09/08/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            SHIN INA UBANGIJI YAKE??
Anyi wani mutum a kasar Baghdad wanda ke nuna gaba da musulunci sosai, Inda duk ƙasar ba wanda ya isa ya amsa mishi wasu tambayoyinshi guda 3 dayake yawan tambayar musulman garin.
Wata rana wani yaro ɗan shekara 10 yafito yaji mutumin yana challenging musulunci da musulmai  akan hanya domin waɗannan tambayoyi nashi da baisamu amsarsu ba.  sai yaron ya tsaya ya saurari mutumin a nutse, nan take ya yanke decision akan zaiyi challenging na mutumin, ya matsa kusa dashi yace yazone domin bashi amsoshin tambayoyinshi,  mutumin ya kwashe da dariya da yaga wannan  ɗan yaron? 🤔
Daga karshe dai ya amince akan zaiyi facing challenging daga yaron, jama'a s**a taru a gindin wani dutse inda ananne daman ake yin dukkan shela kan muqabala. 
Duk jama'ar garin s**a taru a gindin dutsen, mutumin yahau saman dutsen ya ɗaga muryarsa yayi tambayarsa ta farko yace:
Meye Ubangijinka yakeyi yanzu haka?
Yaron yayi tunani kaɗan sai yacewa mutumin yasauko kasa yabarshi yahau saman domin ya bashi amsa,  mutumin yace: mene? kanason nasauko ƙasa? yaron yace eh! domin nasamu nabaka amsarka, mutumin yasauko ƙasa ƙaramin yaron yayi wuf da gajerun kafofinshi yayi sama, sai yaron ya amsa da cewa: Ya Allah Mafi Daukaka kazama shaida a gaban waɗannan mutane cewa yanzu kasa wannan mutumin yayi ƙasa, musulmi ƙarami yayi sama.
Jama'ar wajen s**ace:  "Takbir"...."Allah-hu-akbar!!!"
Mutumin ya hura hanci sannan ya sake tambaya ta 2 sai yace: "Meye kenan a duniya kafin Ubangijinka?" yaron ya nutsu sai yacewa mutumin ya ƙirga mishi 10 amman ta baya ."
mutumin ya ƙirga:"10, 9 ,8 , 7 , 6, 5, 4, 3, 2, 1,0"
Sai yaron yace, "Meye yazo  kafin 0 ?"
mutumin yace: ban saniba, ma'ana  babu komai"
Sai yaron yace: "Exactly" tabbas babu abinda   kenan kafin Allah domin shine farko tunba farkon"
Jama'a s**a kara: "Takbir!"...."Allah-hu-akbar!!!!"
Mutumin yazama completely frustrated, sai yayi  final question dinshi  yace: " wani direction  Allah yake kalla?"
Yaron yace akawomar candle, aka kawo yacewa mutumin ya kunna, bayan ya kunna  sai ya tambayeshi da cewa wani direction hasken ke kalla? sai mutumin yace wannan kuma me kakeson nunamin?
sai yaron yace ka faɗamin wani direction hasken ke kalla? sai mutumin yace: kowani direction hasken nanan. 
sai yaron yace: " ka amsawa kanka tambayar. Allah yana  ko ina tamkar yadda hasken nan ya karaɗe ko ina,  babu inda babu Allah 
Jama`a s**a Kara "Takbir!"...."Allah-hu-akbar!!!"
Mutumin yaji daɗin amsoshin yaron ta hanyar ilimi dayayi amfani dasu, inda daga bisani ya karbi musulunci, Anan muqabala ta kare.
Ko kunsan waye yaron?   shine daya daga cikin maluman addini wato Imamu Abu Haneefa (Rahimahullah)
Allah Ya ƙara daukaka musulunci
ya kuma ƙara bamu ilimi mai amfani.
GARI YA WAYE
Sir wisdom pen 🖊️🖊️🖊️