25/06/2025
*Fim ɗin "MAA"*
*Wanda zai fita*
*Ranar: 27 ga Yuni, 2025*
*Fim ɗin "MAA" wani sabon fim ne mai cike da darasi, tausayi da ƙarfafa gwiwa, wanda ke duba rayuwar uwa da ƙalubalen da take fuskanta wajen kare iyalinta da tabbatar da jin daɗin 'ya'yanta. Wannan fim ɗin yazo da labari mai taba zuciya, inda Kajol, fitacciyar jarumar Bollywood, ta fito da rawar da ta fi dacewa da ita — uwa mai ƙarfi, kauna da jajircewa.*
🌟 Meyasa Ya dace a Kalli Fim ɗin?
*Labari mai zurfi: Fim ɗin "MAA" ya ƙunshi cikakken sako mai tasiri kan muhimmancin uwa da sadaukarwa.*
*Jarumta ta gaske: Kajol ta sake bayyanar da hazakarta ta musamman, inda ta nuna jarumta da ƙarfin zuciya a cikin kowane mataki na fim ɗin.*
Kyawawan kalmomi da zance masu ratsa zuciya, kamar:
*> “Uwa bata fitar da hawaye don ta karaya ba, sai don ta fi ƙarfi fiye da kowa.”*
*“Rayuwar da ba a ambaci sunan uwa ba, tamkar rubutu ne da babu salo.”*
👏 Yabo Ga Kajol
*Kajol ta yi fice wajen bayyana soyayya, damuwa da jajircewar uwa cikin fasaha. A cikin fim ɗin, ta nuna ƙarfin hali da basira ta yadda kowanne mai kallo zai ji kamar yana kallon rayuwar kansa ne. Wannan rawar nata za ta kasance ɗaya daga cikin mafiya tasiri a tarihin aikinta.*
📢 Kar Ku bari a baku Labari!
*Fim ɗin "MAA" ba wai kawai fim ba ne, darasi ne, daraja ce ga uwa, kuma ƙarfafawa ce ga duk wanda ke buƙatar karfin gwiwa a rayuwa. Ku shirya, ku je sinima ranar 27 ga Yuni, Lallai Ka adana ticket dinka domin garzayawa kasar India domin ganewa Idonka, kada ka jira Kace har se an sake shi gabadaya, ku je ku ga yadda fim ɗin zai taba zuciyarku.*
Abdulhameed Kul-kul ✍🏿