26/09/2025
Mafarki Da Gaskiyar Rayuwa:
Kuri’ata Makamina – Gwagwarmayar Gyara Ƙasa
Jiya bayan mun tattauna da jama’a kan yadda za mu ci gaba da gwagwarmayar siyasa domin kawo gyara ta tsarin Kuri’ata Makamina, sai na yi mafarki da ya ƙara tabbatar min da cewa tafiyarmu tana da nasaba da alheri.
A mafarkin, mun wuce mu uku muka ga wani mutum yana kwaba yashi da cement domin a yi flow a gaban masallacin Juma’a a wani kauye. Amma abin da yake yi ba daidai ba ne – yashi ya yi yawa, gauraya ta baci, kuma aikin bai da nagarta. Har ma daga cikin wannan yashin marar amfani ya shiga cikin masallaci, wato cikin wuri tsarkaka da jama’a ke taruwa.
Sai muka tsaya muka gaya masa cewa idan ya yi mix a inda za a yi flow, zai fi kyau kuma aikin zai dore. Mun karɓa muka gyara masa, muka nuna yadda za a yi daidai.
Fassarar Saƙo:
Wannan mafarki alama ce cewa tsarin ƙasarmu da siyasar mu an riga an gauraya shi da kura-kurai, rashin gaskiya, da rashin adalci. Amma al’umma – wato masallacin Juma’a – shi ne ke ɗaukar nauyin wannan kuskuren.
Aiki ne na gwagwarmaya irin ta Kuri’ata Makamina ya gyara wannan mix ɗin, ya dawo da daidaito, ya tabbatar da cewa aikin da ake yi domin jama’a ana yi shi da gaskiya da nagarta.
Kira ga Jama’a:
Ku tashi mu gyara wannan kasa. Mu daina bari a yi mana kwaba da yawa da ba daidaito ba. Mu tsaya mu nuna hanyar da ta dace. Wannan shi ne manufar Kuri’ata Makamina – Kuri’ata shine makamin gyara ƙasarmu.