Kannywoodstyle

Kannywoodstyle Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kannywoodstyle, News & Media Website, Zoo Road, Kano.
(4)

K-S Leading online multi-lingual entertainment media solely to keep you abreast with News, Trailer, Photos & Happening in Kannywood film industry

For ADVERT send Mail 👇🏻👇🏻

HABIBA DORAYI TA ZIYARCI SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR GWALEƘungiyar Kano First TikTokers, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Habiba...
27/08/2026

HABIBA DORAYI TA ZIYARCI SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR GWALE

Ƙungiyar Kano First TikTokers, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Habiba Dorayi, ta kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, Hon. Abubakar Mu’azu Mojo.

Ziyarar ta kasance domin ƙarfafa alaƙa tare da tallata ayyukan Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, da kuma wayar da kan jama’a kan manufofin jam’iyyar APC.

A yayin ziyarar, tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya ƙarfafa musu gwiwa kan ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta wajen wayar da kan jama’a.

YANZU - YANZU; Maryam Ibrahim Dan Azumi daga Jihar Gombe ta samu matsayi na 1 a rukunin Hizb 60 tare da Tafsir, a gasar ...
19/08/2026

YANZU - YANZU; Maryam Ibrahim Dan Azumi daga Jihar Gombe ta samu matsayi na 1 a rukunin Hizb 60 tare da Tafsir, a gasar ƙasa da ƙasa ta Alƙur’ani mai girma ta King Abdulaziz International Holy Qur’an Competition da aka kammala a Masarautar Saudiyya.

Masha Allah! 🤲❤️ Wannan babbar nasara ce da ta zama abin alfahari ga Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Allah Ya ƙara mata basira, Ya sanya Alƙur’ani ya zama haske da hujja a gare ta. 🤲📖✨

Director Mujahid M. Soja ya ba masoya mawakan Hamisu Breaker, Umar M. Shareef da Nazifi Asnanic haƙuri kan rashin ganin ...
07/08/2026

Director Mujahid M. Soja ya ba masoya mawakan Hamisu Breaker, Umar M. Shareef da Nazifi Asnanic haƙuri kan rashin ganin waƙoƙinsu a cikin Album ɗin LAILA da aka saki a jiya.

Daraktan ya bayyana cewa ya samu koke-koke daga masoyan mawakan, kasancewar tun farko ya yi alƙawarin sakin waƙoƙi 11 na kundin LAILA.

Sai dai ya yi uzuri cewa ya zaɓi fara sakin waƙoƙi bakwai ne domin bai wa masu sauraro damar jin su yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa za a saki ragowar waƙoƙin bayan kammala ɗaukar shirin LAILA.

Shirin LAILA dai na ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen da ake ɗauka a yanzu, inda fitattun jarumai kamar Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Umar M. Shareef da Amal Umar ke jagorantar fitowa a cikinsa.

A halin yanzu, waƙoƙi bakwai da aka fara saki suna samuwa a tashar YouTube ta M.SOJA CONCEPT.

Ummah Shehu tare da ’yarta cikin hoto mai cike da farin ciki da ƙaunar uwa da ’ya.Masha Allah! Allah Ya raya cikin imani...
02/08/2026

Ummah Shehu tare da ’yarta cikin hoto mai cike da farin ciki da ƙaunar uwa da ’ya.

Masha Allah! Allah Ya raya cikin imani da albarka. 💖

Muna gabatar muku da Amal Umar a cikin shirin LAILA 😍🔥✊Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai zamu fara daukar shirin LAILA...
02/08/2026

Muna gabatar muku da Amal Umar a cikin shirin LAILA 😍🔥✊

Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai zamu fara daukar shirin LAILA 5 ga watan August insha Allah 🔥✊️

Sannan a wannan rana muke sa ran insha Allahu zamu saki kundin wakokin LAILA 🎙🎶😍🔥

Sannan muna muku kyakkyawan Albishir din cewa insha Allahu zakuji dadin wannan shiri da zamu kawo muku ✔️

LAILA shiri ne mai gajeran zango Episode 7 ne kawai amma na tabbata sai kunso a cigaba 🤪

Tun yanzu ku shiga YouTube Channel mai suna M.SOJA CONCEPT kuyi subscribing ku danna karararrawar sanarwa domin sanar daku dazarar mun fara sakin LAILA 🎬

Wannan shiri zai zo karkashin kamfanina na M.SOJA CONCEPT NIG.Ltd ✍️

Muna Bukatar Addu'arku 🙏

Director Malam Aminu Saira, tare da amaryarsa da uwargidansa, cikin hoto mai matuƙar kayatarwa.Masha Allah! Allah Ya daw...
02/08/2026

Director Malam Aminu Saira, tare da amaryarsa da uwargidansa, cikin hoto mai matuƙar kayatarwa.

Masha Allah! Allah Ya dawwamar da farin ciki da haɗin kai a tsakaninsu. ❤️

Jaruma Maryam Yahaya
28/07/2026

Jaruma Maryam Yahaya

Munasa ran insha Allahu zamu saki Album din shirin LAILA 5th August 2026 🎙🔥Mawaƙan da za su rera waƙoƙin sun haɗa da:* N...
26/07/2026

Munasa ran insha Allahu zamu saki Album din shirin LAILA 5th August 2026 🎙🔥

Mawaƙan da za su rera waƙoƙin sun haɗa da:

* Nazifi Asnanic
* Umar M. Shareef
* Hamisu Breaker
* Abdul D One
* Sadiq Sale
* Umar MB
* Hairat Abdullahi
* Hussaini Danko
* Halifa SK Dorayi
* Maryam A. Sadik
* Real Obey

🎬 Director: Mujahid M. Soja

A cikin waɗannan mawaƙa, wanne ne kuka fi ɗokin jin waƙarsa a cikin kundin waƙoƙin LAILA? Ku faɗa mana a comment! 👇🎵🔥

Mawaƙa 11 ake sa ran za su rera waƙoƙi a cikin shiri mai gajeren zango na LAILA, wanda fitaccen darakta Mujahid M. Soja ...
25/07/2026

Mawaƙa 11 ake sa ran za su rera waƙoƙi a cikin shiri mai gajeren zango na LAILA, wanda fitaccen darakta Mujahid M. Soja zai bada umarni.

Mawaƙan da za su rera waƙoƙin sun haɗa da:

* Nazifi Asnanic
* Umar M. Shareef
* Hamisu Breaker
* Abdul D One
* Sadiq Sale
* Umar MB
* Hairat Abdullahi
* Hussaini Danko
* Halifa SK Dorayi
* Maryam A. Sadik
* Real Obey

🎬 Director: Mujahid M. Soja

A cikin waɗannan mawaƙa, wanne ne kuka fi ɗokin jin waƙarsa a cikin kundin waƙoƙin LAILA? Ku faɗa mana a comment! 👇🎵🔥

24/07/2026

Abaka Auren Wadda Kakeso
Yafi Abaka Million 100
🤧

Address

Zoo Road
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kannywoodstyle posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share