28/02/2025
BUDDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNA ENGR. ABBA KABIR YUSIF.
Bayan Sallama da gaisuwa irin ta addinin Islama. Assalamu alaikum.
Cikin salo na girmamawa nake mika wannan 'yar gajerar rubutu zuwa ga Maigirma gwamna Alhaji Abba Kabiru Yusif dangane da aikin titin Bunkure na 5 Kilo mitas wanda ka gada a wajen gwamnatocin da s**a shude na Jagora Kwankwaso, tare da tsohon Gwamna Ganduje, tare da alkawarin gwamnatinka zata dora, Kamar yadda ka ambata a wajen Kamfen dinka na 2023.
Ya Maigirma Gwamna, Alhamdulillah. kamar yadda ka ambata zakai tabbas munga alamar hakan a aikace, Saidai Dan korafe korafen da aikin yazo dashi
Ya Maigirma Gwamna korafin mu a wannan aiki, shine;
1- Rashin ingancin aikin
2- Rashin Kayan aiki wa Dan Kwangila.
3- Rashin iya tafiyar da aikin
4- Rashin gudun aikin.
1- Rashin Ingancin Aiki: Ya Maigirma Gwamna a zahirin gaskiya duk Wanda yasan garin da ake wannan aiki, to ya sanshi da matsalar mugudanen ruwa musamman a lokacin damuna.
Sai gashi kuma wannan aiki maimakon a fada mugudanen saboda kaucewa matsalar da garin ya jima yana fama, sai muka wayi gari ana saka randar ruwa Mara inganci.
2- Rashin Kayan Aiki: Ya Maigirma Gwamna wannan kamfani da aka bawa kwangila yana da karancin kayan gudanar da wannan aiki. Domin kayan aikin da kamfanin ke amfani dasu bai wuce Mota biyu ba. Mota daya ta s**ar kaya, sai kuma daya ta zuba kaya, wannan ya kawo rashin tafiyar aikin.
3- Rashin Iya Tafiyar da Aiki: Maigirma Gwamna wannan Kamfani duk Wanda ya shiga wannan gari zai tabbatar da maganar nan, domin sun kasa tsayuwa da hankalinsu waje daya a aikin. Sun damula cikin garin, babbar hanyar dake wajen garinma sun dau hanyar damuleta.
4- Rashin Gudun Aikin: Ya Maigirma Gwamna ba zalama muke ba wajen tafiyar aikin, saidai matsala daya da muke tsoro ta zuwan damuna, saboda idan damuna ta riskemu a wannan yanayi tabbas za a tafka asararori a sakamakon rashin magudanen ruwa.
Na tabbata ruwa zaici gidaje tare da taba shagunan masu neman abinci, idan ba ayi aune bama za a iya asarar rayuka ta dalilin rushewar dakuna.
Ya Maigirma Gwamna da dai banso nace wani abu ba sakamakon yadda na samu labarin takardar wakilin Bunkure a Majalissar dokokin Kano "Hon Hafizu Sharif Gambo Gurjiya da ya aike ma dangane da wannan aiki,"
Sai kuma naga dacewar a kara yi maka tuni ko saboda bukatar mutanen wannan gari da kammaluwar wannan aiki.
Ya Maigirma Gwamna muna fatan zaka dube mu kamar yadda Allah ya dubeka a lokacin Shiri'ar Zaben 2023.
Haza Wasallam.
Aminu Ahmad Alhassan