13/05/2026
Majalisar Dinkin Duniya ta nemi gudanar da bincike kan kisan fararen hula a Najeriya
Shugaban hukumar kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Volker Turk, ya buƙaci a gudanar da bincike na musamman game da kisan fararen hular da aka samu a Arewacin Najeriya, bayan hare-haren da dakarun ƙasar da na Chadi s**a kai kan ƴan ta’adda.
Rahotanni sun nuna cewar masinta da dama ne s**a rasa rayukansu a harin da sojojin Chadi sun kai a yankin Tafkin Chadi, wanɗanda mahukunta N'Djamena s**a zarga da taimakawa ƴan ta’addan Boko Haram.
A cikin sanarwar da Volker Turk ya fitar, ya kuma ce akwai buƙatar a gudanar da bincike na musamman, kan yadda aka kashe fararen hula a harin da jirgin saman sojin Najeriya ya kai kasuwar Tumfa da ke yankin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, wanda rahotanni s**a ce sama da mutum ɗari s**a mutu.
Kafin wannan kira na Majalisar Ɗinkin Duniya, anji dama Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adam ta Amnesty International na Allah wadai da wannan hari.
RFI HAUSA