03/12/2024
Watan fa yazo
Jumada al-Thani 2024 (Watan Haihuwar Sayyada Fatima Zahra AS)
Jumada al-Thani shi ne wata na shida a kalandar Musulunci (Hijira) kuma ana kiransa da Jumada al-Akhirah.
Wata ne na musamman ga Manzon Allah (SAW), domin shi ne watan da aka haifi ‘yarsa mafi soyuwa a gareshi Sayyida Fatima Zahra (AS) a (ranar 20 ga Jumada al-Thani).
Ga musulmi lokaci ne mai girma da za mu yi sallamawa a gare ta da yin tunani a kan rayuwarta da dabi'arta da kusancinta ga Manzon Allah (SAW), wanda daga ciki ne za mu iya fitar da muhimman darussa wadanda za mu iya aiwatar da su a rayuwarmu.
Annabi (SAW) ya ce: Fatima wata tsoka ce a cikin jikina: ita ce zuciyata da ruhina da ke cikin kirjina. Duk wanda ya cutar da ita hakika ya cutar da ni, kuma wanda ya cutar da ni ya fusata Allah.
(Bukhari). Wannan yana nuna kusancinta ga Manzon Allah (SAW) da daukakarta ga Allah.
Jumada al-Thani ko Jumada al-Akhirah zai fara a ranar 2 ga Disamba 2024 bayan watan Jumada al-Awwal.
Asali
Ya kasance al’ada ce ta al’ummar larabawa jahiliyya su sanya sunayen watanni gwargwadon yanayin abinda da s**a faru a cikinsa, ko kuma al’adar da aka saba yi a lokacin. Kalmar Jumada ta samo asali ne daga kalmar da ke nufin busasshiyar ƙasa, ko kuma ƙasar ba ruwan sama. Hakanan yana iya nufin kekashewa. Wannan na iya kasancewa yana da alaƙa da yanayi na lokacin da aka fara ba wa watanni suna a tarihi. Kamar yadda shekarar Musulunci ke aiki a kan lissafin watanni, don haka ake samun karin kwanaki 11-12 a kowace shekara a kan shekarar miladiyya. Wannan yana nufin cewa sunan watan na iya kin zuwa daidai da yanayin sunan da aka sa masa ko kuma abubuwan da s**a dangance shi. Alal musali kamar watan Ramadan yana iya zuwa lokacin sanyi ko damina ko kuma lokacin zafin bazara.
Ibada
Jumada al-Thani ba wata ne na wata ibada ta musamman ba, amma Allah (SWT) da manzonsa Annabi (SAW) suna ba da umarnin ayyukan alheri kamar sadaqah jaariyah, karatun alqur’ani, istighfari da sallolin nafilfili duk tsahon watanni shekara.
Yana da mahimmanci ku yi amfani da lokacinku cikin hikima. Ga Mumini, kowane lokaci, kowace rana wata dama ce mai daraja ta samun lada da goge zunubai da ayyuka nagari.
"Ka ci riba biyar kafin biyar: kuruciyarka kafin tsufanka, lafiyarka kafin rashin lafiyarka, dukiyarka kafin talaucinka, lokacinka na rayuwarka kafin mutuwarka." "In ji Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) – Ibn Abbas kuma Al Hakim ya ruwaito.