Hausa Mirror

Hausa Mirror Hausa Mirror zata dinga kawo muku labarai da harshen Hausa da bidiyo na zamani. Zaku Iya Tuntubarmu Ta WhatsApp- 07017233284
(2)

Jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu A Majalisar Dinkin Duniya, Wanda Ya Samu Wakilcin Kashim Shettima."Duniyar 2026 ...
26/09/2026

Jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu A Majalisar Dinkin Duniya, Wanda Ya Samu Wakilcin Kashim Shettima.

"Duniyar 2026 ta fi karfin Tsohon Tsarin Shugabancin 1945. Nahiyar Africa ba zata ci gaba da Biyayya ga Tsarin da bata da Wakilci ba"

Inji Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, ta bakin Mataimakinsa Kashim Shettima.

Ga Karin wasu Gabobi daga jawabin nasa.

1. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin Najeriya na ci gaba da amfani da diflomasiyya, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa, maimakon tilastawa, ware ƙasashe ko amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.

2. Ya yi kira da a gaggauta gyara Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC), yana mai cewa tsarin rarraba iko na shekarar 1945 bai dace da yanayin duniya na shekarar 2026 ba.

3. Najeriya ta buƙaci Afirka ta samu aƙalla kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaro, tare da cikakken haƙƙi da nauyin da ke tattare da kasancewa mamba na dindindin, ciki har da ikon amfani da veto, matuƙar ana ci gaba da amfani da wannan tsarin, da kuma kujeru biyar marasa dindindin.

4. Tinubu ya bayyana shirye-shiryen Najeriya na ƙara taka rawa a harkokin duniya, bisa dogon tarihin ƙasar wajen wanzar da zaman lafiya, sasanci da ayyukan tsaro a Afirka.

5. Ya danganta manufofin harkokin wajen Najeriya da gyare-gyaren tattalin arzikin cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin ingantaccen tsarin tafiyar da tattalin arziki, ƙarfafa hukumomi, saka hannun jari da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu.

6. Najeriya ta yi watsi da ra’ayin cewa dole ƙasashe masu tasowa su zaɓi tsakanin ci gaban tattalin arziki da yaƙi da sauyin yanayi. Ta ce ya k**ata ƙasashe masu tasowa su samu damar bunƙasa masana’antu, rage talauci da faɗaɗa samar da mak**ashi ta hanyoyin da s**a dace.

7. Tinubu ya yi kira da a samar da tallafin kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, fasaha da ƙwarewa, bisa adalci da kuma la’akari da nauyin da ya rataya kan kowa.

8. Najeriya ta sake jaddada Energy Transition Plan da burinta na cimma net-zero nan da shekarar 2060, ta hanyar amfani da mak**ashi mai sabuntawa, tsaftataccen girki, iskar gas a matsayin mak**ashin miƙa mulki, noma mai la’akari da sauyin yanayi da kuma hanyoyin kare muhalli.

9. Tinubu ya yi kira ga duniya da kada ta bari tsoron Artificial Intelligence (AI) ya hana amfani da damar da fasahar ke da ita wajen inganta kiwon lafiya, ilimi, noma, shugabanci da tattalin arziki.

10. Najeriya ta gayyaci ƙasashen duniya su haɗa gwiwa da matasanta a fannin fasaha da kirkire-kirkire, tare da ƙara saka hannun jari a harkokin dijital, broadband, bincike da kasuwancin fasaha.

11. Tinubu ya yi kira da a yi sauyi mai zurfi a tsarin kuɗaɗen duniya, tare da samar da sauƙaƙan rance da tsarin kula da basuss**a da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar saka jari a ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

12. Najeriya ta bayyana African Continental Free Trade Area (AfCFTA) a matsayin muhimmin ginshiƙi na sauya tattalin arzikin Afirka, tare da kira ga nahiyar ta daina dogaro da fitar da albarkatun ƙasa kawai, ta mayar da hankali kan ƙara musu daraja, masana’antu, kirkire-kirkire da tattalin arzikin da ilimi ke jagoranta.

13. A fannin tsaro, Najeriya ta yi kira da a ƙarfafa musayar bayanan sirri, dakile hanyoyin samar da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci da safarar mak**ai ba bisa ƙa’ida ba. Ta kuma jaddada muhimmancin ilimi, damar tattalin arziki, shugabanci na gari da kare haƙƙi da mutuncin al’umma wajen magance matsalolin tsaro.

14. Tinubu ya yi kira da a gaggauta amfani da diflomasiyya wajen magance rikice-rikice, musamman a Sudan, tare da kare fararen hula, tabbatar da isar da agajin jin ƙai da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

15. Najeriya ta bayyana ƙudirinta na fifita haɗin gwiwa maimakon faɗa, tattaunawa maimakon rarrabuwar kai, fata maimakon tsoro, da haɗin gwiwa maimakon warewa, tana mai jaddada cewa Majalisar Ɗinkin Duniya mai gyara, haɗa kowa da inganci na da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, adalci da ci gaba mai ɗorewa a duniya.

Daga Abdulmajid.

A yayin da siyasar Kano ke ci gaba da daukar sabon salo gabanin babban zaben 2027, ana ci gaba da tattaunawa kan alakar ...
25/09/2026

A yayin da siyasar Kano ke ci gaba da daukar sabon salo gabanin babban zaben 2027, ana ci gaba da tattaunawa kan alakar wasu manyan ‘yan siyasa da kuma sabanin ra’ayoyi da ake zargin suna tasowa tsakaninsu.
‎
‎Daya daga cikin abubuwan da s**a jawo ce-ce-ku-ce shi ne dangantakar da ake alakanta tsakanin Hon. Abubakar Kabir Bichi da Sanata Barau I. Jibrin, musamman ganin cewa dukkaninsu ‘yan jam’iyyar APC ne kuma daga Kano suke.
‎
‎Bichi, wanda ke wakiltar Bichi Federal Constituency a Majalisar Wakilai, shi ne Shugaban Kwamitin Appropriations na Majalisar Wakilai ta 10.
‎
‎Dangantakar da aka dade ana magana a kanta
‎
‎A cewar masu bibiyar siyasar Kano, Sanata Barau ya kasance cikin mutanen da s**a tallafa wa Bichi a farkon tafiyarsa a Majalisar Tarayya, musamman wajen ba shi shawarwari da bude wasu hanyoyin siyasa.
‎
‎Ana kuma cewa dangantakar tasu ta samo asali ne tun daga lokacin da Barau yake da kyakkyawar alaka da marigayi mahaifin Bichi, lamarin da ya sa ake kallon Bichi a matsayin wanda Barau ya dauka tamkar karamin dan’uwa.
‎
‎Sai dai wadannan bayanai na dangantakar baya.sun sami tazgade bayan da ake ganin Abba Bichi yana kokarin yakar Barau.
‎
‎Zargin yunkurin hana Barau komawa Majalisa
‎
‎Wasu masu sharhi kan siyasar Kano na zargin cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke kokarin ganin Sanata Barau bai samu damar komawa Majalisar Dattawa ba a 2027.ciki ake zargin Bichi shine ya kunna wannan wutar.saboda ane idan Barau ya dawo majalisa shi kuma Bichi yana yunkurin zai sami speaker to wannan lamarin bazai yiwu ba tubda sun fito da shiyya da.
‎
‎Yanzu bayan Barau ya sami tikitin yakin ya canza salo inda wasu masu bukatun s**a kuma kunno kai inda ake son ayi Masa Anti party kada ya koma majalisa saboda wasu masu bukatun iri daya da na Barau, baza su sami biyan bukatar su wajen neman shugabancin majalisa.
‎
‎Tambayar da ake yi: Me ya sa ‘yan APC za su yi gaba da juna? bayan kowa yana kan arzikin sa.
‎
‎A siyasar jam’iyya, bambancin ra’ayi ba sabon abu ba ne. Amma idan sabanin ra’ayi ya koma rikicin cikin gida, hakan na iya haifar da tambayoyi daga magoya baya.
‎
‎bai k**ata ace ana Jam'iyya daya ba amma ace ana ta hada rikicin sa an yaki Barau ba ko anyi masa anti party.
‎
‎Barau ya nemi hadin kan APC
‎
‎A ranar 29 ga Agusta 2026, rahotanni sun bayyana cewa Barau ya yi kira ga ‘yan APC a Kano North da su hada kai, tare da jaddada cewa bambancin siyasa bai k**ata ya kawo cikas ga ci gaban yankin ba.
‎
‎Wannan kira ya kara nuna cewa Barau shi kullun batun hadin kan jam’iyya ne a gaban sa yana daga cikin muhimman abubuwan da ya bawa Mahimmaci kuma yake tattaunawa a siyasar Kano gabanin 2027.
‎
‎Siyasa tana da rana da dare
‎
‎A karshe, abin da siyasar Kano ta koya shi ne cewa mukami ba ya dawwama har abada. Wanda yake da matsayi a yau, gobe wani na iya maye gurbinsa.
‎
‎Saboda haka, masu ruwa da tsaki suna ganin ya dace bambancin ra’ayi tsakanin ‘yan jam’iyya ya kasance cikin tsarin siyasa mai mutunci, ba tare da mayar da shi rikicin da zai iya raba kan jam’iyya ko al’umma ba ko ya janyo mata faduwa.

BUDADDIYAR WASIKA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, ALH. ABBA KABIR YUSUF; SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KANO, HON. UMAR...
25/09/2026

BUDADDIYAR WASIKA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, ALH. ABBA KABIR YUSUF; SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KANO, HON. UMAR HARUNA DOGUWA; DA MAIGIDANA, RT. HON. KABIRU ALHASSAN RURUM

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

A wannan rana ta Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, na ga ya dace in rubuto muku wannan budaddiyar wasika ne a matsayina na ɗan jam’iyyar APC, kuma ɗan gidan siyasar Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, domin jan hankalinku cikin gaggawa kan wani lamari da ke faruwa a ƙaramar hukumar Bichi.

Jam’iyyar APC, musamman a Jihar Kano, tana cikin shirye-shiryen tunkarar zaɓukan shekarar 2027 da ke tafe. Ina da yakinin cewa tunanin shugabannin jam’iyyar a kullum shi ne yadda za a samu nasara a waɗannan zaɓuka. Sai dai, a halin yanzu, wata sabuwar takaddama ta kunno kai a ƙaramar hukumar Bichi wadda, idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, za ta iya haifar da babbar matsala ga jam’iyyar a zaɓukan da ke tafe.

Kusan mako guda ko sama da haka ke nan da aka fara samun sabani tsakanin magoya bayan Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), wanda ke neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa, da kuma magoya bayan Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi (Abba Bichi).

Abin da da farko ake ganin k**ar ƙaramin rashin jituwa ne, yanzu ya fara ƙara ɗaukar wani sabon salo, inda ba wai kawai ana nuna bambancin ra’ayi tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu ba, har ma an fara samun gasar ajiye muk**ai tsakanin wasu daga cikin mutanen da ke riƙe da muk**ai a ɓangarorin biyu.

A cikin kwanaki uku da s**a gabata, na ga wasu daga cikin magoya bayan Sanata Barau, kusan mutum biyar, sun ajiye muk**an da Hon. Abba Bichi ya ba su, tare da sanar da jama’a cewa sun janye daga tafiyar Abba Bichi, suna kuma bayyana cewa su ’yan Bichi ne kuma ’yan APC.

Haka kuma, a cikin kwanaki biyu da s**a gabata, an samu wasu daga cikin magoya bayan Hon. Abba Bichi da s**a ajiye ko s**a yi watsi da wasu muk**an da Sanata Barau ya ba su, tare da bayyana cewa suna tare da Abba Bichi, kuma ba sa son a danganta su da harkokin siyasar Sanata Barau.

Duk da cewa tazarar da ke tsakanin cikin birnin Kano da Bichi ba ta wuce kimanin mil 40 ba, abin takaici ne idan irin wannan rikici zai ci gaba na tsawon kwanaki ba tare da shugabannin da abin ya shafa sun shiga tsakani ba.

Saboda haka, ina kira tare da jan hankalin Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf; Mataimakin Gwamna, Alh. Murtala Sule Garo; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa; da Jagorana, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, wanda yake ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasar Jihar Kano, da su gaggauta shiga cikin wannan lamari domin shawo kan matsalar kafin ta kai matsayin da zai yi wahalar magance ta.

Abin lura shi ne, duk da irin wannan rikici da ake gani tsakanin magoya bayan Sanata Barau da Hon. Abba Bichi, har yanzu ba a ji daga bakin manyan shugabannin biyu sun fito fili sun dakatar da magoya bayansu daga wannan rikici ba.

Har ma an samu bayani daga mai magana da yawun Sanata Barau a kafafen yaɗa labarai, inda aka bayyana cewa an shiga wani sabon babi na takaddama da Hon. Abba Bichi. Wannan lamari, idan ba a yi gaggawar shiga tsakani ba, zai iya ƙara dagula al’amura a cikin jam’iyyar APC a Bichi.

Saboda haka, ya k**ata a ɗauki matakin gaggawa domin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Bichi kaɗai ba za su iya magance wannan matsala cikin sauƙi ba, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu suna da alaƙa ko biyayya ga ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu.

A wannan lokaci ne nake ganin ya dace Jagorana, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum (Jarumi), ka shiga cikin wannan lamari, domin ina da yakinin cewa kana da kyakkyawar alaƙa da ɓangarorin biyu, kuma hakan zai iya taimaka wajen samar da hanyar sulhu da fahimtar juna.

Burina ba wai in goyi bayan wani ɓangare ba ne, illa dai a samu zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin ’yan jam’iyyar APC a Bichi, domin a kare haɗin kan jam’iyyar kafin zaɓukan 2027.

Allah Ya sa a ɗauki matakin da ya dace, Ya kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jam’iyyar.

Fatihu Yusuf Bichi
Ɗan Jam’iyyar APC, Bichi
Akwati mai lamba 7, Mazabar Sabon Layi

25 ga Satumba, 2026

Al’ummar Tudun Wada sun yaba da ayyukan alheri da ci gaban da Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Soja,...
24/09/2026

Al’ummar Tudun Wada sun yaba da ayyukan alheri da ci gaban da Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Soja, ke gudanarwa, tare da bayyana jin daɗinsu kan yadda ayyukanta ke kawo sauyi a yankin.

Sun kuma sha alwashin sake zaɓar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a karo na biyu, da kuma jam’iyyar APC daga ƙasa har sama.

Haka kuma, sun gode wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa amincewarsa da Sa’adatu Soja a matsayin shugabar ALGON, tare da yaba masa kan goyon bayan da yake ba ta wajen kawo ci gaba a jihar.

Ana Zargin Gwamnatin Kano da K**a ’Yar Kwankwasiyya Fatima Haruna Dayyabu Saboda Adawar SiyasaAna zargin gwamnatin Jihar...
24/09/2026

Ana Zargin Gwamnatin Kano da K**a ’Yar Kwankwasiyya Fatima Haruna Dayyabu Saboda Adawar Siyasa

Ana zargin gwamnatin Jihar Kano da k**a Fatima Haruna Dayyabu, wadda aka bayyana a matsayin ’yar tafiyar Kwankwasiyya, bisa zargin cewa an k**a ta ne sak**akon adawar siyasa.

Rahotanni sun ce an gurfanar da Fatima Haruna Dayyabu a gaban kotu, inda aka fara gudanar da shari’ar ta.

Masu goyon bayanta sun bayyana damuwa kan lamarin, inda s**a ce suna kallon matakin a matsayin wani abu da ya shafi bambancin ra’ayin siyasa.

Sai dai, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin Jihar Kano da ta tabbatar da dalilin k**a Fatima ba.

Me za ku ce?

“Shi kansa Tijjani Gandu yana cikin yan takarar da za'a canja, amma na dakatar da abin saboda alakarsa da Kwankwaso.”Hon...
23/09/2026

“Shi kansa Tijjani Gandu yana cikin yan takarar da za'a canja, amma na dakatar da abin saboda alakarsa da Kwankwaso.”

Hon. Hussaini Isah Mairiga
(Shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kano)

Shugaban kungiyar tallata manufofin shugaban kasa Tinubu ta PBAT Door to Door Movement a yankin Arewa Maso Gabas, Comr. ...
23/09/2026

Shugaban kungiyar tallata manufofin shugaban kasa Tinubu ta PBAT Door to Door Movement a yankin Arewa Maso Gabas, Comr. Zakari Hashim, ya gamu da wani gagarumin hadarin mota a jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne yayin da yake kan hanyarsa ta tafiya birnin Maiduguri na jihar Borno, inda yake shirin halartar wani muhimmin taro na kungiyar.

“Ba abin mamaki ba ne Sha’aban Sharada ya yi rijistar zama ɗan NDC, domin doka ta ba shi damar yin hakan. Haka kuma, jam...
23/09/2026

“Ba abin mamaki ba ne Sha’aban Sharada ya yi rijistar zama ɗan NDC, domin doka ta ba shi damar yin hakan. Haka kuma, jam’iyyar ta tanadi damar yin rijistar zama ɗan jam’iyya ta yanar gizo.”

— Hon. Hussaini Isah Mairiga, Shugaban Jam’iyyar NDC na Jihar Kano.

Me kuke tunani game da wannan batu?

“Idan muka ci zaɓe, za mu dawo da tallafin man fetur ta hanyar da muka ga ta dace” — Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso.
23/09/2026

“Idan muka ci zaɓe, za mu dawo da tallafin man fetur ta hanyar da muka ga ta dace” — Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso.

“Abin mamaki! Ashe Sha’aban Sharada na cikin jerin ’yan takarar jam’iyyar NDC.”-Sanata Rabi`u Musa KwankwasoJagoran Kwan...
23/09/2026

“Abin mamaki! Ashe Sha’aban Sharada na cikin jerin ’yan takarar jam’iyyar NDC.”

-Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya

Address

Kano
700101

Telephone

+2348056667299

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Mirror posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share