05/09/2025
TABARBAREWAR HARKOKIN SUFURI A BABBAR HANYAR DAKATSALLE ZUWA BEBEJI
Daga :
Comrd Idris Rabi'u DutsenGarma
Muna Kira gare ku jagorori da shuwagabannin karamar hukumar Bebeji,tare da gwamnatin jihar Kano karkashin ma'aikatar ayyuka da raya karkara ta jihar da ku kawo wa wannan hanya dauki domin tana cikin mummuna Yanayi tare da fargaba sakamakon ci gaba da lalacewa da ta ke yi a kowanne lokaci.
Hanyar ta kunshi mazabu biyar Kamar haka mazabar WAK,TARIWA,BAGUDA,DAMAU da Kuma BEBEJI.
Akwai
Sannan akwai manya garuruwa da al'ummah Ke rayuwa a cikin su da s**a hadar da Dakatsalle,H/Kurmi, DutsenGarma,Yandatsa,Baguda,Damau,Kira,Bebeji da dai sauran mahimmann garuruwa da suke bayar da gagarumar gudun mawar wajen Inganta tattalin Arzikin Karamar hukumar Bebeji.
Al'ummar wadannan yankuna Suna Shan wahala matuka a duk lokacin damuna sakamakon laka,santsi,tabo,kwantawar ruwa a tsakiyar hanya da sauran su,Hakazalika lokacin rani ma Akwai matsalar kura,turbaya ,kwazazzabai da sauran su.
Sakamakon haka bata gari Suna amfani da wannan damar wajen kwacen babura tare da dauwamar da barazana da tsoro da shiga halin rashin tabbas ga Al'ummomin wadannan yankuna.
Wannan hanya ta Zama kashin Bayan tattalin Arzikin wadannan yankuna,ta hanyar yin amfani da ita wajen fitar da kayan gona zuwa kasuwanni tare da shigo da ababen bukata na yau da kullum,rashinn ta Babbar barazana ce ga tattalin Arzikin yankin tare da dauwamar da su cikin rashin sannin dadin demokaraddiyya.
A karshe Muna addu'ar Muna Addu'ar Allah ya sa koken mu ya kai inda ya kamata
Comrd.IDRIS RABIU DUTSENGARMA
FRI.05/09/2025.