DMS HAUSA 24

DMS HAUSA 24 D M S HAUSA 24 Jarida ce Mai yada
shirye-shirye a kafar Facebook da YouTube. a halin yanzu cikin Harshen HAUSA, daga Kano.

Jarida ce da ta kudiri aniyar kawo mu ku sahihan Labarai daga ko ina cikin duniya.

Saƙon Gayyata Da Taya Murnar Maukibi Na 76 Ga Ɗaukacin Muhammadawa A Ƙarkashin Jagorancin Maulana Halifah Sheikh Qaribul...
03/10/2026

Saƙon Gayyata Da Taya Murnar Maukibi Na 76 Ga Ɗaukacin Muhammadawa A Ƙarkashin Jagorancin Maulana Halifah Sheikh Qaribullah Sheikh Nasir Kabara.
Daga: Alhaji Abdullahi Yaro Yahaya (CHAIRMAN OSTRO TRADING COMPANY NIG LTD).

Allah Yasa Ayi Maukibi Lafiya A Gama lafiya.

Su Waye Ke Juya Akalar Hakar Ma'adanai A Niger, Yayin Da Mutane 37 S**a Mutu Hannun Jami'an Tsaro?An cafke Matas 37 Yayi...
19/09/2026

Su Waye Ke Juya Akalar Hakar Ma'adanai A Niger, Yayin Da Mutane 37 S**a Mutu Hannun Jami'an Tsaro?

An cafke Matas 37 Yayin wani samamen jami'an Tsaro a Wushishi/Lukoto bisa zargin su da Hakar Ma'adanai ba bisa ka'ida ba, Daga bisani aka ce sun mutu a hannun hukumar Tsaron al'umma ta civil Defence.

Bayan faruwar abin, Gwamnatin jiha ta Bada Umarnin bin bahasi, Yan sanda Zasu gudanar da bincike, Sauran Hukumomin Tsaro suma sun kaddamar da bincike. An dakatar da kwamandan Civil Defence na jihar, wannan kawai Wasu matakai ne, ba a Kai ga gano gaskiyar al'amarin ba

Ba a tuhumi Wadannan matasa da Ayyukan Ta'addaci ba, abin da ya bayyana shi ne suna kokarin Neman na Kan su ne Domin iyalan su, su Kuma tallafawa iyayen su, amma Gwamnatin jihar ta gaza samar musu da ingantaccen Tsarin sana'ar.

Tambayar da ke fitowa Daga bakin duk wani Mai hankali ita ce, waye ya Bada Umarnin k**a su ? Har zuwa lokacin da sak**akon bincike zai bayyana, za a Ci Gaba da danganta lamarin da yuwuwar barkewar wata cuta, ko guba ko cinkoso ko suma, dole ne a yi bincike ba wai Daukar matakai Kan zato ba.

Hatta Wurin Hakar Ma'adanan ba zai ware shi Wajen bincike ba. Akwai zarge-zargen cewar Wasu Masu Fada aji a jihar, sun dauki lokaci suna son kwace wannan Wurin Hakar Ma'adanai, akwai bukatar bincika wannan Ikirarin.

Ana Yan gulmace-gulmace da tsaigungumi a garin Minna, cewar k**ar abinda ake zargin ya faru a Zamfara, Gwamnan jihar Niger nada sha'awar mallakar Wurin, Kuma akwai ana cewar akwai shiri na sauyawa al'ummar Wushishi gari da sunan tsaftace muhalli.

Har ila yau, an rawaito cewar ya je wuraren Hakar Ma'adanan da yawa, Kuma ma ana zargin cewar ana bashi wani kaso duk mako Daga zinare, abinda aka ce ya Sanya shi dukan kirji da alfahari a wani lokaci a Baya, Wadannan manyan dalilai ne. Ba wai sheda bace, Wadannan batutuwan sune a takaice ake tattaunawa .

Wadannan batutuwan sun Isa a bukaci amsar su, waye yake Neman a bashi izinin Hakar Ma'adanai? Waye ya tura bukatar lasisi ko Kuma a Sayar Masa da Wurin Hakar Ma'adanan? Shin akwai Wadanda S**a yi yunkurin karbe iko da Wurin a Baya? Ko akwai wata bukatar Dake Kasa Kafin cafke Wadannan matasa? Shin ko akwai shi ne shiri na tsaftace muhalli a Wushishi da batun sauya mutanen sa gari Kafin samamen jami'an Tsaro?
A barin kundin bayanai su fayyace, ya k**ata a gayyaci Hukumar da'ar ma'aikata da kotun ta su kallo batun bayyana Kadarorin da kundin lasisi da bayanan kwamitin karta kwana da Kuma bayanan kasuwar hada-hadar gwala- gwalai.

Rade-radin da ake a Minna shi ne Hakar Ma'adanai a jihar Niger ba fagen marasa galihu ba ne. Bada lasisi hakkin Gwamnatin Tarayya ne, tafiyar da wuraren hakar Kuma na hannu gwamnatocin jihohi. Daraktan lura da albarkatun Kasa Ademola Banjo Gwamnan ne ya nada shi a shekara ta 2024, bincike ya nuna cewar ma'aikacin banki ne kuma Dan kasuwa. Baya Cikin aikin sa Bada hayar wuraren hakar Ma'adanai Babu batun rajistar Masu harkar, ga Kuma kwamitin karta kwana Kan Hakar Ma'adanai ta haramtaciyyar hanya.akwai tambayoyi da yawa irin Wadannan.
Babu Wanda zai baka wannan bayani, ko akwai Wanda zai Fada Maka Wanda ya San adadin gwal din Dake fita Daga Niger ta hannun dilallai Masu lasisi da Kuma Sauran hanyoyi.

Babu Wanda zai fake karkashin Rashin Tsarin hukuma a fannin Hakar Ma'adanai ya kaucewa doka, duk abinda aka Tabbatar k**ata ya yi a Kai kotu, Bai k**ata su mutu ba saboda a kulle su, Kuma Neman abinci Cikin Ramin Ma'adanai ba shelar Yaki bane.

Ya k**ata a fitar da sahihin Tsarin bincike a bainar jama'a, a fadi jami'in da ya Bada Umarnin Kamo Matasan da sashin da ya aikwatar da yanayjn da aka saka su da Kuma bayanin waye ya amfana ko zai amfana idan aka share Wurin.

Jihar Niger ta cancanci Wadannan bayanai da iyalai 37 Dana 'yan Najeriya Gaba daya

Daga Ibrahim Maigida Shehu, Maitumbi, Minna.

Sponsored Who Runs Niger’s Mines While 37 Die in Custody?Thirty-seven young people arrested in an operation against susp...
19/09/2026

Sponsored

Who Runs Niger’s Mines While 37 Die in Custody?

Thirty-seven young people arrested in an operation against suspected illegal mining at M.I. Wushishi/Lukoto later died in NSCDC custody. The state has ordered inquiries and autopsies, the police is to do an investigation, the other security agencies also launched investigations. The Niger State NSCDC Commandant has been suspended. That is procedure. It is not yet truth.

These were not charged as bandits or terrorists. Many appear to have been seeking a living from artisanal work to feed their families, help their parents and get themselves daily earnings, but the state has failed to regularise.

The question on the lips of every right-thinking citizen is who ordered the arrest? Until forensic findings are published, breakout of disease, poisoning, overcrowding and suffocation remain allegations that must be tested, not assumed.

The site itself cannot be left outside the inquiry. There are allegations that some powerful individuals linked and connected in the state have, for some time, sought to take over or gain control of this particular ground because of its mineral potential though those claims remain to be proven.

In Minna those claims now have a sharper name attached to them. Side talk in the city is that the State Governor has a personal interest just as it happened in Zamfara in taking over the mining location, and that a proposal is in the offing to relocate M.I. Wushishi residents under the excuse of environmental cleanup.

It is also said, as a matter of local certainty rather than published record, that he is in many gold sites and that a weekly gold return is made to him a boast he is alleged to have made, at one time, to people around him. Those are grave assertions. They are not proof. They are precisely the sort of talk that an inquiry which stops at cells and commandants will leave hanging over the thirty-seven dead.

They are serious enough to require answers on the record: who is interested in the mining rights; who has applied for licences or concessions of that same location; whether earlier attempts or proposals were made to takeover the site; whether any application or commercial interest was pending before the arrests; whether any relocation or “cleanup” plan for M.I. Wushishi existed before the raid; and whether any such interest is connected to the operation. Let the documents speak. Let us also invite the Code of Conduct Bureua and its Tribunal to look into asset declarations, licence files, task-force minutes and gold-market inventories speak.

Gossip in Minna is not a substitute for paper, mining in Niger State is not an orphan file. Licences are federal. Administration on the ground is state. The Director-General of Mineral Resources is by name Ademola Banjo, appointed in March 2024 by the Governor. From the fact check it is confirmed he was a banker and businessman; he was formerly a staff of First City Monument Bank. His brief is not to grant mining leases. It is to profile operators, and sit on enforcement structures, including the 2024 illegal-mining task force. A lot of questions here to ask.
That architecture makes the silence on output indefensible. Who holds the statistics on gold leaving Niger State by licensed concession and by informal routes?

If influential interests wanted this site including, if the talk in Minna is ever to be retired, interests at the very top of the state, the public is entitled to see the paper trail, not a body count.

No one should hide behind informal mining to escape the law; proven offences must go to court. Being locked up is not a licence to die, and earning a living from the pits is not the same as waging war.

The inquiry should set out, in public, the government’s decision at it State Security Council meeting, the officer who authorised the raid, the unit that executed it, the conditions of detention, and the official record of what the ground has yielded including who benefits when the ground is cleared.

That accounting is due to the thirty-seven families. It is due to Niger State as it due to citizens of Nigeria as well.

Ibrahim Maigida Shehu, Esq
Writing from Maitumbi Minna.

Sponsored.A yunkurin tallafawa kokarin Gwamna Abba Kabir Yusuf a fannin ilimi, jami'an Gwamnatin Kano uku da S**a fito D...
18/09/2026

Sponsored.

A yunkurin tallafawa kokarin Gwamna Abba Kabir Yusuf a fannin ilimi, jami'an Gwamnatin Kano uku da S**a fito Daga yankin Dambatta da S**a hada da Kwamishinan Kudi Dr Ismail Danmaraya da na Ayyuka Injiniya Marwan Ahmad Shugaban sashin lura da tasirifi da kuɗaɗen Ayyuka Aliyu Lawal Majidadi sun Jagoranci raba jakankunan makaranta da muhumman kayan karatu ga daliban firamare 1,000 a yankin.

An raba kayayyakin ne ga rukunin dalibai uku da S**a kunshi marayu da yayan marasa karfi sai yaran da S**a nuna kwazon karatu da Kuma yara Masu da'a da zuwa makaranta Kan lokaci da basa fashin zuwa.

An sace wasu malamai shida da s**a je taron addu’ar nasarar Tinubu da APC a ZamfaraRundunar ‘yansandan Nijeriya reshen J...
13/09/2026

An sace wasu malamai shida da s**a je taron addu’ar nasarar Tinubu da APC a Zamfara

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.

Rahotanni dai sun ce malaman suna Kan hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.

‘Yansandan sun ce tuni s**a baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace.

’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan mak**ai, s**a yi wa wata mota da ke ɗauke da waɗanda lamarin ya rutsa da su kwanton ɓauna.

A cewar ’yan sandan, mutanen shida, waɗanda dukkaninsu limaman Musulunci ne, suna tafiya ne zuwa Talata Mafara lokacin da maharan s**a tare su tare da yin garkuwa da su

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Bamanga Tukur Ya Rasu.Allah ya yi wa fitaccen attajirin nan na Nijeriya kuma tsoho...
12/09/2026

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Bamanga Tukur Ya Rasu.

Allah ya yi wa fitaccen attajirin nan na Nijeriya kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP Alhaji Bamanga Tukur rasuwa yana da shekaru 90.

Iyalen marigayin sun ce ya rasu ne ranar Asabar a gidansa da ke Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sun Kuma shedawa majiyar mu cewar ana sa ran za a yi jana'izarsa a ranar Asabar din nan a Fadar Lamidon Adamawa, da ke Jihar Adamawa.

Marigayin ɗan kasuwar Kuma Dan siyasa, ya rasu ya bar 'ya'ya 17.

Marigayin ya yi gwmanan tsohuwar Jihar Gongola (Adamawa da Taraba a yanzu) a zamanin Jamhuriyya ta Biyu.

Bamanga Tukur ya yi ministan masana'antu a lokacin gwamnatin Sani Abacha, sannan ya taɓa neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya.

Madogara TRT Africa

Gwarzo ya bukaci daukin gaggawa kan hare-haren yan bindiga a KanoDan takarar gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NDC, Comrad...
01/09/2026

Gwarzo ya bukaci daukin gaggawa kan hare-haren yan bindiga a Kano

Dan takarar gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi Allah-wadai da hare-haren yan bindiga a wasu sassan jihar, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin kare rayukan al’umma.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar ranar Talata, Gwarzo ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da s**a shafi Chiromawa a Karamar Hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji da wasu al’ummomin da ke kusa da Gwarzo.

Ya jajanta wa iyalan wadanda s**a rasa rayukansu tare da addu'a ga waɗanda s**a jikkata, s**a rasa matsugunansu ko kuma s**a fuskanci wasu matsaloli sak**akon hare-haren.

Gwarzo ya ce matsalar tsaro na barazana ga rayuka, sana’o’i da tattalin arzikin al’umma, yana mai cewa bai k**ata yan jihar su bar gidajensu, gonakinsu da wuraren kasuwancinsu saboda ayyukan masu aikata laifuka ba.

Ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri, sanya ido da gudanar da samamen da aka tsara kan maboyar yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Dan takarar ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gano tare da rufe duk wani giɓi na tsaro da ka iya bai wa yan bindiga da masu aikata laifuka damar kafa sansanoni a yankunan karkara.

Ya ce kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban nauyin gwamnati, don haka ya k**ata a dauke shi a matsayin abin da ke bukatar daukin gaggawa.

Gwarzo ya kuma yaba da kokarin jami’an tsaro wajen yaki da masu aikata laifuka, tare da kira gare su da su kara amfani da bayanan sirri da inganta tsarin kai dauki cikin gaggawa a yankunan da ake ganin suna cikin hadari.

Ya shawarci mazauna yankunan da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai bayanan da s**a dace ga hukumomin tsaro, domin taimakawa wajen dakile hare-hare, ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kuma k**a wadanda ke da hannu a aikata laifukan.

Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi addu’ar Allah Ya ji kan wadanda aka kashe, tare da fatan samun nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce babu yadda za a samu ci gaban tattalin arziki, bunkasar noma da ingantuwar rayuwar al’umma ba tare da samar da zaman lafiya da tsaro ba.

Tun 2024 Tinubu Ya Bude Iyakoki- Fadar Shugaban Kasa Ga AtikuFadar shugaban Najeriya ta maida martani ga dan takarar shu...
29/08/2026

Tun 2024 Tinubu Ya Bude Iyakoki- Fadar Shugaban Kasa Ga Atiku

Fadar shugaban Najeriya ta maida martani ga dan takarar shugaban Kasa na Jam'iyyar ADC Atiku' Abubakar Kan kalaman sa na sake buɗe iyakoki idan aka zaɓeshi a shekara mai zuwa.

Wata sanarwar da hadimin shugaba Tinubu ɓangaren yaɗa labarai Sunday Dare ya fitar, ta ce tun a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2024, gwamnatin Tarayya ta buɗe iyakokin ƙasa na ƙasar.

Sunday Dare ya ce suna mamakin waɗanne iyakoki ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar ke shirin buɗewa, ganin dama can a buɗe suke.

Ya kuma ce a ranar 14 ga watan Faburairun wannan shekarar, shugaba Tinubu ya bada umarnin buɗe iyakar ƙasar ta garin Kamba da ke jihar Kebbi.

A baya-bayan nan dai adawar siyasa na kara zafafa tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar da kuma fadar shugaban ƙasar.

Domin a baya-bayan nan sai da fadar ta yi watsi da alƙawarin Atiku na maido da tallafin man fetur da gwamnatin ta cire, yayinda a jiya Juma’a ya sake shan alwashin buɗe iyakokin ƙasar da ke ƙulle da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro cikin shekara guda idan har ya lashe zaɓen da ke tafe

Yau 29 ga watan Augusta hukumar zabe ta INEC za ta Saki jerin sunayen yan takarar gwamna da mataimakan su.Wane ne fata K...
29/08/2026

Yau 29 ga watan Augusta hukumar zabe ta INEC za ta Saki jerin sunayen yan takarar gwamna da mataimakan su.

Wane ne fata Ku ke da shi game da zaben gwamnoni a jihohin Ku???

Dan takarar shugaban Kasa na Jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ya yi Alkawarin Bude iyakokin Najeriya na kan Kasa idan aka za...
28/08/2026

Dan takarar shugaban Kasa na Jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ya yi Alkawarin Bude iyakokin Najeriya na kan Kasa idan aka zabe shi shugaban Kasa a zaben watan janairun badi .

Atiku Abubakar ya yi Alkawarin ne Yayin jawabi ga magoya bayan sa Cikin wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan dada zumunya Wanda jigo a Jam'iyyar ta ADC Dele Momodu ya Saki yau juma'a.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya yace rufe iyakokin ya haifar da babbar illa ga kasuwancin Kasa da Kasa tare da haifar da Rashin aikin yi tsakanin matasa.

Ya ce jihohin Arewa ne ke Kan iyakokin Kamaru da Chadi da Nijar da Kuma Benin.

“Ka kulle Wadannan iyakokin, wannan ta Sanya dukkan matasa Dake kasuwanci a tsakanin Wadannan kasashen marasa aikin yi. Kowa ya Sani kasuwanci tsakanin Kasa kasa halastaccen ciniki ne.

Atiku yace matasa da yawa Wadanda a Baya ke juya miliyoyin Kudi an tilasta musu barin kasuwanci sak**akon rufe boda.

Ya kara da Cewa Matasan Dake kasuwanci da Naira miliyan 10 zuwa 20 tare da samar da Ayyukan yi ga Wasu Matasan maza da Mata yanzu duk sun talauce saboda wannan mataki.

Inda yace wannan nada alaka da Rashin Tsaro, inda yace tabbas zai sake Bude bodajin Kasar Nan.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DMS HAUSA 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share