21/09/2025
Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana ranar 8 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar ƙarshe ga Jihohi, Kwamitoci ko Ma’aikatar Kula da Walwalar Alhazai, da kuma kamfanonin da aka ba lasisi, su kai kuɗaɗen aikin Hajji na 2026.
A wata sanarwa da Mataimakiyar Darakta ta Sashen Bayani da Hulda da Jama’a na NAHCON, Hajiya Fatima Usara, ta fitar a ranar Lahadi, hukumar ta ce an sanya wannan wa’adi ne bisa tsarin kalandar aiki da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar.
Usara ta bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun ayyana tsakanin 6 zuwa 23 ga watan Satumba, 2025, a matsayin lokacin ƙulla kwangila da biyan kuɗi na sansanoni, yayin da aka sa 23–24 ga watan Satumba, 2025 domin hidimomi masu muhimmanci irin su sufuri da masauki.
Sanarwar ta ce Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, tare da kwamishinoni da Sakataren hukumar, Dr. Mustapha M. Ali, za su tafi Saudiyya a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025, domin kammala yarjejeniyar hidima da hukumomin da abin ya shafa.
Mai magana da yawun hukumar ta kara da cewa Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ta sa ranar 12 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin rana ta ƙarshe ta yin rajista da tura bayanan mahajjata.
Dan'uwa Rano TV
21/09/2025