10/07/2025
Ga magoya bayan Madrid, ku tsaya ku karanta: Matsalolin da Real Madrid ke fuskanta da kuma matakan da zasu ɗauka bayan tsige su daga gasar Club World Cup.
• Ƙungiyar ta na fama da matsaloli na haɗin kai, kamar yadda aka gani a wasan su da PSG. Daga ɓangaren Madrid an samu rashin fahimtar juna tsakanin ƴan wasan ƙungiyar, musamman bayan da aka fara zura musu ƙwallaye.
• Alamun damuwa da rashin jituwa sun bayyana ƙarara a tsakanin ƴan wasan ƙungiyar, sannan kuma babu daidaito a cikin tawagar, musamman bayan kuskuren Asensio wanda ya haifar da zura musu ƙwallo ta farko a raga.
▪️ Shugabannin ƙungiyar za su gudanar da zama da ƴan wasa domin jin ra’ayoyinsu da fahimtar manufofin su, tare da jaddada cewa haɗin kai shi ne ginshiƙi na farko a cikin tawagar indai suna son a samu nasara. Idan kuma ba haka ba, za a ɗauki matakai kafin a rufe kasuwar saye da musayen ƴan wasanni ta bana a watan Satumba.
▪️ Ƙungiyar na nuna damuwa sosai a kan Vinícius Jr saboda raguwar ƙoƙarin sa da kuma yadda bajintar sa ta ragu sosai ba kamar yadda yake yi a baya ba. Kungiyar zata nemi sanin ainihin gaskiya daga gare shi kan makomarsa.
● Rodrygo Goes zai iya barin Real Madrid, domin a yanzu haka ya fara neman ƙungiyar da zai koma bayan shafe wasanni uku a jere ba tare da ya buga wasa ba.
● Kylian Mbappé ma bai yi ƙoƙari ba kamar yadda ake tsammani, musamman a ɓangaren dawowa a tare. Wannan yana ƙara ɗaga hankalin Xabi Alonso, wanda ke jaddada mahimmancin aiki tare da kuma tare ta kowanne ɓangare.
Babbar matsalar ba wai rashin iya wasa bane tsakanin ƴan wasan ba kaɗai, harma da rashin haɗin kai da fahimtar juna musamman a lokutan da ake fuskantar ƙalubale.
Xabi Alonso tare da taimakon mahukuntan ƙungiyar ya gano wannan matsalar, kuma ya ƙudiri aniyar magance ta. Ya bayyana cewa matsalar ta dangana ne da halin da ake ciki yanzu, ba wai a kan mutum ɗaya kawai ba, amma ga kowa da kowa. Kuma wannan fahimtar ta sa ta yi daidai da abun da tsohon kocin ƙungiyar Carlo Ancelotti ya taɓa faɗa.
• Fagen Wasanni