11/06/2025
Dan Majalisar Tarayya ya Maka Wasu Matasan Mazabarsa A Gaban Kotu A Kano
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Bagwai da Shanono a Jihar Kano, Hon. Yusuf Ahmad Badau, ya maka wasu matasa a gaban kotu, wadanda ke karkashin kungiyar Bagwai/Shanono Together for Progress, bisa zargin kafa kungiya ba bisa ka’ida ba da kuma bata masa suna.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da kungiyar ta shigar da koke a kansa gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) da kuma kwamitin ladabtarwa da sauraron korafe-korafe na Majalisar Tarayya.
Kungiyar ta bayyana a cikin korafinta cewa akwai bukatar a binciki ayyukan mazabar da s**a kai kimanin Naira biliyan daya, inda s**a zargi dan majalisar da karkatar da kudade da kuma kin aiwatar da ayyukan yadda ya kamata. Ayyukan da ake magana a kansu sun hada da gyaran hanyoyi, tallafin matasa, da kuma samar da kayayyakin more rayuwa.
Sai dai yayin da AREWA UPDATE ta tuntubi lauyan dan majalisar, Barrister M. M. Sani, ya bayyana cewa sun dauki matakin gurfanar da matasan ne a kotu bisa hujjojin cewa kungiyar ba ta da rajista da kuma cewa ta ke bata sunan dan majalisar ta kafafen yada labarai da kuma gaban hukumomi.
Ya ce, “Aikin dan majalisa shi ne wakilci da kokarin samar da ayyuka ga al’ummarsa, amma ba shi ne ke aiwatar da ayyukan kai tsaye ba. Abin mamaki ne yadda s**a cakuda ayyukan da ba su da alaka da dan majalisar domin kawai su gina zargi a kansa.”
Barrister Sani ya kara da cewa matakin da kungiyar ta dauka yana da illa ga mutunci da martabar dan majalisar a idon jama’a da hukumomi, wanda hakan ya tilasta musu daukar matakin shari’a domin kare martabarsa da mutuncinsa a bainar jama’a.
Yanzu haka dai ana jiran yadda kotu za ta gudanar da shari’ar, yayin da al’umma a yankin Bagwai da Shanono ke ci gaba da sa ido kan cigaban da rikicin siyasar ya dauka.