10/09/2026
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta kira Mashigar Hormuz da "Mashigar Trump," sannan ya ƙara da cewa Amurka na "samun nasara" a yaƙin da take yi da Iran.
"Farashin mai (zai ragu) da zarar mun yi nasara a yaƙin da muke yi da Iran, wanda ke gudana a yanzu. Za mu ci nasara," a cewar Trump a yayin gangamin yaƙin neman zaɓe na tsakiyar wa'adi na Jam'iyyar Republican a birnin Dallas na Texas.
"Muna samun nasara a kansu. Mu za mu riƙa iko da harkokin cinikayyar Hormuz. Ina ganin ya kamata mu kira Mashigar Hormuz da suna Mashigar Trump. Ya kamata na samu wani abu daga ciki. Mashigar Trump.
"Za a kira ta da sunanan, jama’a maza da mata, zan yi sanarwa - za mu kira ta Mashigar Trump, kuma ina da tabbacin shugabannin Iran za su fusata da hakan," in ji shi.
Trump ya kare yaƙin Iran sosai, yana mai ikirarin nasara da kuma danganta hakan da samun ragi a farashin mai.
"Farashin abinci da kusan duk wani abu suna raguwa cikin sauri. Kuma a zahiri, mai zai ragu da zarar mun yi nasara a yaƙin da muke yi da Iran, wanda ke gudana a yanzu," in ji Trump.
Trump ya jaddada abin da sauran 'yan Republican s**a faɗa a taron, yana mai cewa guguwar gurguzu ce ke barazana ga Amurka.
"Za ta zama ƙasar gurguzu idan s**a yi nasara," in ji shi.
"Ƙuri'arku za su yanke hukunci ko ƙasarmu za ta faɗi a ƙofar babin farko na shekaru 250 masu zuwa ko kuma ta yi gaba kuma ba za ta taɓa waiwaya baya ba," in ji shi.
Haske Radio Online.