04/02/2026
KA SAN DALILIN DA YASA MAZA SUKE SAURIN MUTUWA KO SUKE SAURIN TSUFA FIYE DA MATA?
Ba shan taba bane, ba kuma rashin motsa jiki bane kawai.
Babban dalilin shine BINNE DAMUWA.
Namiji halitta ce da aka koya masa tun yana yaro cewa: "Namiji ba ya kuka", "Namiji ba ya nuna rauni."
Saboda haka, Namiji yana hadiye abubuwa masu guba a ransa kullum:
1. Hadiye Wulakanci:
Yana hadiye wulakancin maigidan haya, da wulakancin maigidan aiki, da wulakancin masu bashi... don kawai ya kare mutuncin iyalinsa, kar su kwana da yunwa.
2. Hadiye Tsoro:
Yana tsoron gobe. Yana tsoron "Babu". Amma dole ya yi murmushi a gaban matarsa da 'ya'yansa ya ce: "Kada ku damu, akwai Allah." Alhali shi kansa a ciki, yana rawar jiki.
3. Hadiye Ciwo:
Jikinsa yana ciwo, kansa yana ciwo. Amma ba zai je asibiti ba. Zai sayi Panadol na ₦50 ya sha, ya ci gaba da aiki. Saboda a lissafinsa, ₦5,000 na katin asibiti zai iya sayen shinkafar kwana biyu a gida.
Wata rana, sai kawai ka ji an ce: "Wane ya yanke jiki ya fadi."
Ko ka ga yana da shekara 35 amma ya yi furfura k**ar dan shekara 50.
Zuciyar ta gaji da daukar nauyin da aka jibge mata ba tare da hutu ba.
Dan uwa, Yi Kuka idan ya k**a. Nemi aboki na gari ka gaya masa damuwarka.
Ba karfe bane kai, Mutum ne mai jini da tsoka.
Kada ka kashe kanka saboda burge duniya.
Idan ka mutu yau, matarka wani za ta aura, 'ya'yanka wani zai rike su (ko su wulakanta).
Ka rangwanta wa kanka.
SAKO GA MATA:
Idan kuka ga Mazanku sun yi shiru, sun yi zurfi a tunani...
Kada ku ce "Me na maka?" ko ku kawo lissafin kudi.
A'a, ku kawo masa ruwa mai sanyi, ku tausa kafadarsa, ku ce: "Sannu da kokari Baban wane, Allah Ya yi maka albarka.
Wannan kalmar kadai tana rage "Blood Pressure" fiye da magani.
Ya Allah, duk Namijin da yake hadiye bakin ciki da wahala don ya ciyar da iyalinsa na Halal...
Ya Allah Ka sanyaya zuciyarsa.
Ya Allah kar Ka bari ciwon zuciya ko hawan jini ya kashe shi.
Ka ba shi tsawon rai mai albarka ya ci moriyar guminsa.
Fasi Sharubutu Koki ✍️