20/09/2025
BA ZAKU DAWO AFGHANISTAN BA....
Gwamnatin Taliban a Afghanistan tayi watsi da batun neman dawowar sojojin Amurka zuwa babban sansanin sojojin sama na Bagram dake kusa da birnin Kabul,
Kakakin Hukumar harkokin kasashen waje na Afghanistan Malam Zakir Jalal shine ya fitar da sanarwa a shafinsa na Twitter cewa Afghanistan ba zata taba amincewa Amurka ta sake dawowa zuwa cikin kasarta ba..
Tun da farko an jiyo shugaba Trump yana bayyana cewa Amurka ta kusa sake komawa zuwa sansanin soji na Bagram dake Afghanistan saboda sanya idanu akan ayyukan Nukiliya na kasar China, domin daga Bagram zuwa yankin da China ke ayyukan Nukiliya baifi nisan tafiyar awa daya ba, don haka ya zama lallai ga Amurka ta sake komawa cikin Afghanistan domin ayyukan sanya ido da leken asiri akan kasar China...
Taliban sunce da karfin tuwo s**a kwaci Afghanistan ciki harda sansanin sojojin Bagram wanda ke kusa da Kabul, don haka babu wata kasa a duniya da ta isa ta zare musu idanu suyi abun da basuyi niyya ba, duk da cewa tabbas suna bukatar yin hulɗar kasuwanci da kasar Amurka amma fa cikin mutumta juna ba wai bisa nuna isa ba...
Tun dai a shekarar 2021 Taliban ta sake karbe ragamar gwamnatin kasar Afghanistan bayan da sojojin Amurka da Nato s**a tattara kayansu s**a gudu sakamakon mamayar da Taliban tayi a lokacin, Amurka ta gudu daga Sansanin Bagram inda ta bar kayayyakin yaki masu yawa ciki har da jiragen saman yaki...
Shi dai Trump yace dole yana son sansanin Bagram su kuma Taliban sunce uban kuturu yayi kadan....