18/07/2025
Majalisar dokokin Kano ta tabbatar da karɓar ƙorafe-ƙorafe kan shugabar ALGON amma ta ƙaryata rahoton bincikar ta
Majalisar dokokin jihar Kano ta ƙaryata rahotannin da ke cewa za ta fara binciken Hajiya Sa’adatu Yusha’u, shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma shugabar kungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi, ALGON, a jihar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na shugaban majalisar, Kamaludeen Sani Shawai, majalisar ta bayyana ikirarin da aka yi a matsayin “marasa tushe, yaudara, kuma gaba daya karya ce.”
Majalisar ta fayyace cewa Shugaban Masu Rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala bai bayar da wata tattaunawa ba ko kuma ya yi magana a bainar jama’a dangane da fara wani bincike a kan Shugaban ALGON.
“Hon. Dala, kamar kowane zababben mamba, kundin tsarin mulki ya ba shi ikon karbar koke daga mazabu. Karbar koke ba ya nufin amincewa da abin da ke cikinta ko kuma wani mataki na doka,” in ji sanarwar.
Majalisar ta kuma yi gargadin cewa rahotannin da ake ta yadawa, musamman ma daga majiyoyin da ba na hukuma ba, suna nuna bata-gari ne na tsarin dokoki, kuma da alama wani shiri ne na lalata mutuncin Shugaban masu rinjaye.
Da take jaddada kudurinta na bin ka’ida, majalisar ta tunatar da jama’a cewa babu wani bincike da zai iya ci gaba ba tare da bin ka’idojin da aka kafa ba, ciki har da yin adalci ga duk bangarorin da abin ya shafa.
Ya yi Allah wadai da yada zarge-zarge marasa tushe ba tare da wata shaida ko tabbaci daga wata majiya ta Majalisar ba.