17/09/2025
Babu ruwan ubangiji da halin da Nigeria take ciki. Bai zama lallai sai ka yarda ba, saboda haka zaka iya fassara wannan rubutun duk yadda kake so. Ina da tabbacin sai na samu matsala da mutane da yawa a wannan rubutun. Amma koda zaka dena min magana sai na faɗa maka gaskiya 🫵. Duk abinda kake tunani saida nayi nazari mai faɗi ta kowacce irin fuska sannan nayi bincike daidai fahimta ta ga rayuwa sannan nayi wannan rubutun. Abinda yasa nayi rantsuwa cewa "Babu ruwan ubangiji da halin da Nigeria take ciki" shine:
Na farko duk wani abu daka sani a duniya tun daga kan Natural resources, intensive population, highly recommended naturally talented individuals, very productive fertile agricultural lands da sauran duk wani abu da ake buƙatar ɗan adam ya rayu da shi har yau ɗin nan Nigeria ce a gaba a duk faɗin ƙasashen Afrika 54 tunda aka shata duniya. Babu wani abu a duniya da wani mutum zai nuna a Europe, Asia, American ko Australian continent wanda Allah bai ajiye shi ba a Nigeria. Akwai wani great philosopher Adam Smith wanda ya taɓa cewa, "da ace za'a tambaye shi a ina ubangiji yake zaune a duniya zai ce wallahi a Nigeria yake". Duk wata ƙasa daka san ta cigaba a duniya sai da ta nemi haɗin gwiwa da tattalin arzikin Nigeria directly or indirectly. Google it idan baka yarda dani ba.
Dubai daka ke ji cewa ita ce ƙasa mafi more abubuwan jin daɗin rayuwar da ɗan adam yake buƙata yau a duniya, to a 1960 ko jihar Jigawa ma tafi ta cigaba ta kowacce irin fuska duniya da lahira idan baka sani ba. Titunan da suke ƙasar Saudi Arabia yau a duniya, a 1960 ko rabin titunan da suke ƙwaryar garin Kaduna ma basu da shi. Manyan gine-ginen da kake jin labarin su a kasar Singapore wanda yanzu itace ƙasa ta 4 a tattalin arziki a duniya, to a 1960 ko Jihar Lagos ta fita cigaba a duniya. Kar ka yarda da abinda na faɗa maka. Google it.
Amma kullum kana zaune kana ɗorawa ubangiji laifi tare da yin addu'o'i marasa fa'ida da sunan Tauhidi wai "Allah ya gyara mana Nigeria". Ko Ni nan ka isa na daga darajar ka ta kowacce irin fuska a duniya kuma ka dawo ka ɗora min alhakin abinda ba Ni bane da haƙƙin sa - na saurare ka?🙄. Am I playing with you?. Allah da kansa sai da yace "wallahi bazan taɓa gyara muku rayuwa ba har sai ku da kanku kun gyara kawunan ku tukunna". Kana zaune ne fa zaka ga wani mutum ko wani abokin ka wanda kake tunanin yayi karatu daidai gwargwado kuma ya samu tarbiyya daga nagartattun iyaye, amma haka kawai zaka hango shi yana tallata wasu d@bbobin 'yan siy@sa marasa tunani da alƙiblar rayuwar duniya da ta lahira a matsayin waɗanda ya riƙe alƙiblar sa.
Ƙarara fa Ni da kai ko kuma shi ɗin duk munsan mutanen b@nza ne j@hilai marasa tunani kuma f@jirai ta kowacce irin fuska ko a mizanin Allah, amma haka kawai saboda tsabar w@uta da j@hilci tare da zunzurutun talaucin zuciya dana alƙiblar rayuwa sai kaga mutum har rikici ana yi da shi wajen wai dole sai ya nuna maka cewa wane mutumin kirki ne kawai saboda abinda zai samu. Zuciyar sa bata taɓa nuna masa abinda zai biyo baya ga rayuwar 'ya'yan sa, iyayen sa ko al'ummar da zasu biyo baya koda shi ɗin ya tsallake. Don Allah wacce irin rayuwa kake tunanin zamu yi nan gaba idan bamu chanza ba. Kai dai ka sani cewa da ace addu'a ce zata gyara Nigeria ba tare da mun chanza hali ba, ba yadda za'a yi a adalcin ubangiji ya bari mu riski wannan tsawon lokacin ace kullum muna cikin masifa. It's impossible kowanne irin Tauhidi ne da kai kasan ƙarya ne wallahi bazai yiwu ba.
Ni na fahimci inda rayuwa ta ta dosa in sha Allahu. Saboda haka ka fassara wannan rubutun da kowanne irin yare for your earliest convenience.
© Ameer Salihu Koko (RPHP, EMT)