
21/09/2025
Canada Ta Bayyana Goyon Baya Ga Falasɗinu
Firaministan Canada, Mark Carney, ya sanar a hukumance cewa daga yau (Lahadi) “Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu.”
A cikin wata sanarwa da ya bayyana a shafinsa na X, Mista Carney ya ce:
“Mun amince da ƙasar Falasɗinu, kuma muna miƙa gudummawarmu wajen ganin an samu zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra’ila.”