Halacci Online TV -HTV

Halacci Online TV -HTV Hallaci is an online TV which aims is to promote cultural values, commerce, politics and tackle insec

MAI RABA AL'KHAIRI SHIMA YA RABAUTAShugaban ƙwamatin raba tallafi da bada Jari na Jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Tudun ...
29/08/2026

MAI RABA AL'KHAIRI SHIMA YA RABAUTA

Shugaban ƙwamatin raba tallafi da bada Jari na Jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Tudun Wada, ƙarƙashin jagorancin RT Hon Doguwa, Mallam Garba Najume, yau shima ya rabauta da kyautar Moto kirar Camry daga wajan Sardaunan ƙasar Hausa maituta, RT Hon Alhassan Ado Doguwa wakilin ƙananan hukumomin Tudun Wada/Doguwa a zauren majalisar tarayya.

Dino Melaye ya yi barazanar maka shugaban hukumar haraji a kotu saboda samun gurbi a kwamitin  kamfen na TinubuTsohon Sa...
24/08/2026

Dino Melaye ya yi barazanar maka shugaban hukumar haraji a kotu saboda samun gurbi a kwamitin kamfen na Tinubu

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce zai maka Shugaban Hukumar Harajin Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, a kotu kan mukamin da aka ba shi a Kwamitin Kamfen na Shugaban Ƙasa na APC na zaɓen 2027.

Melaye, wanda ke cikin shugabannin jam’iyyar ADC a Kogi, ya ce akwai yiwuwar samun rikicin muradun aiki, ganin cewa Adedeji ma’aikacin gwamnati ne kuma aka nada shi Mataimakin Daraktan tara kudaden kamfen Tinubu.

Ya kuma soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na jagorantar kwamitin kamfen dinsa da kansa, yana mai cewa hakan na nuna rashin amincewa da wasu shugabannin APC.

Melaye ya ce zai garzaya kotu domin a tantance ko nadin Adedeji ya dace da dokokin aikin gwamnati da ka’idojin da’a na ma’aikatan gwamnati.

A jerin kwamitin kamfen da APC ta fitar, Tinubu ne Shugaban Kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa Nentawe Yilwatda s**a kasance Mataimakan Shugaban Kwamitin. An nada tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, Darakta-Janar, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama Sakatare.

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shi ne Daraktan Tara Kudaden Kamfen, yayin da Zacch Adedeji aka nada Mataimakinsa.

Gawuna Campaign Coordinating Team, (GCCT) ya kaddamar da Shuwagabannin kananan Hukumomi goma shabiyar ( 15 _ LG) dake ka...
24/08/2026

Gawuna Campaign Coordinating Team, (GCCT) ya kaddamar da Shuwagabannin kananan Hukumomi goma shabiyar ( 15 _ LG) dake kano ta tsakiya, a Karkashir jagorancin tsohon Kwamishina Hon. Saleh Adamu Kwaru,

An Gudanar da taron a Babban Ofishin yakin Neman zaben Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya H.E Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Kunga fuskokin jiga-jigan tafiyar Gawuna ?

Sojoji sun k**a mutane uku da ake zargi da safarar mak**ai tare da ceto mutane shida a Zamfara Rundunar Sojin Najeriya t...
24/08/2026

Sojoji sun k**a mutane uku da ake zargi da safarar mak**ai tare da ceto mutane shida a Zamfara

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun k**a wasu mutane uku da ake zargi da safarar mak**ai a Jihar Zamfara, tare da kwato bindigar AK-103-2 guda daya da harsasai 30.

An k**a wadanda ake zargin ne a ranar Lahadi yayin wani samame na tsayawa da bincike da sojoji s**a gudanar a kan hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi.

Rundunar ta ce an boye bindigar da harsasan ne cikin buhun gero da ke cikin wata motar Golf Wagon.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutanen da safarar makamin zuwa Yar-Galadima da ke karamar hukumar Maru, inda aka shirya kai shi ga wani mutum mai suna Tijjani Goguwa.

Sojojin sun ce wadanda ake zargin, makamin da aka kwato da motar an tsare su domin ci gaba da bincike da daukar matakin doka.

A wani samame na daban a jihar, dakarun Sojin Najeriya sun ceto mutane shida bayan wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan wata mota a yankin Gadan Manya, a kan hanyar Anka zuwa Gummi.

Rundunar ta ce sojojin sun isa wurin cikin gaggawa bayan sun gano harin, inda s**a fatattaki ‘yan ta’addan tare da ceto mutanen shida da suke kokarin tilasta musu shiga cikin daji.

An kai wadanda aka ceto zuwa Babban Asibitin Anka domin samun kulawar lafiya. Mutane uku daga cikinsu sun samu kananan raunuka, amma suna cikin koshin lafiya.

Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin kokarin dakile safarar mak**ai da kayan tallafin ‘yan ta’adda, tare da kare fararen hula da masu amfani da manyan hanyoyi a yankin.

Gwamnatin Sokoto ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga iyalan wadanda hare-haren ‘yan bindiga da hadarin kwale-kwale...
24/08/2026

Gwamnatin Sokoto ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga iyalan wadanda hare-haren ‘yan bindiga da hadarin kwale-kwale ya shafa

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da tallafin sama da Naira miliyan 100, tare da buhunan kayan abinci guda 408, ga iyalan mutanen da hare-haren ‘yan bindiga da hadarin kwale-kwale ya shafa a kananan hukumomin Wurno da Goronyo.

Tawagar gwamnatin jihar karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC na jihar, Sanata Aliyu Wamakko, ta kai ziyara ga iyalan wadanda abin ya shafa domin jajanta musu.

A Dinawa, iyalan mutane bakwai da ‘yan bindiga s**a kashe sun samu Naira miliyan daya kowanne, da buhunan masara biyu, gero biyu da shinkafa daya. Mutane biyar da s**a samu raunuka kuma sun samu Naira 250,000 kowanne da kayan abinci.

Haka kuma, a Birjingo, iyalan mutane uku da aka kashe sun samu Naira miliyan daya kowanne da kayan abinci, yayin da mutane shida da s**a jikkata s**a samu Naira 250,000 kowanne.

A Gorau, inda mutane 65 s**a rasa rayukansu sak**akon hadarin kwale-kwale, gwamnatin ta bai wa kowane iyalin mamacin Naira miliyan daya, tare da buhunan masara biyu, gero biyu da shinkafa daya.

Da yake magana yayin ziyarar, Wamakko ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin dakile matsalar rashin tsaro. Ya kuma bukaci al’ummomin karkara su rika hada kai da jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan bindiga.

A Gorau, Wamakko ya sanar da umarnin Gwamna Ahmed Aliyu na daina cika kwale-kwale da fasinjoji fiye da kima, domin rage yawan hadurran kwale-kwale da asarar rayuka a yankin.

Gwamnatin ta kuma jajanta wa al’ummar Tsamaye a karamar hukumar Sabon Birni bisa rasuwar shugaban APC na yankin, Alhaji Amadu Malale.

Dawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya — Mohammed IdrisMinistan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Moha...
24/08/2026

Dawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya — Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Najeriya cikin matsalolin tattalin arzikin da ta fuskanta kafin cire tallafin.

Idris ya ce matakin cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka ya taimaka wajen samar da karin albarkatun da aka raba tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya ce a shekarar 2022, Najeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin man fetur, a lokacin da kasar ke fama da raguwar samar da danyen mai da karancin kudaden shiga.

Ministan ya bayyana cewa bayan cire tallafin, an samu tanadin Naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 da Disambar 2025, wanda ya kara yawan kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati.

A cewarsa, daga cikin kudaden, kusan Naira tiriliyan 5.43 sun samu ne ga Gwamnatin Tarayya, yayin da jihohi s**a samu Naira tiriliyan 6.52, sannan kananan hukumomi s**a samu Naira tiriliyan 3.88.

Ya ce karin kudaden da jihohi da kananan hukumomi s**a samu ya taimaka musu wajen biyan albashi da fansho, tare da kara zuba jari a fannonin kiwon lafiya, ilimi, tituna da sauran ayyukan more rayuwa.

Idris ya kuma ce karin damar kashe kudi da sauye-sauyen tattalin arzikin s**a samar ya taimaka wajen aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da manyan hanyoyi, gidaje, noma, sufuri da tsaro.

Ya ce sama da gidaje miliyan 10 sun amfana da shirye-shiryen tallafin jin kai, yayin da gwamnatin ta kuma ware sama da Naira biliyan 400 ga wasu manyan shirye-shiryen tallafawa al’umma, ciki har da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).

Ministan ya ce sauye-sauyen sun kuma taimaka wajen farfado da kwarin gwiwar masu zuba jari, karuwar kudaden ajiyar waje da kuma habakar samar da danyen mai, wanda ya zarce adadin da kungiyar OPEC ta ware wa Najeriya a wasu lokuta.

Ya yi gargadin cewa sake dawo da tallafin man fetur a yanzu zai iya kawo cikas ga ci gaban da ake samu a bangaren man fetur, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke kara habaka matatun man cikin gida.

A cewarsa, idan aka koma tsarin tallafin da aka cire, matsalolin karancin man fetur, matsin lamba kan kudaden gwamnati da kuma cin hanci da rashawa da ke tattare da tsarin na iya sake kunno kai.

Ya ce Najeriya na fuskantar wani nau'in tallafin mak**ashi a bangaren wutar lantarki, wanda ya lakume Naira tiriliyan 3.14 tsakanin Yunin 2023 da Disambar 2025.

“Dawo da tallafin man fetur a kan wannan zai kara wa tattalin arzikin kasar wani babban nauyi,” in ji shi.

Idris ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jawo matsin rayuwa ga ‘yan Najeriya, amma ya ce mafita ba ita ce a mayar da tsarin da ya haifar da matsalolin tattalin arziki ba.

Ya ce abin da ya dace shi ne gwamnati ta kara kokarin ganin amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin ya kai ga jama’a ta hanyar samar da ayyukan yi, inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka.

Ministan ya ce muhawarar dawo da tallafin man fetur ta shafi zabi ne tsakanin ci gaba da amfani da kudaden gwamnati wajen tallafa wa amfani da man fetur ko kuma a karkatar da su zuwa ilimi, kiwon lafiya, tsaro, tituna, wutar lantarki da sauran ayyukan ci gaba.

Ya kara da cewa kungiyoyin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki sun yi gargadin cewa sauya manufar gwamnati na iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari tare da yin illa ga dorewar tattalin arzikin kasar.

“Najeriya ba za ta iya gina tattalin arzikin gobe ta hanyar komawa tsarin tallafin jiya wanda ba ya dorewa ba. Mun wuce wannan tsarin,” in ji Idris.

Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da kokarin sauya wahalhalun da sauye-sauyen s**a haifar zuwa ingantattun ayyukan gwamnati, karin damar tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

Bai k**ata yakin neman zaben 2027 ya kasance akan shaidar karatun Tinubu kadai ba — NdumeTsohon Shugaban Masu Rinjaye a ...
24/08/2026

Bai k**ata yakin neman zaben 2027 ya kasance akan shaidar karatun Tinubu kadai ba — Ndume

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya shawarci jam’iyyun adawa da su mayar da hankali kan manufofi da abubuwan da ‘yan Najeriya ke bukata yayin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027, maimakon ci gaba da magana kan takardun shaidar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ndume, wanda kuma jigo ne a jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Ya ce k**ata ya yi ‘yan takarar jam’iyyun adawa su bayyana irin manufofin tattalin arziki da tsare-tsaren da suke da su, tare da bayyana wa ‘yan Najeriya abin da za su iya yi fiye da gwamnatin Tinubu.

Sanatan ya ce batun cancantar Tinubu ya riga ya kasance cikin shari’o’i da dama da s**a biyo bayan zaben shugaban kasa na 2023, don haka bai k**ata ya zama babban jigon yakin neman zaben 2027 ba.

Ndume ya yi nuni da cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi cewa wanda zai tsaya takarar shugaban kasa dole ne ya kasance ya kai matakin karatu na School Certificate ko mak**ancinsa, kuma a cewarsa Tinubu ya cika wannan sharadi.

Ndume ya kuma bukaci Yan adawa da su mayar da muhawarar siyasa kan tattalin arziki, tsaro da ayyukan gwamnati, maimakon kai hari kan mutum ko takardunsa.

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), tare da jagorori d...
24/08/2026

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), tare da jagorori da ’yan jam’iyyar (APC) na Karamar Hukumar Bebeji, sun karɓi bakuncin shugaban Jam’iyyar (APC) na Jihar Kano, Hon. Haruna Doguwa, tare da Exco ɗinsa da tawagarsa a Kofa karamar hukumar Bebeji.

Kafin gudanar da taron, an tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban jam’iyya, haɗin kai da kuma tsare-tsaren tunkarar zaɓen shekarar 2027, domin tabbatar da nasarar APC daga sama har ƙasa, insha Allah.

Ko abokan adawa na shiri irin Abdulmumin Kofa ?

Yadda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika da wata babbar tawaga zuwa Jihar Kano domin jajantawa iyalan marigayi Al...
24/08/2026

Yadda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika da wata babbar tawaga zuwa Jihar Kano domin jajantawa iyalan marigayi Alhaji Hamza Darma, wanda ya rasu a farkon wannan makon.

Tawagar, wadda Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabiru Masari, ya jagoranta, ta samu tarba daga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya kasance babban mai masaukin baƙin.

A cikin tawagar akwai Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu; da Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, tare da wasu fitattun Ministoci da manyan jami’an gwamnati.

Abinda Nijeriya ta samu bayan cire tallafin mai ya kai Naira Tiriliyan 15.8 a shekaru 3Cire tallafin man fetur na daga c...
22/08/2026

Abinda Nijeriya ta samu bayan cire tallafin mai ya kai Naira Tiriliyan 15.8 a shekaru 3

Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauka tun bayan hawanta mulki a shekarar 2023. Duk da radadin da matakin ya haifar, sabon rahoton Nigeria’s Reform Scorecard ya nuna cewa ya samar da gagarumin karin albarkatun kudi ga Najeriya.

Tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025, an samu Naira tiriliyan 15.8 na tanadin kudaden da a baya ake kashewa wajen tallafin man fetur. Daga cikin wannan kudi, an raba wa jihohi da kananan hukumomi Naira tiriliyan 10.4, yayin da Naira tiriliyan 5.4 s**a samu shiga Gwamnatin Tarayya.

Wannan karin kudade ya kara wa gwamnati damar daukar nauyin muhimman bukatun kasa. A bangaren tarayya, karin albarkatun ya taimaka wajen daukar nauyin karin albashi da alawus-alawus, biyan basuss**a da kuma zuba jari a manyan ayyukan more rayuwa.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kudaden da aka samu ba su tsaya a matsayin adadi a takarda ba. An yi amfani da wani bangare wajen tallafawa sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000, ayyukan more rayuwa, tallafin jama’a da sauran shirye-shiryen da s**a shafi rayuwar ’yan Najeriya.

Tabbas, cire tallafin mai ya zo da tsadar da ’yan Najeriya s**a ji sosai. Amma manufar gyaran ita ce a mayar da kudaden gwamnati daga tsarin da ba ya dorewa zuwa ayyukan da za su amfani kasa na dogon lokaci. Naira tiriliyan 15.8 da aka samu na tanadi na daga cikin alkaluman da ke nuna girman sauyin da wannan gyara ya kawo wa tsarin kudaden Najeriya.

Address

103 Sky Complex
Kano
9333

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Halacci Online TV -HTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category