18/08/2025
Masu Garkuwa da Mutane Sun Yi Hatsari Bayan Karɓar Kuɗin Fansa a Nasarawa
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargi da masu garkuwa da mutane sun yi hatsari da motarsu kirar Peugeot 406 dauke da bindigogi, a daidai garin Angwan Mayo da ke kusa da Karamar Hukumar Kokona, jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne a safiyar yau, lokacin da ake zargin sun karɓi kuɗin fansa daga hannun waɗanda s**a yi garkuwa da ’yan uwansu.
Sai dai abin mamaki, bayan hatsarin, ’yan ta’addan sun tsere, amma sun bar kuɗin da s**a karɓa da kuma bindigogin da suke ɗauke da su a cikin motar.
Farfesa Akyala Ishaku, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yaba da gaggawar da jami’an tsaro s**a nuna. A cewarsa, sojoji da ’yan sanda sun isa wurin cikin hanzari tare da ɗaukar matakan da s**a dace.
~ Funtua Post News