20/04/2024
DEPARTMENT OF HAUSA
FEDERAL UNIVERSITY DUTSIN-MA
PMB 5001 DUTSIN-MA KATSINA STATE, NIGERIA
GASA! GASA!! GASA!!!
SASHEN HAUSA NA JAMI’AR TARAYYA DA KE DUTSIN-MA, JIHAR KATSINA NIJERIYA na farin cikin sanar da marubuta da masu sha'awar rubutu cewa, ga dama ta samu da za ku nuna fasaharku da baiwar da Allah ya huwace maku, domin kuwa sashen ya shirya maku GASAR GAJERUN LABARAI NA HAUSA A KAN MATSALAR TSARO A AREWACIN NIJERIYA.
Wannan gasa za ta buɗe wani sabon babi wanda ake da ƙamfar rubutu a kansa, musamman ga ɗaliban manyan makarantu tun daga kan sakandire har zuwa kwalejoji da jami’oin ƙasar nan. Duba da girman asalin matsalar tsaro, wato yadda ta zamar wa al’umma ƙayar kifi a maƙogoro kuma ta yi kaka-gida, musamman a yankin arewacin Nijeriya wato Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
MANUFAR GASAR
Manufar wannan gasa ita ce samar da gajerun labaran da za su fito da girman matsalolin da ake fuskanta na tsaro ta sigar labari ta hanyar zaƙulo duk wani abu da ya shafi matsalar ko yake goya wa matsalar tsaro baya a da da kuma yanzu. Misali rikicin Fulani da makiyaya da fashi da makami da rikicin ‘yan banga (‘yan sa kai da mutanen gari) da rikicin addinai ko na gari ko na ƙabilanci ko garkuwa da mutane don kuɗin fansa ko tayar da ƙayar baya ko ta’addancin ɓarayin daji ko ƙwacen ababen hawa kamar mota da babur ko ƙwacen waya ko bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda ko goyon bayansu, ko gayyato su su yi ta’addanci domin biyan wata buƙata/cimma wata manufa ko ƙulla wata mu’amalar sirri da su.
Wata manufar kuma ita ce, don a ƙara ilmantar da mutane cikin sigar rubutun zube, irin haɗarin da yake tattare da tashin hankali da kuma fa’idar da take tattare da zaman lafiya da lumana, wanda hakan ne yake zama silar cigaban ƙasa da bunƙasarta.
Haka kuma, labaran za su haska wa gwamnati da al’umma girman yadda matsalar ta hana wa kowa haɗiyar ruwa cikin sa’ida musamman ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da ilimi da kasuwanci da mutuncin mutane da cigaba kowane iri da zaman lafiya mai ɗorewa da sauransu.
ƘA'IDOJON SHIGA GASAR
1. Ba za a karɓi duk wani labarin da ya ci mutuncin wani ko wasu ba, ta fuskar ƙabila yare ko addini ko ɗaura wa wata hukuma laifi kacokam.
2. Ƙagaggen labarin kar ya gaza kalmomi dubu huɗu kar kuma ya wuce dubu biyar (4000-5000).
3. Dole ƙagaggen labarin da za a rubutu ya kasance ya shafi matsalar tsaro ta hanyar fito da girman matsalar tsaron da yadda ta shafi ɓangarori da yawa na rayuwar al’umma da mayar da su baya tare da fito da wasu hanyoyi da za su iya zama mafita kan matsalolin.
4. Dole ne a kula da ƙa'idojin rubutu, kuma wajibi ne a yi rubutun bisa tsarin haruffa masu ƙugiya na Hausa Latin, sannan kuma rubutun ya kasance an turo shi bisa tsarin Microsoft word.
5. Wajibi ne labaran su kasance sababbi waɗanada ba a taɓa shiga wata gasa da su ba ko kuma aka buga su a littattafai ko wasu jaridu ko zauruka na kafafen sadarwa ko gidajen rediyo da talabijin ba.
6. Duk wanda za ya shiga gasar, dole ya zama shi kaɗai, ba haɗin guiwa wajen shigarta ba. Wato dai ana buƙatar ɗaiɗaikun mutane ne kawai mace ko namiji. Haka kuma gasar a buɗe take ga duk wanda ya iya rubutu da harshen Hausa ko da ba a Nijeriya yake ba, matuƙar dai zai iya kiyaye dokoki da ƙa'idojin da aka shimfiɗa.
7. Wajibi ne a aiko da cikakken aiki daga 12 dare na ranar 17 ga watan Afrilu zuwa 12 dare na 30 ga watan Yuli na shekarar 2024.
8. Duk labarin da aka shiga gasar da shi mallakin sashen Hausa na Jami'ar Tarayya Dutsin-Ma ne, ba a yarda a sake ɗaukar shi a shigar da shi wata gasa ba ko a sarrafa shi ta wata hanya ko makamancin haka ba.
9. Hukuncin da alƙalan gasa s**a yanke shi ne maganar ƙarshe ba za a sake tattaunawa ko duba hukuncin bayan fitar sakamako ba.
10. Marubuta za su turo da cikakken sunansu, lambar waya da adireshi a saman shafin farko na labarinsu ta wannan imail (ƙibɗau): [email protected]
KYAUTUTTUKAN DA ZA A BAYAR
Za a bayar da kyauttuka ga waɗanda s**a shiga gasar daga na ɗaya zuwa na uku,sannan daga na uku zuwa na goma kuma za a buga labaran nasu a matsayin littafi a kuma ƙaddamar da shi a yayin bikin bayar da kyautukan.
Za a bayar da kambu ga na ɗaya zuwa na uku, sannan daga na hudu zuwa na shida za a ba su tukuicin kudin alkalami da takardar shaida wadda take ɗauke da sa hannun shugaban Jami'a da Shugaban Sashen Hausa na Jami'ar Tarayya da ke Dutsin-Ma.
SAKAMAKON DA AKE SA RAN GASAR ZA TA SAMAR BAYAN KAMMALATA
Ana sa ran idan an yi wannan gasa za ta haifar da samuwar abubuwa muhimmai kamar haka:
a. Ankarar da mutane irin rawar da kowa zai iya takawa domin magance ko kawo ƙarshen wannan matsala ta tsaro.
b. Samar da littafi guda ɗaya sukutum wanda zai ƙunshi labarai masu ɗauke da maudu’i kan sha’anin tsaro da za a ringa karantawa da nazarta a makarantu tun daga ƙananan makarantu har manya.
c. Daga cikin sakamakon da ake sa ran gani a ƙarshen wannan gasa shi ne zaƙulo zaƙaƙuran marubuta masu baiwa da baiwarsu za ta iya taimakawa wurin magance wasu matsalolin da suke cikin al’umma ta hanyar amfani da alƙalummansu a inda ya dace
d. Gasar na iya zama dalilin shigar da darasin Ilimin Zaman Lafiya da Tsaro (Peace And Security Education) a cikin Manhajar karatun ɗaliban makarantun Firamare da Sakandare.
e. Jawo hankalin ‘yan kasuwa da masu hali da kamfanoni da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa da masu zaman-kansu domin su tallafa wa matsalar tsaro domin a kai ƙarshenta domin samun cigaba mai ɗorewa a ƙasa.
f. Fito da girman matsalar tsaro da yadda ta shafi ɓangarori da yawa na rayuwar al’umma da mayar da su baya tare da fito da wasu hanyoyi da In Sha Allahu za su iya zama mafita kan wannan gagarumar matsala.
Domin tuntuɓa ko ƙarin bayani:
07067708766
08036796121
08167600111