27/06/2025
ILLOLIN HAƊAMA (GUDA 8 )
Haɗama na nufin wata dabi'a ta son kai da handuna da babakere, da kishin abin da wani yake da shi ko yake samu, tare da ƙoƙarin hana shi wannan ni’ima ko musguna masa saboda kyashi ko tsanar ci gabansa.
Wannan ɗabi’a ta kasance mummuna ce wadda take haifar da barna iri-iri a cikin al’umma.
Akwai bambanci tsakanin hassada da haɗama: yayin da hassada ke nuna ƙyashi da buri ni’imar wani ta gushe, haɗama na tare da ƙoƙarin hana ko kawo cikas kai-tsaye.
1. Haɗama na lalata kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane. Idan mutum yana da haɗama, sai ya kasa ganin alfarmar ‘yan uwansa. Wannan na haddasa rarrabuwar kawuna da ɓangaranci a tsakanin mutane, wanda ke hana zaman lafiya da ci gaban al'umma.
2. Mutumin da ke da haɗama ba ya son ganin wasu na farin ciki ko samun ci gaba. Wannan na iya kai shi ga haddasa rigima ko fitina ta kowane fanni – a cikin gida, kasuwa, ko ma cikin shugabanci.
3. Haɗama na kaiwa ga ɗaukar matakai na munana kamar yada ƙarya, ɓata suna, da ɓarna.
4. Idan mutane suna da haɗama, babu wanda zai so wani ya zarce shi. Wannan na hana ƙarfafa juna ko bayar da gudunmawa wajen ci gaban jama’a. Ma’aikata ba sa taimakon juna, shugabanni ba sa tallafawa nagari, malamai ba sa son wani ya fisu ilimi – duk saboda haɗama.
5. Haɗama na haifar da damuwa da tashin hankali ga mai yinta, domin kullum zuciyarsa na cike da zafin ganin wasu na ci gaba. Hakan na hana shi kwanciyar hankali da jin daɗin rayuwa. Har ma yana iya kamuwa da cututtukan zuciya ko hauka saboda kishi mara iyaka.
6. Mutumin da ke da haɗama yana kin yarda da yadda Allah ke raba arziki da daraja tsakanin bayinsa. Wannan dabi’a tamkar ƙin hukuncin Allah ne .
A Musulunci, wannan kuskure ne mai girma.
7. Mai haɗama na iya fadawa zalunci saboda kishin wani. Zai iya yanke shari’a ba tare da adalci ba, ko ya haɗa baki da wasu domin hana wani wata dama. Wannan hali na ɗaya daga cikin abubuwan da ke lalata adalci da gaskiya a cikin al’umma.
8. Haɗama cuta ce da ke cin gaban al’umma da ruɗar da zuciya. Duk wanda ke da ita yana barazana ga zaman lafiya da ci gaban kowa. Don haka wajibi ne a wayar da kan jama’a game da haɗarin wannan ɗabi’a, a kuma ƙarfafa kyakkyawar zuciya da haɗin kai.
Mu cire wannan dabi'a daga cikin mu domin samun alkhairi ds zaman lafiya.
Allah ya raba mu da haɗama.