Amarawa Media

Amarawa Media News & Current Affairs and many more

01/09/2026

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ADC Alh. Atiku Abubakar ya lashi takobin yi wa hukumar bada rancen karatu ga ɗaliban manyan makarantun ƙasarnan NELFUND garambawul, tare da yafewa ɗaliban da s**a karɓi rancen a baya.

News & Current Affairs and many more

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gayyaci Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma tsohon minista ...
01/09/2026

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gayyaci Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma tsohon minista a gwamnatin marigayi shugaba Muhammadu Buhari, domin amsa wasu tambayoyi bisa ɓatan dabon sama da dala miliyan 14 a ma'aikatar da ya riƙe.

Ƙungiyar Jama'atu Nasrul Islam JNI ta barranta kan ta da yunƙurin kafa Hisbah a jihar Plateau
01/09/2026

Ƙungiyar Jama'atu Nasrul Islam JNI ta barranta kan ta da yunƙurin kafa Hisbah a jihar Plateau

Bikin Takutaha ana gudanar dashi ne a kowace ranar 19 ga watan Rabi'ul Awwal, inda mabiya ɗariƙu da dama ke shirya shagu...
01/09/2026

Bikin Takutaha ana gudanar dashi ne a kowace ranar 19 ga watan Rabi'ul Awwal, inda mabiya ɗariƙu da dama ke shirya shagulgula iri daban-daban a matsayin murnar ranar sunan Ma'aiki SAW.

Tuni dai gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alh. Abba Kabir Yusuf ta ayyana ranar Talata 1 ga watan Satumba, 2026 a matayin ranar hutu domin karramawa ga ranar.

Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kori wasu jami'an ta 40, bisa zargin rashawa.Shugaban h...
01/09/2026

Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kori wasu jami'an ta 40, bisa zargin rashawa.

Shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ce matakin ya zama wajibi domin tsaftace ayyukan hukumar

Gwamnatin jihar Kano ta kawo ƙarshen tirka-tirkar filaye dake tsakanin jami'ar Bayero da al'ummar yankin Rimin Zakara.Ri...
31/08/2026

Gwamnatin jihar Kano ta kawo ƙarshen tirka-tirkar filaye dake tsakanin jami'ar Bayero da al'ummar yankin Rimin Zakara.

Rikcin dai ya shafe kimanin shekaru 50 tsakanin ɓangarorin biyu, inda gwamnatin jihar Kano ta kawo ƙarshen sa bayan biyan diyyar filayen ga mamallakan su na asali.

Gwamnatin shugaba Tinubu ta Muslim Muslim na cigaba da karɓar luguden hamayya daga madugun ƴan adawar ƙasar Alhaji Atiku...
29/08/2026

Gwamnatin shugaba Tinubu ta Muslim Muslim na cigaba da karɓar luguden hamayya daga madugun ƴan adawar ƙasar Alhaji Atiku Abubakar.

Ko me ya jawo hakan, kuma ya zata kaya?

Ana raɗe-raɗin cewa an yi yunkurin yin juyin mulki a jamhuriyar Nijar a ranar Asabar 29 ga Agustan 2026
29/08/2026

Ana raɗe-raɗin cewa an yi yunkurin yin juyin mulki a jamhuriyar Nijar a ranar Asabar 29 ga Agustan 2026

Fuskokin wasu daga cikin gwamnonin da s**a yabawa Sheikh Jingir kan tallan Muslim-Muslim
28/08/2026

Fuskokin wasu daga cikin gwamnonin da s**a yabawa Sheikh Jingir kan tallan Muslim-Muslim

Shugaba ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin tantance ma'aikatun tarayya, domin tabbatar da sahihanci da kuma ingancin...
28/08/2026

Shugaba ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin tantance ma'aikatun tarayya, domin tabbatar da sahihanci da kuma ingancin ayyukan su.

Address

Kano
63522

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amarawa Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share