03/07/2026
Mataimakin Kwamandan hukumar Mujahideen Aminundeen ne ya sanar da Kamen a wani sakon murya da ya aikowa Global Tracker.
Ya ce Hisbah ta mika wanda ake zargin da kuma 'yan Matan biyu Fatima Safiyanu 'yan Shekaru 23, Yar Asalin garin Daura a Jihar Katsina da kuma Asiya Haruna 'yar Shekaru 11 daga garin Kazaure a Jihar Jigawa duk an mika su ga hukumar yaki da Safarar Bil'adama ta kasa NAPTIP domin fadada bincike.