17/09/2025
Hakan ya biyo bayan cikakken bincike da hukumomin kasar Saudiya s**a gudanar, tare da tabbatar da cewa mutanen da ake zargin basu da laifi, bayan sun shafe makonni 4 a tsare.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Sadiq.
Rahotonni sun bayyana cewa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano aka sanyawa mutanen miyagun kwayoyi a cikin kayansu, yayin da suke shirin tafiya zuwa kasar Saudiya domin gudanar da aikin Umara, inda suna isa birnin Jiddah aka k**a su.