17/07/2024
Wata kotun tarayya a Legas ta kori wata kara da ta nemi a cire rubutun Ajami daga jikin takardun kudin Nijeriya, naira.
Kotun karkashin Mai Shari’a Yellin Bogoro ta ce lauyan da ya shigar da karar ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji cewa rubutun yana nuna Nijeriya tana bin tsarin addinin Musulunci, sabanin kasancewarta wacce ba ruwanta da addini, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Lauyan da ya shigar da karar a 2020, Cif Malcolm Omirhobo, ya bukaci kotun ta umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sauya rubutun ajami daga jikin kudin kasar zuwa na Ingilishi, wanda shi ne harshen da aka amince da shi a hukumance, ko kuma a sauya da daya daga harasan Nijeriya uku, Hausa ko Yaruba ko Igbo.
A yayin shari’ar dai, Babban Bankin Nijeriya ya musa da’awar da mai shigar da karar ya yi na cewa, amfani da Ajami a jikin kudin kasar na nuna Nijeriya ta karkata zuwa ga addinin Musulunci.