Vision FM Kano

Vision FM Kano VISION FM KANO 92.5
SAMAR MUKU DA SAHIHAN LABARAI A KODA YAUSHE SHINE MURADUN MU. MIKIYA MAI HANGEN NESA

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce bayan kammala addu'ar uku a gidan tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buha...
17/07/2025

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce bayan kammala addu'ar uku a gidan tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari da ke Daura, shi da tawagar gwamnatin tarayya za su koma gidan gwamnatin Katsina domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga baƙi masu zuwa.

Cikin wata hira da BBC, Gwamna Radda ya ce iyalan tsohon shugaban ƙasar za su ci gaba da zama a gidansa da ke Daura domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga masoya da dangi.

Tawagar gwamnatin tarayya da ke Daura ta ƙunshi ministoci kusan 22, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da jinkirta buɗe shafin karɓar bayanan neman aiki na hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (...
17/07/2025

Gwamnatin Najeriya ta sanar da jinkirta buɗe shafin karɓar bayanan neman aiki na hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), hukumar ba da tsaro ga fararen hula (NSCDC), hukumar kula da gidajen gyarin hali (NCoS) da kuma hukumar kashe gobara ta ƙasa (FFS).

Sanarwar jinkirtawar ta fito ne daga ofisoshin da ke da alhakin gudanar da wannan aikin, inda s**a ce matakin na ɗaya daga cikin shirye-shiryen tabbatar da tsari da inganci wajen gudanar da tantancewa da karɓar bayanan sabbin ma’aikata.

Tun da farko, gwamnati ta bayyana cewa za a buɗe shafin ne ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025, amma yanzu ta jinkirta zuwa Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

17/07/2025

LABARAN HANTSI TARE DA BADARU SANI 17 JULY 2025

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP, ba za ta haifar...
16/07/2025

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP, ba za ta haifar da wata matsala ga jam’iyyar ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a yau Laraba.

Makinde, wanda ya kasance babban bako mai jawabi a wani taron bitar ilimi domin bikin cika shekaru 10 da naɗin Oba Aladetoyinbo Aladelusi, Deji na Akure, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a yau Laraba a Akure.

“Ina ganin hakan ba zai yi wa PDP wata illa ba. PDP wata cibiya ce, kuma kowa na da ‘yancin shiga da fita,” in ji shi.

Kano Pillars FC zata rattaba hannun yarjejeniya da Radio France International (RFI Hausa), a matsayin masu ɗaukar nauyin...
16/07/2025

Kano Pillars FC zata rattaba hannun yarjejeniya da Radio France International (RFI Hausa), a matsayin masu ɗaukar nauyin ƙungiyar a ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025.

Ana ganin cigaban na zuwa ne bayan fara aikin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar, Ahmed Musa MON, OON, wanda jagorancinsa ke cigaba da ɗaga matsayin ƙungiyar.

Atiku ya miƙa takardar murabus dinsa ne a yayin shirye-shiryen zaɓen 2027, bayan da ya amince da kafa wata sabuwar jam’i...
16/07/2025

Atiku ya miƙa takardar murabus dinsa ne a yayin shirye-shiryen zaɓen 2027, bayan da ya amince da kafa wata sabuwar jam’iyyar haɗin gwiwa ta ADC

Takardar ficewar tasa, wacce take da kwansn watan Litinin, 14 ga Yuli, 2025, an aike da ita ne zuwa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Jada 1, a karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.

16/07/2025

LABARAN BARKA DA WARAKA HAKA TARE DA KHADIJA SHEHU

16/07/2025

SHIRIN MADUBI TARE DA MUSA ADO MUSA

An kammala binne gawar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.
15/07/2025

An kammala binne gawar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.

15/07/2025

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya iso filin jirgin sama na Katsina da misalin ƙarfe 1:53 na rana tare da gawar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga birnin London.

Manyan baƙi da dama sun isa Daura domin halartar jana'izar marigayi Muhammadu Buhari, ciki har da tsohon Shugaban Nijar,...
15/07/2025

Manyan baƙi da dama sun isa Daura domin halartar jana'izar marigayi Muhammadu Buhari, ciki har da tsohon Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou da Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, tare da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo tare da wasu gwamnoni.

📸 - Gwamnatin Katsina

15/07/2025

Da Dumi Dumi

Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ta bar Landan zuwa Daura da safiyar yau

Address

Kano

Opening Hours

Monday 06:00 - 01:00
Tuesday 06:00 - 01:00
Wednesday 06:00 - 01:00
Thursday 06:00 - 01:00
Friday 09:00 - 01:00
Saturday 06:00 - 01:00
Sunday 06:00 - 01:00

Website

https://stream.zeno.fm/5510fz5kkzzuv

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Vision FM Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share