HAUSA LEADS News

HAUSA LEADS News Fidda Aya daga cikin tsakuwa, faɗar Gaskiya komai ɗacinta shi ne Jarinmu
HAUSA LEADS DOMIN KU MUKE

Muna taya ƴan uwa Muhammadawa murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta manzo S.A.W
25/08/2026

Muna taya ƴan uwa Muhammadawa murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta manzo S.A.W

Sakataren Yada Labarai  Jam’iyyar APC na Kasa, Felix Morka, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta janye jeri...
25/08/2026

Sakataren Yada Labarai Jam’iyyar APC na Kasa, Felix Morka, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta janye jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Yayin da yake zantawa da TheCable a safiyar ranar Talata, Morka ya bayyana wadannan rahotanni a matsayin jita-jita.

A cewarsa, duk wani sauyi da za a samu a jerin sunayen za a sanar da shi ta hanyar da ta dace.

Cewar Junaidu Aminu Kilishi...Ku mene ra'ayin ku
24/08/2026

Cewar Junaidu Aminu Kilishi...

Ku mene ra'ayin ku

Sakon Abdulmajid Danbilki Kwamanda
24/08/2026

Sakon Abdulmajid Danbilki Kwamanda

24/08/2026

Sakon Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ga Naja'atu

🛑 LABARI CIKIN GAGGAWAGwamnoni bakwai na Arewa, tare da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da mai ba s...
22/08/2026

🛑 LABARI CIKIN GAGGAWA

Gwamnoni bakwai na Arewa, tare da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da mai ba shugaban ƙasa shawara Ibrahim Kabir Masari, sun gudanar da taron sirri da malaman addinin Musulunci da masana daga jihohin Arewa 19 da Abuja, a birnin Dutse na Jihar Jigawa.

Taron ya samu halartar Gwamnonin Jigawa, Kano, Yobe, Sokoto, Kaduna da Katsina, inda aka tattauna batutuwan da s**a shafi tsaro, tattalin arziki, ilimi, noma da samar da ayyukan yi ga matasa.

Sai dai ba a bayyana dalilin taron a hukumance ba, kuma an bukaci ’yan jarida su fice kafin fara ganawar sirrin.

Ana kuma alakanta taron da shirye-shiryen zaben 2027, duk da cewa babu wata sanarwar hukuma da ta tabbatar da hakan.

Jigo a APC Hamza Darma ya rasu yana da shekaru 76Fitaccen dan siyasa a jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Hamza Usman Darma, y...
21/08/2026

Jigo a APC Hamza Darma ya rasu yana da shekaru 76

Fitaccen dan siyasa a jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Hamza Usman Darma, ya rasu yana da shekaru 76.

SolaceBase ta ruwaito cewa Alhaji Hamza Darma ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a ranar Juma’a.

A cewar majiyoyi daga iyalansa, za a gudanar da jana’izar sa a gidansa da ke Hororo, kusa da Jami’ar Maryam Abacha ta Najeriya (MAAUN) a yau.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata a matsayin ranar hutu Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsay...
21/08/2026

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu na kasa don yin bikin Maulidi na bana, wato tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW).

Gwamnatin Kano za ta hana zirga-zirgar manyan motoci a cikin kwaryar birni da ranaGwamnatin Jihar Kano ta sanar da shiri...
20/08/2026

Gwamnatin Kano za ta hana zirga-zirgar manyan motoci a cikin kwaryar birni da rana

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin takaita shigowar manyan motoci cikin birnin Kano daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa dare, domin rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirga.

Kwamishinan sufuri na jihar, Haruna Isa Dederi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce an kammala shirye-shiryen fara aiwatar da sabuwar dokar.

Dederi ya ce matakin ya zama dole ne sakamakon ƙaruwa da yawan jama’a a jihar da kuma kasancewar Kano babbar cibiyar kasuwanci a yankin.

Ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da wani kamfani mai zaman kansa domin zamanantar da tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa da inganta harkokin sufuri.

A cewar kwamishinan, hanyoyin shiga birnin guda shida ne za su kasance ƙarƙashin sabon tsarin. Su ne Kano-Katsina, Kano-Zariya, Kano-Danbatta, Kano-Gwarzo, Kano-Wudil da Hadejia.

Ya ce takaita shigowar manyan motocin zai taimaka wajen rage cunkoso a manyan hanyoyin shiga birnin tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci.

Shi ma Manajan Daraktan kamfanin da ke haɗin gwiwa da gwamnatin jihar, Kafilu Abdulkadir, ya ce irin wannan tsari da aka fara amfani da shi a Jihar Legas a shekarar 2007 ya taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa ta hanyar samar da wuraren ajiye manyan motoci.

Abdulkadir ya bayyana cewa za a gina babbar tashar ajiye manyan motoci a Daka Tsalle, yana mai cewa sama da manyan motoci 3,000 ne ke shiga Kano a kullum.

Ya ce tashar na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoson ababen hawa a manyan hanyoyin shiga birnin Kano.

CIKIN HOTO Ademola Adeleke Ya Gabatar Da Takardar Shaidar Nasararsa Ga Shugaba Tinubu A Fadar Shugaban ƘasaGwamnan Jihar...
20/08/2026

CIKIN HOTO

Ademola Adeleke Ya Gabatar Da Takardar Shaidar Nasararsa Ga Shugaba Tinubu A Fadar Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gabatar da takardar shaidar komawarsa kan kujerar gwamna ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Adeleke, wanda ya sake lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, ya isa Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 5:20 na yamma.

Bayan isowarsa, Gwamna Adeleke ya nufi ofishin Shugaban Ƙasa kai tsaye, inda s**a gudanar da ganawar su.

An gudanar da ganawar ne bayan da hukumar zaɓe ta tabbatar da nasarar Adeleke a zaɓen, wanda ya ba shi damar ci gaba da jagorantar Jihar Osun na wa’adi na biyu.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HAUSA LEADS News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share