26/07/2025
___MATAKAN TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI___
Matashiya:- Tarbiyya
Mawallafi:- Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Shekarar bugu:- 1446 / 2024
DARASI NA (1️⃣3️⃣)
1️⃣1️⃣. RASHIN NUNA BAMBANCI TSAKANIN 'YA'YANSA
Abin da ake nufi da adalci shi ne daidaita tsakanin 'ya'ya a abubuwan da bana dole ba, amma abin da ya danganci ciyarwa ko sutura to za a baiwa kowanne yaro gwargwadon abin da yake bukata, ba zai yiwu a daidata tsakanin yaron da yake shan nono da kuma wanda ya girma ba wajan cin abinci.
Magabata nagari sun kasance abin koyi wajan adalci tsakanin 'ya'yayansu, suna son ayi adalci har a wajan sumbantar yara, da kuma daukarsu a rungume, ana bukatar adalci a wajan mu'amala da ukuba da kyauta da kuma wasa.
Ba ya halatta a kebance daya daga cikin yaran da wata kyauta a bar dayan, Nu'uman dan Bashir ya rawaito cewa; mahaifinsa Bashir ya yi masa kyauta, sai ya kira Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi don ya zama shaida, sai ya ce masa duka yaranka ka yi musu irin wannan kyautar, sai ya ce a'a, sai ya ce masa "Ku ji tsoran Allah, ku yi adalci a tsakanin'ya'yayanku, sai ya dawo ya janye wannan kyautar".
A wata riwayar yake cewa: "Ba zan yi shaida akan zalunci ba".
Shalabi ya ambata a cikin littafinsa na tarihi, dalilin da ya jawo fitina tsakanin 'ya'yan Haruna Arrashid, wato Ma'amun da Al'amin, har yaki ya turu atsakaninsu, duk da cewa dukkansu sun haddace Muwadda Malik.
Ma'amun da ne ga sanannen halifan Musulunci Haruna Ma'ahid, wanda aka kammala wallafa Muwadda Malik a zamaninsa, sai dai mahaifiyarsa Marajir baiwa ce, wannan yasa duk da cewa ya girme wa kaninsa Al'amin da watanni shida, amma mahaifinsu ya gabatar da Al'amin a matsayin wanda zai fara gadarsa a halifancin Musulunci,, kafin Ma'amun, saboda shi Al'amin mahaifiyarsa Zubaida 'ya ce kuma jinin sarauta.
Wannan hukuncin da babban Halifa ya yanke, ya fusata Ma'amun, wannan yasa ya yaki dan'uwansa tsawon lokaci, har sai da ya ci galaba akansa, ya saro kansa ya dire shi a gaban mahaifiyar Al'amin, shi kuma ya dare kan gadon sarauta, duka wannan ya faru ne sakamakon nuna bambanci tsakanin 'ya'yaye.
Sai dai akwai abubuwan da suke iya sanyawa a bambanta tsakanin wasu yaran da wasu, kamar hana wani daga cikinsu wani abin saboda ya yi laifi, ko kuma a yiwa wani sakayya saboda ya yi abin kirki, ko kuma wani yana da bukata ta musamman, saboda bai da shi ko kuma yawan iyali, haka nan mara lafiya ana iya bambanta shi da mai lafiya, gurgu a cikinsu ana iya ba shi kulawa ta musamman sama da mai kafa.
Sai dai yana da kyau iyaye su yi wa ragowar yaran bayani cikin hikima da tausasawa, ta yadda za su fahimta cikin sauki.
Hidayatul Khair Da'awa ✍️