Aminchi Sports

Aminchi Sports Maraba da zuwa shafin Aminchi Sports shafin da yake kawo muku ingantattun labaran wasanni da cikin gida da kasashen ƙetare.

Shafin da ke wayar da kan matasa akan harkar Crypto, musamman Mining da Trading...

Shekaru 22 kenan rabon da a zurawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kwallaye 3 cikin mintuna 24 na farko da fara was...
10/07/2025

Shekaru 22 kenan rabon da a zurawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kwallaye 3 cikin mintuna 24 na farko da fara wasa, sai a daren jiya da PSG tayi wannan babban aiki.

A ranar 9 ga watan Nuwamba 2003, Sevilla ta samu nasara akan Madrid inda Kuma ta jefa kwallaye 3 cikin minti 25 da fara wasa,Yan wasan da s**ayi wannan aika-aika ga Real Madrid a waccan lokaci sune:

Dani Alves
Dario Silva
Da Kuma Ivan Helguera da yaci gida wato own goal.

, Alonso.

Shekaru 7 da s**a gabata irin wannan rana Cristiano Ronaldo ya tsallaka kungiyar kwallon kafa ta Juventus daga Real Madr...
10/07/2025

Shekaru 7 da s**a gabata irin wannan rana Cristiano Ronaldo ya tsallaka kungiyar kwallon kafa ta Juventus daga Real Madrid kan kudi £95:

Wasanni 🏟️ 134
Kwallaye ⚽ 101
Taimakawa aci kwallo 🅰️ 22

Gasar 🏆 2x Serie A
Gasar 🏆 1x Coppa Italia
Gasar 🏆 2x Supercoppa Italiana

, ,

An Yi Jana’izar Diogo Jota da Ɗan’uwansa a Gondomar Bayan Mummunan Haɗarin MotaAn yi jana’izar ɗan wasan gaba na Liverpo...
10/07/2025

An Yi Jana’izar Diogo Jota da Ɗan’uwansa a Gondomar Bayan Mummunan Haɗarin Mota

An yi jana’izar ɗan wasan gaba na Liverpool da ƙasar Portugal, Diogo Jota, da ƙanensa, a ranar Asabar a Gondomar, garinsu na haihuwa, bayan rasuwarsu a wani haɗarin mota da ya girgiza duniya.

Tarin jama’a daga ko’ina, ciki har da abokai, iyalai da fitattun 'yan wasa, sun halarci jana’izar domin girmama rayuwarsu. Babban Bishop na Porto ne ya jagoranci addu’o’in, yayin da aka yi jimamin wannan babban rashi cikin nutsuwa da girmamawa.

A makon da ya gabata ne duniya ta wayi gari da labarin mutuwar Diogo Jota da ɗan’uwansa, bayan sun yi haɗari a cikin mota yayin tafiya. Wannan lamari ya girgiza masoya wasanni, musamman ‘yan ƙwallon ƙafa da masu goyon bayan Liverpool.

Rasuwar Jota ta bar babban gibi a ƙungiyar Liverpool da kuma cikin tawagar Portugal, inda ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan wasa mafi ƙwazo a 'yan shekarun nan. Ana ci gaba da aiko da saƙonnin ta’aziyya daga kungiyoyi da magoya baya daga sassa daban-daban na duniya.

Wacce kungiya ce zata iya kai wa zagayen karshe a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi tsakanin Real Madrid da PSG a Dare...
09/07/2025

Wacce kungiya ce zata iya kai wa zagayen karshe a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi tsakanin Real Madrid da PSG a Daren yau.

Menene hasashen ku??

, ,

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi.Godiya ga dan wasa Joao Pedro...
08/07/2025

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi.

Godiya ga dan wasa Joao Pedro, da ya zura kwallaye biyu a wasan sa na farko cikin rigar Chelsea.

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Golan Super Eagles, Peter Rufai, Ya Rasu.Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon golan ƙungiyar ƙw...
03/07/2025

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Golan Super Eagles, Peter Rufai, Ya Rasu.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon golan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, Peter Rufai.

An bayyana cewa marigayin ya rasu ne da safiyar yau Alhamis yana da shekaru 61 a duniya.

Rufai ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan da s**a wakilci Najeriya a manyan wasanni na duniya, kuma ya bar tarihi mai ɗimbin armashi a fagen wasanni.




22/06/2025

Captain din Super Eagle, Ahmad Muss, ya 6ana da kokarin kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Afirka wadanda suke bugawa gasar Club Wolrd Cup.

18/06/2025

Zlatan Ibrahimovic ya bayyana manyan 'yan baya guda biyar mafi ƙarfi da ya taɓa fuskanta a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Waɗannan yan wasan kuwa su ne Alessandro Nesta, Jaap Stam, Giorgio Chiellini, paulo Maldini da Thiago Silva.

Ibrahimovic ya bayyana Maldini da Nesta a matsayin manyan kwararrun 'yan baya na Italiya, yayin da ya kwatanta Thiago Silva da shi kansa a bangaren tsaro. Jaap Stam kuwa, ya ce yana da karfi da kuma iya bayar da tsaro a filin wasa.

Chiellini kuwa, ya bayyana a matsayin jarumi wanda ya taka rawar gani a Juventus da ƙasar Italiya. Dukkaninsu sun bar tarihi mai ban mamaki.


Shin ko ka yarda da Ibrahimovic a wanna ɓangaren?

18/06/2025

Yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sun tunkari Nico Williams ƙaitsaye tare da neman alfarmar cewa ya fara tuntuɓar ƙungiyar ta Barcelona kafin yayi tunanin komawa kungiyar kwallon ƙafa ta Bayern Munich ko kuma Arsenal,

Tun a ƙakar wasannin da ta gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelonan ta ke nuna tsananin sha'awarta ga ɗan wasan, sai dai bayan kai ruwa rana ya yi watsi da ƙoƙarin barin ƙungiyar ta sa ta Athletic Bilbao, har zuwa wannan shekarar.

Shin ko yanzu ka na ganin zai karɓi tayun kungiyar kwallon kafar ta Barcelona? Kuma wacce rawa ka ke ganin zai taka a ƙungiyar?

Pep Guardiola ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a Gaza...Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City,...
12/06/2025

Pep Guardiola ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a Gaza...

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bukaci duniya da kada ta ci gaba da kauda kai daga azabar da al’ummar Gaza ke fuskanta, sakamakon hare-haren Isra’ila da kuma dogon kulle da ake yi wa yankin.

Da yake jawabi a Jami’ar Manchester inda aka karrama shi da digiri na girmamawa a ranar Litinin, Guardiola ya bayyana cewa: “Abin da ke faruwa a Gaza yana da matukar radadi. Yana taba ni a dukkan jikina.”

Ya ce wannan lamari ba na siyasa ba ne, kuma ba batun wanda ya fi gaskiya ba ne: “Kawai maganar jin kai ce, da kaunar rayuwa da kulawa da ƴan-adamtaka.”

An karrama Guardiola ne bisa nasarorinsa a fagen kwallon kafa da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen walwalar al’umma ta hanyar gidauniyar danginsu wato 'Guardiola Sala Foundation'.

Guardiola ya kara da cewa: “Wata kila muna ganin yara ‘yan shekara hudu ko biyar na mutuwa sakamakon bam ko rashin kula a asibiti. Muna tunanin ba abin da ya shafe mu bane. Amma ku kula, gobe wani daga cikinmu ne zai shiga wannan hali.”

Ya danganta damuwarsa da halin da ya ke ciki a matsayinsa na uba, yana cewa duk lokacin da ya kalli yaransa Maria, Marius da Valentina, yana ganin irin tsoron da ya ke ji saboda abinda ke faruwa da yaran Gaza tun da wannan masifa ta fara.

Duk da muhimmanci da girman wannan maganar ta Guardiola, Jami'ar da ta gayyaceshi domin karramashi ba ta wallafa jawabin nasa a shafinta na yanar gizo ba, musamman inda ya shafi rikincin Gaza.

Portugal sun samu nasarar lashe gasar Nations League, bayan samun nasara akan Spain a bugun Penality...
08/06/2025

Portugal sun samu nasarar lashe gasar Nations League, bayan samun nasara akan Spain a bugun Penality...

Ronaldo, yanzu wasa  2 da 2
08/06/2025

Ronaldo, yanzu wasa 2 da 2

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminchi Sports posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminchi Sports:

Share