22/10/2025
DA DUMI-DUMI: ‘Yan sanda sun k**a manyan masu fataucin miyagun ƙwayoyi a Jihar Jigawa.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta k**a wasu manyan masu fataucin miyagun ƙwayoyi uku a yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya tabbatar da k**a mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Ya bayyana cewa, samamen da aka gudanar ranar 18 ga Oktoba, 2025, ya haifar da nasarar k**a waɗanda tuni ‘yan sanda ke bibiyarsu saboda hannu da suke da shi wajen rarraba miyagun ƙwayoyi a cikin jihar Jigawa da wajen ta.
SP Shiisu ya ce a lokacin samamen, jami’an ‘yan sanda sun gano nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban.
Kayan da aka kwato sun haɗa da:
Exol (13,505), D5 (1,583), Tramadol (3,572), Diazepam (565), Rubber Solution (2,469), tabar wiwi (block da wraps 886), Suck and Die, Akuskura, Farin Malam (340), da sauran miyagun ƙwayoyi da abubuwan maye (1,042).
An gano waɗanda aka k**a da sunayensu k**ar haka: Muhammad Garba, Musa Garba, da Hudu Ma’ilu, dukkansu mazauna ƙauyen Guneri, gundumar Malamawa, daga Jamhuriyar Nijar.
Ya ƙara da cewa waɗanda aka k**a suna hannun ‘yan sanda yanzu haka ana gudanar da cikakken bincike a kansu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala binciken farko.
Kwamishinan ‘yan sanda ya yaba da ƙwazon jami’an da s**a gudanar da samamen tare da jaddada matsayar rundunar kan rashin sassauci ga laifukan da s**a shafi fataucin miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, ya roƙi jama’a da su ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci don taimakawa wajen gano da kuma k**a masu aikata laifuka.