01/10/2025
A gaskiya ƙasar nan ana cikin mawuyacin yanayi, Wallahi sai da wani Ɗan India, jiya yake cemin yau Public Holiday ne, na ce me akeyi, ya ce min gobe 1st October(Independence Day), Wallahi ni na manta, na ji kunya sosai🙈
Ina Ɗan Ƙasa ace sai wani baƙon haure ne zai tuna min, maimakon ace ni zan sanar dashi.
Allah Ubangiji ya shiryi Shuwagabanninmu, ya farfaɗo mana da martabar ƙasarmu, ya kawo mana zaman lafiya da arziƙi mai albarka.
Allah ka bawa yankunan da suke fama da tashe-tashen hankula da rikicin ƴan bindiga da bandit da na boko haram zaman lafiya, amin.
Abdullahi Musa Musa (Abba)
1st October 2025