Gtv Hausa News

Gtv Hausa News GTV Hausa Tashar gidan talabijin nakawo labaran duniya a harshen Hausa tareda hirarraku da fittatu

25/05/2024

Sarki Sanusi Lamido Sanusi

Gtv Hausa

23/05/2024

Yanzu-Yanzu: An k**a wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Gusau, jihar Zamfara. Kalli yadda suke bada bayanai.

Matashi Ya Hallaka ‘Yar Uwarsa 'yar shekara 6 Bayan Ya Yi Garkuwa Da Ita, Ya Turbudeta A Kango An k**a wani matashi  Abd...
13/05/2024

Matashi Ya Hallaka ‘Yar Uwarsa 'yar shekara 6 Bayan Ya Yi Garkuwa Da Ita, Ya Turbudeta A Kango

An k**a wani matashi Abdulazeez Idris, mazaunin unguwar Jama’a da ke ƙaramar hukumar Maƙarfi a Jihar Kaduna, kan zargin sace ‘yar uwarsa ‘yar shekara 6 tare da kashe ta da kuma turbude gawarta a kango.

Gtv hausa

Jami'in Kwatsam Ya Harbe Kansa A  Banɗaki A KanoWani jami’in hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa, Abdulwahab Magaji, dake a...
13/05/2024

Jami'in Kwatsam Ya Harbe Kansa A Banɗaki A Kano

Wani jami’in hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa, Abdulwahab Magaji, dake aiki a babban birnin tarayya, ya harbe kansa har lahira a gidansa da ke Garin Centre a Kano, lamarin ya faru a yau Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa iyalan mamacin sun bayyana cewa Marigayin ya harbe kansa da bindiga, lamarin da ya sa jami’an ‘yan sanda s**a ziyarci inda lamarin ya faru, kuma bayan an garzaya da mamacin zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Mai magana da yawun rundunar Kwastam ta kasa Abdullahi Maiwada ya tabbatar muna da mutuwar jami'in Kwatsam Abdulwahab Magaji, ya ce an gano gawarsa ne a banɗaki a gidansa da ke jihar Kano, "jami'in yana aiki ne a Abuja amma a Kano lamarin ya faru, sai dai zuwa yanzu ana binciken musababbin rasuwarsa, ba zamu iya faɗa ko shi ne ya kashe kansa ba ko a'a, har sai abinda bincike ya tabbatar". In ji Abdullahi Maiwada.

Tuni dai aka bai wa iyalan mamacin gawarsa, domin yi mata sutura k**ar yadda Musulunci ya tanadar.

Gtv hausa

Yan Bindiga Sunkai hari a Kauyen Sakajiki a karamar hukumar mulkin  Kaura Namoda Dake Jihar Zamfara.  A  Daren Jiya.GTV ...
09/05/2024

Yan Bindiga Sunkai hari a Kauyen Sakajiki a karamar hukumar mulkin Kaura Namoda Dake Jihar Zamfara. A Daren Jiya.

GTV Hausa

HOTUNA: Yadda sojojin Najeriya su ka kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kwato mak**ai daga hannun ƴa...
05/05/2024

HOTUNA: Yadda sojojin Najeriya su ka kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kwato mak**ai daga hannun ƴan bindiga a jihar Taraba.

GTV Hausa

Akawu ya maka mai-ɗakin sa da ƴansanda a kotu bisa shirin k**a shi kan zargin cin-amanaWani akawu kuma ɗan kasuwa, Paul ...
05/05/2024

Akawu ya maka mai-ɗakin sa da ƴansanda a kotu bisa shirin k**a shi kan zargin cin-amana

Wani akawu kuma ɗan kasuwa, Paul Makolo ya shigar da ƙara a gaban Babbar kotun jiha da ke Ikeja a jihar Legas, inda ya maka rundunar ƴansanda da kuma matar sa, Endurance Modupe Makolo.

Makolo ya nemi kotu ta bi masa hakkinsa na take cuzguna masa da matarsa ke yi da hadin kan ƴansanda , duba da sashe na 35 da 46 na kundin tsarin mulkin Nijeriya (1999).

Waɗanda Akawun ke kara sun hada da Kwamishinan Ƴansanda na Legas, DPO din Caji-ofis din Anthony, Istifanus Danielda kuma matar ta da Endurance.

A ƙarar, Makolo yayi korafn cewa waɗanda ake kara sun cuzguna masa tare da hana shi ya yi rayuwar sa, inda ya ce hakan ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulki kuma an saɓa wa doka.

Saboda haka Makolo ya nuna cewa hakan ya saɓawa doka.

GTV Hausa

Rikincin Kasuwar Kayan Abinci Ta Ilepo A Legas, Rikicin Da Ya Barke A Kan Naira Dubu 2 Kudin C**a, Wanda Ya Janyo Salwan...
02/05/2024

Rikincin Kasuwar Kayan Abinci Ta Ilepo A Legas, Rikicin Da Ya Barke A Kan Naira Dubu 2 Kudin C**a, Wanda Ya Janyo Salwantar Kayayyakin Daruruwan Miliyoyin Naira.

GTV Hausa

BABBAN LABARI Gwamnatin zamfara ta Haramtawa dukkanin masu Muk**an siyasa da shuwagabannin hukumomin Gwamnati Hira da ya...
22/04/2024

BABBAN LABARI

Gwamnatin zamfara ta Haramtawa dukkanin masu Muk**an siyasa da shuwagabannin hukumomin Gwamnati Hira da yan Jarida, ko saka wani Shiri nasu a kafafen Rediyo television ko kafafen sada zumunta har sai sun nemi izinin gwamnatin

Zan Wargaza Ɗaukakata Da Kaina In Canza Sana'a. Ina Ganin Kamar Idan Na Daina Fim Ba mútuwa zan yi ba, Céwar Adam A.  Za...
16/04/2024

Zan Wargaza Ɗaukakata Da Kaina In Canza Sana'a. Ina Ganin Kamar Idan Na Daina Fim Ba mútuwa zan yi ba, Céwar Adam A. Zango

A daidai lokacin da ya fidda bidiyoyi ya furta maganganun da s**a jawo cece-ku-ce a shafukan sadarwa na zamani, fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Adam A. Zango ya sake wallafa wani saƙo a shafinsa inda ya bayyana cewa matsalolinsa da ake gani a yanzu ya jima da su, kuma ya daɗe yana bayyana su ta cikin waƙoƙinsa amma abokan sana'arsa sun kasa fahimtarsa.

Jarumin ya bayyana haka ne ta cikin shafinsa k**ar yadda Jaridar GTV Hausa ta ruwaito inda ya ce: "Na daɗe ina faɗa muku matsalata a cikin waƙoƙina amma kun kasa fahimtata".

Zango ya kuma ƙara da cewa zai yi yaƙi a kan ƴancinsa da abubuwan buƙatarsa na rayuwa. Dan haka "ba sai kun sha wahala ba bayan na mutu k**ar yadda ƴan Kudu s**a yi a kan (Moh Bad)". In ji shi.

Daga nan ya cigaba da cewa "Zan wargaza ɗaukakata da kaina in canza sana'a. Ina ganin k**ar idan na daina fim ba mutuwa zan yi ba. Bakin da Allah Ya tsaga ba zai hana shi abinci ba. Kun san ni na san ku, kun san abin da nake aikatawa a ɓoye na san naku. Shekara goma sha takwas kuna azabtar da ni. Mu zuba mu gani, kun san komai kuka bari ana wulaƙanta ni". Cewar Adam A. Zango.

Jarumin ya kuma yi nuni da cewa "matata ta farko aurenta ɗaya, matata ta biyu aurenta biyu za ta yi na uku, matata ta uku aurenta huɗu za ta yi na biyar, matata ta huɗu aurenta uku, matata ta biyar aurenta biyu za ta yi na uku, matata ta shida aurenta ɗaya za ta yi na biyu. Shin ƙaddararsu ce haka ko su ma auren ɗanɗano suke k**ar yadda kuka ce nake yi ?". In ji shi.

Address

Kano

Telephone

+2349034363006

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gtv Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gtv Hausa News:

Share