29/07/2026
🚨 REMI TINUBU: "BAI KAMATA WANI ƊAN NAJERIYA YA KWANA DA YUNWA BA"
Uwargidan Shugaban Ƙasa, , ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Ta bayyana hakan yayin rabon kayan abinci ga marasa galihu a Akure, Jihar Ondo, inda matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, , ta wakilce ta.
A cewarta, gwamnatin za ta ci gaba da faɗaɗa shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da kafa bankunan abinci na al'umma domin tallafa wa marasa ƙarfi da kuma inganta lafiyar yara.
Ta ce:
«"Babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kwana da yunwa. Wannan shi ne manufarmu kuma wani ɓangare ne na hangen nesa na shirin Renewed Hope Initiative."»
💬 A ganinku, shin irin waɗannan shirye-shiryen tallafin abinci za su taimaka wajen rage yunwa a Najeriya, ko akwai wasu matakan da s**a fi dacewa?