15/07/2025
Allah Ya ji kan Buhari: Amma A Bar Gaskiya ta yi Halinta
Daga ฦan Bello
Muhammadu Buhari ya rasu โ tsohon shugaban da ya shigo da sunan wanda zai tsirantar da alโumma, amma ya bar ta cikin bakin ciki, talauci, da rashin gaskiya.
Ya sha neman mulki. Ya dauki alkawura. Ya samu amincewar talakawa. Amma abin da ya bari?
โ Matasa ba aiki.
โ ฦananan โyan sanda da sojoji suna azabtuwa.
- Cire manyan โYan Sanda daga tsarin CPS na zalunci
โ Kudin fansho ya zama arzikin wasu barayi
โ Manoma, malamai, maโaikata โ dukkansu sun zama marasa ฦarfi a garuruwansu.
โ Gwamnatinsa ta zama mafaka ga barayi da azzalumai.
Ya rasu a asibitin ฦasar waje โ abin da yawancin talakawa ba su da damar zuwa ko mafarkin samu idan ba su da lafiya.
Amma Dole Mu Fadi Gaskiya:
A alโadance kuma a addinance, muna adduโa ga matattu. Amma mu โYan Gaskiya ba za mu binne Gaskiya ba. Idan ka yi mulki ka jawo mutuwar wasu, ka jawo wahala, ka karya alkawura โ to babu wanda ya isa ya wanke ka a tarihi.
Gaskiyar da muke Gudu:
Yafiya ba gazawa bane. Amma tunanin cewa ba za mu yi kamar baโa zalunci talaka ba don mutum ya koma ga ubangiji โ hakan ne ke sa azzalumai da barayi su ci gaba da cin zarafinmu su na satar arzikinmu.
Mu roฦi gafara a matsayin Musulmi โ amma ba za mu karyata tarihi ba.
Buhari bai zama waliyi ba saboda ya rasu. Kuma ba zai tsira daga abunda yayi a tarihi ba.
โ๐ฝ Dan Bello | โYan Gaskiya