai amfani al'umma.
4. Kada ka yarda a yi wani zaman Muqabala da Shaik Masussuka. Gayyatarsa da zaman Muqabala kaucewa tsarin mulkin Najeriya ne, da tauye masa hakkinsa a matsayinsa na Dan kasa.
5. Na yarda da kai a matsayin gwamna mai ilimi da hangen nesa, sanin ya kamata da adalci. Ina kara ba ka shawara cewa, Jihar Katsina ba hayaniya da musun fahimtar addini take bukata ba, maimakon haka tana neman wanda zai cece ta daga halin da take ciki, kuma Kai ne ka dace da haka.