SirrinsU MEDIA

SirrinsU MEDIA SirrinsU MEDIA Nigeria Limited Kamfanin Yada Labarai Masu Jaridar SARAUNIYA Online. Wallafa Litattaf

Media, News, Films, Documentary, Publishing, Books, Magazines & Consulting

06/08/2019

Ta Bayar Da Kodarta Ga Tsohon Mijinta, Shekaru Biyar Bayan Saki

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Wata mata mai suna Kelly Hope ta bai wa tsohon mijinta kodarta domin ta ceci rayuwarsa da ke cikin hadari.

Rahotanni sun bayyana cewa Dan Pyatt, tsohon mijin Kelly Hope, ya gamu da matsalar ciwon koda wanda likitoci s**a tabbatar masa da cewa dole a yi masa dashen sabuwar koda, matukar yana son ya ci gaba da rayuwa.

Dan Pyatt ya shafe watanni 12 yana neman koda amma bai samu ba. Hakan ya sa Kelly Hope, matarsa da s**a rabu shekaru biyar baya, kuma uwar 'ya'yansa, ta yanke shawarar taimaka masa da kodarta guda daya.

Kelly Hope ta bayyana cewa ba za ta bari uban 'ya'yanta ya mutu ba duk kuwa da ba sa tare.

MU SHA DARIYA....MATARSA TA K**A SHI YA JE LALATA DA KAWARTAAlmajiri! Almajiri!!Matar ta leko tana fada alamun tana nema...
03/08/2019

MU SHA DARIYA....

MATARSA TA K**A SHI YA JE LALATA DA KAWARTA

Almajiri! Almajiri!!

Matar ta leko tana fada alamun tana neman yaro karami, wani zabgegen gardi sanye da zabgegen tabarau ya zo kansa da askin yan bana-bakwai rike da sanda a zuwan shi makaho ne kuma almajiri.

"Ga Ni" Ya fada

Cikin mamaki ta kalle shi sama da kasa

"Almajiri nake nema".

"Ai nima Almajirin ne".

"Ya ina neman almajiri za ka zo godai-godai da kai ka ce kai Almajiri ne?"

"To a taimaka min da sadaka"
"Ban yi niyya ba"
"Ikon Allah wai na kwance ya fadi" Inji mai cewa shi Almajiri ne.

"To dan Munafuka uban me ya kawo ka nan?" Wani mai k**a da tsoho ya fada a yayin da ya zo wajen a fusace.

"To jaba ta sako baki" Almajiri ya fada almun bai ji dadin zuwan tsoho ba.

"Za ka bar nan ko sai na yi kasa-kasa da kai!" Ya yi wa Almajiri barazana.

"Ni ba bakon zafi ba ne ko a tsakanin miji da mata sai na kwana". Ya fada yayin da ya bangaje tsoho ya wuce.

"Ke ki ji dan shegiya wai ko a tsakanin Miji da mata sai kwana" Ya ke fadawa matar.

"Ni fa ba ruwana da shi Almajiri na fito ina nema" Ta fada masa tana Ja baya da shi saboda matsawa kusa da ita da yake yi.

"Idan ma ana neman wanda zai kwana a tsakanin Miji da Mata ba za a nemi irin Mu masu ido ba sai Makaho? Me Makaho zai iya yi? Gola zai k**a?"

"Ka ga Malam ka tafi kafin Mijina ya dawo?"

"Au baya nan ne?" Cikin jin dadi ya fada

"Eh baya nan amma ya kusa dawowa".

Domin Kallon Yadda Aka Yi Abin Kunya Danna Nan A Sha Kallo:

https://youtu.be/AC-K4yYSeFM




MATARSA TA K**A SHI YA JE LALATA DA KAWARTA (Budurwar Zuciya Episode 4)

https://youtu.be/XHS52nSG5cY
27/06/2019

https://youtu.be/XHS52nSG5cY

SABON FIM 2019 Na Barkwanci Da Nishadi Akan Wani Gogaggen Kwarto Da Ya Addabi Matan Aure Da 'Yan Mata. ...

Address

C 21 Safiya House Off Umar Bn Khattab Mosque Along Zaria Road
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SirrinsU MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to SirrinsU MEDIA:

Share