04/08/2024
Wannan shi ne dogon jawabin da ogah Tunibu yayi a yau ko kuna da lokacin karantawa kuwa?
Inda ya ke cewa
Ya ku Yan uwana `yan Nijeriya!
Ina magana ne da ku a yau cikin alhini, tare da kokarin sauke nauyin da ke wuyana cikin gaggawa, hakan na faruwa ne saboda sanin irin tashe-tashen hankula da zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin mu ta haifar.
Wani abin takaici shine yadda aka sami tarin hazikan matasan Najeriya cikin zanga-zangar wadan da basu da wani buri ko mafarki sai na ganin an samu ci gaba mai kyau da dorewa a kasar mu.
Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da barnata dukiyoyin jama'a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka rika wawushe manyan kantuna da shaguna, sabanin alkawarin da masu shirya zanga-zangar s**a yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a fadin kasarmu. Mu sani, rushe kadarori babu abinda zai haifar sai mayar da mu baya a matsayinmu na al'umma, domin kuwa da dan abinda muke riritawa za a sake amfani wajen sake gina abinda aka rusa.
Ina mika ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwan wadanda s**a rasa rayukansu a yayin zanga-zangar. Ina so mu sani cewa, dole ne mu daina amfani da zubar da jini da tashin hankali da barna a matsayin hanyar neman biyan bukata.
A matsayina na shugaban wannan kasa, wajibi ne a kai na in tabbatar da doka da zaman lafiya. Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya dora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane dan kasa, don haka gwamnatinmu ba za ta saka ido ta bar wasu tsiraru masu boyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan kasa mai albarka ba.
A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu yinta umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da bude kofar tattaunawa da sulhu, wanda a koda yaushe kofata a bude take ga hakan. Najeriya na bukatar dukkan mu baki daya ne a halin yanzu, tana so mu hada kai - ba tare da la'akar