09/01/2024
LAYMAN THINKING
Yau na je shagon siyar da kayayyakin electronics components a kasuwar Sabon Gari sai na hadu da wani ya karbi wani component, sai na tambaye shi, mene wannan? Sai yace inverter ce ta TV power supply. Kuma sai na ga ya karbi electrolytic capacitor 400v 47uF, I think. Sai na ce da shi, "ana samun 2200uF 35v kuwa?" Sai yace: "Aa sai dai 2200V", “30V shi ne input 2200uF shi ne output. Idan kasa 2000uF a gun 400v zai fashe, in kuma 400V ne wutar bazata kai ba”. Ni dai kawai na ce “Na gane.”
35V INPUT, 2200uF kuma OUTPUT. Wai!
Shine abinda 'yan boko ke cewa: "Layman Thinking". Zahiri yasan aikin shi. Sabanin 'yan takarda. Kusan haka na fada ga wani engineer da yake solar installation. Banda wannnan akwai wani yaro dazu a inda nake IT ya ce: "Ku kun je Jamia'a, kun yi a makaranta”. Ni kuma na ce da shi:“Kai kuma da kake hannun daman Engineer”. Gaskiya da ace Engineer zai je jamia‘a, watakila in ba'a bashi prof. ba, yayi managing da Dr., Ya koyar da dalubai masu yawa, wasu sun yi companies, duk sun sami rufin asiri. Shima yana ta aiyuka da yawa na electronics, yana samun na kashewa. Ga dalubai, ko yau akwai wasu daga poly, Buk, FUD da sun zo gurin sa an dora su kan hanyar final year project din su. Ga 'yan Siwes, 'yan special classes, da sauransu. Amma fa shi karanta yay a jami'a.
Abin nufi nan shi ne, don kana koyon engineering ko wani course, a jami'a ko polytechnic, karka raina duk wanda ka gani mai sana'a da ta shafi abinda kake karanta ganin shi bai je jami'a ba. Da yawa sun fi wasu 'yan makarantar Naseebi da sanin ainihin iliman a zahiri.
Learn by doing.
Practice makes perfect.
Use it or lose it.
"It's not about what you learn. It's about what you do with what you learn, that makes a difference. " - Nishant Kasibhatla.
Naseeb TECH
Arewa Explorer