22/04/2025
Daga cikin abinda yake raunata tunani kuma yake hana cigaban wasu matasan mu na Arewa shine zancen da ake dogara dashi cewa (ai wane yaki yayi mun hanya, wane bai taimaka mun ba, wane yaki ya 'daga Ni).
~ Kar ka dogara da sai wani yayi maka hanya, ko kuma sai wani ya 'daga ka, kayi abinda zaka iya, Allah zai 'daga ka har fiye da inda kake zato, shima wanda kake cewa yaƙi yayi maka hanya ko ya 'daga ka idan ka kula shima ba wani ne ya 'daga shi ba. Kokari ne kawai da jajircewa har Allah ya kai shi inda ka ganshi a yau.
Idan ka zauna kana jiran sai wane ya 'daga ka to da wahala ka kai inda kake so a rayuwar yau.
Lokacin da kake 'kokarin zama wani babu wanda zai damu da kai, lokacin kai ba kowa bane, baka da komai, babu wanda zai ga darajar ka ko kimar ka har sai ka kai inda kake so ko kuma kayi rabi. So, ka tashi ka fara kawai, watakil along the way sai wani ya ganka har ya taimaka maka. Ko a hakan ma ba shi yayi maka hanya ba, dama already ya same ka da kokarin ka kuma kana kan nema.
Ina mamakin wasu yan uwana matasa, mutum yana so yayi kudi kuma yayi ilimi, amma zai shafe 12 hours online yana hira da yam mata yana kallon comedy a kullum. Kana so kayi arziki kana so ka daukaka amma ka kira wancan a waya kayi hirar soyayya, ka gama kaje wajen wancan, ka kare ka kira wancan video call.
Kuma daga karshe kazo kana zargin wane yaki ya taimaka maka kayi gaba.
Kana so kayi kudi kayi ilimi kuma ka samu daukaka amma zaka shafe Awanni 10 kana bacci da daddare, tun daga 10pm har 8am, sannan zaka yi baccin rana na Awa uku, zaka yi hira da yam mata, zaka je filin ball ko kallon ball.
Zaka fita kofar gida cikin unguwar majalisa domin yin hira. Haba Malam a 21 century kana bata lokacin ka haka? Sai dai kaji labarin daukaka gaskiya tsakani da Allah.
Kana son daukaka amma tun a yanzu kana son saka sabbin kaya masu tsada, tun a yanzu kana son manyan wayoyi, manyan kudade kana kashewa. Gaskiya idan ka bayar da muhimmanci ma wadannan abubuwan babu inda zaka je a rayuwa.
Matukan baka da time management da time utilisation zaka dade baka fahimci abinda kake son yi a rayuwa ba. Dole ka hakura ka san cewa akwai shekarun da zaka yisu cikin hakuri da dauriya da kai zuciya nesa akan kayan more rayuwa. Wadannan shekarun ka sadaukar dasu ne domin ka samu ginuwar da har abada ba zaka dawo baya ba, in sha Allah.