20/08/2026
Subhanallah! Yan uwa, wani mugun bala'i ya afku a garin Gorau, Goronyo, Jihar Sokoto. Kwale-kwale ya nutse, kuma sama da mutane 40 s**a rasa rayukansu. Wannan abin baƙin ciki ne mai girma.
Muna ta jin labarin rasuwar 'yan uwanmu ta hanyar hatsarin ruwa. Wani lokaci ruwa yana da saukin tafiya, amma wani lokacin kuma yana da hatsarin sosai. Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin kare rayukanmu.
Allah Ya jiƙan wadanda s**a rasu, Ya yi wa iyalansu haƙuri. Mu kuma mu yi addu'a domin su. Muna fatan wannan bala'i zai zama darasi ga kowa.