11/05/2025
MINISTAN TSARO YA BAYYANA GOYON BAYANSA KAN TARON DA MAJALISSAR DATTAWA ZA TA GUDANAR DANGANE DA MATSALAR TSARON ƘASA
Mai girma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, ya bayyana goyon bayansa kan babban taron ƙoli da majalissar dattawa ta 10 za ta gudanar domin tattauna wa kan sha’anin tsaron ƙasa, a cewarsa taron ya zo a daidai lokacin da ya dace domin magance matsalolin tsaron da ƙasa ta ke ciki.
Da yake magana a wajen taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaban ƙasa Tinubu ga manema labarai, minista ya nuna cewa taron zai zama tamkar wani fage na tattaunawa da samar da tunane-tunane da dabarun da za a bi a inganta tsaro a ƙasar.
Da yake amsa tambayar wakilin Jaridar Punch a ma’aikatar tsaro, Minista Badaru cewa ya yi "idan ka gudanar da taro, al’umma za su tofa albarkacin bakinsu, za a tattara tunani daban-daban, sannan za a tace a ɗauki na ɗauka a tsara yadda za a aiwatar". Wannan shi ne yadda za a samu sauyi.
Ya kuma yaba wa ƙoƙarin majalissar na haɗa masu ruwa da tsaki, inda ya bayyana hakan a matsayin abin yabo kana kuma wani yunƙuri na samar da tsarin aiki da samar da kykkyawan sakamako. "Majalissar ƙasa ta shirya haɗa al’umma waje ɗaya domin tattauna matsalar tsaro. A lokuta daban-daban na jinjinawa tsofin ministocin tsaro da shugabannin rundunonin tsaro kan yadda s**a fahimci ƙalubalen tsaro a jiya da yau da kuma yadda za mu inganta. Na tabbata shugabannin rundunonin tsaro suna kan wannan hanya". Ya ce.
Ya kuma ƙara da nuna muhimmancin taron na majalissar dattawa tare bayyana shi a matsayin wani mataki na samun ci gaba mai ɗorewa, ba wai a tattauna kawai a tashi ba.