
04/06/2025
Koken Nura Kasafi Ga Gwamnati 👇 Allah yasa Ta duba Ayi Aikin 👇👇
Dole Fa Hankalin Mu Ya Tashi Akan Harkar Nan Sama Da Shekara 10 Muna Kiraye Korayen Azo Ayi Mana Aikin Titunan Mu Amma An Wafantar Damu.
Mun Zaɓi Ɗan Majalisar Tarayya Na APC Ya Kasa.
Mun Zaɓi Ɗan Majalisar Jaha Na APC Ya Kasa
Mun Zaɓi Senator Na APC Ya Kasa
A 2023 Akwai Ɗan Unguwarmu Da Ya Futo Takarar Majalisar Tarayya Amma Muka Kayar Dashi Mu Tura Wakili.
Yau Shekara Biyu Wakili Na Jam'iyar NNPP Wanda Ya Samu Nasara Da Gagarumin Rinjaye a Gayawa Duk Da Cewa Akwai Badaru Umar Gayawa Haka Muka Ƙi Zaɓar Shi Muka Zaɓi Wakili Amma Ya Wafantar Damu.
Dukkan Waɗanda Muke Da Ƙwarin Gwiwa Akan Su Duk Sun Kasa Gwamna Ya Fara Rage Wasu Ayyukan Amma Fa a Halin Da Gayawa Take Ciki Indai Ba Gaba Ɗaya Akayi Aikin Nan Ba Za'a Dena Ƙorafi Ba Saboda Babu Inda Baya Buƙatar Agajin Gaggawa.
Yak**ata Akawo Mana Ɗauki😭
Nura Kasafi ✍️✍️