Alheri TV

Alheri TV Sabuwar Tasha ce ta Hausa da za ta dinga yin shirye shirye Kala Kala, da kuma sabbin sahihan labarai na nishadi da ilmantarwa domin ta zamo ALHERI TV

19/09/2026

Nagge dadi goma

Hukumar Hisbah ta yaba wa wani direban Adaidaita Sahu mai suna Atamma Madugu, bayan ya taimaka wajen mika wani fasinjans...
18/09/2026

Hukumar Hisbah ta yaba wa wani direban Adaidaita Sahu mai suna Atamma Madugu, bayan ya taimaka wajen mika wani fasinjansa ga hukumar, bayan da ya gano cewa mutumin yana dauke da abin da ake zargi da giya

Rahotanni sun bayyana cewa Atamma Madugu ne ya gano abin da fasinjan yake dauke da shi a lokacin da yake gudanar da aikinsa na jigilar mutane.
Bayan ya fahimci lamarin, direban ya yanke shawarar kai mutumin ga Hukumar Hisbah, maimakon ya kyale shi ya ci gaba da tafiya da abin da yake dauke da shi.

Saboda wannan mataki da ya ɗauka, Hukumar Hisbah ta yaba da halin da direban ya nuna, musamman yadda ya taimaka wajen hana abin da ake zargin laifi faruwa.

A matsayin nuna godiya da ƙarfafa gwiwa, hukumar ta bai wa Atamma Madugu kyautar Alƙur’ani mai girma guda ɗaya da kuma Naira 5,000.

Tsohuwar matar Adam A Zango Maimuna Musa ta bayyana hakanne a shafinta na sada zumunta inda ta rubuta cewa "Yau 15 ga wa...
15/09/2026

Tsohuwar matar Adam A Zango Maimuna Musa ta bayyana hakanne a shafinta na sada zumunta inda ta rubuta cewa "Yau 15 ga watan Satumba, 2026, na kammala iddata. Ina gode wa Allah da Ya bani ƙarfi da hakurin tsallake wannan lokaci.

A yau, na zabi in bar duk abin da ya wuce a matsayin darasi. Na yafe daga zuciyata, kuma ina roƙon Allah Ya yafe mana kura-kuranmu.

Ga tsohon mijina, ina maka fatan alheri da zaman lafiya a duk inda rayuwa ta kai ka. Allah Ya albarkaci rayuwarka, Ya ba ka farin ciki da kwanciyar hankali, Ya kuma shiryar da mu baki ɗaya zuwa ga abin da Ya yarda da shi.
Allah Ya sa abin da ke gaba ya fi abin da Ya wuce kyau, Ya bude mana kofin rahama da alheri."

Shin me zaku ce?

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba a zango na biyu na shekarar 20...
15/09/2026

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba a zango na biyu na shekarar 2026, inda GDP ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100, sama da kashi 3.89 da aka samu a zango na farko.

Hukumar ta kuma nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da raguwa. A rahoton CPI na watan Yuli 2026, hauhawar farashin kayayyaki ta koma kashi 15.43 cikin 100.

Sai dai, duk da wannan ci gaban da ake gani a alkaluman tattalin arziki, wasu masana tattalin arziki sun bayyana cewa har yanzu ba a samu cikakken sauƙin rayuwa ga mafi yawan ‘yan Najeriya ba.

Shahararren ɗan kasuwar Najeriya kuma attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa bai damu da rashin samun ɗa namij...
15/09/2026

Shahararren ɗan kasuwar Najeriya kuma attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa bai damu da rashin samun ɗa namiji ba, yana mai cewa ’ya’yansa mata suna yi masa duk abin da yake buƙata.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan iyalinsa da kuma yadda yake kallon ’ya’ya, inda ya nuna cewa a wurinsa muhimmiyar magana ita ce tarbiyya, nagarta da kuma yadda ’ya’ya suke amfani da damar da Allah Ya ba su.

Innah Lillahi Wa Innah Ilaihirraji’un! Allah yayiwa Hajiya Hadiza Umar Soja Rasuwa Yanzu.Allah yayi Mata Rahama Dan Isar...
15/09/2026

Innah Lillahi Wa Innah Ilaihirraji’un!

Allah yayiwa Hajiya Hadiza Umar Soja Rasuwa Yanzu.

Allah yayi Mata Rahama Dan Isar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam

15/09/2026

Matar Kauye sabon shiri

Alheri tv mun shirya tsaf domin kawo muku alheri har cikim gidajenku.Alheri Tv farincikin Maikallo, muna marhabun da maa...
15/09/2026

Alheri tv mun shirya tsaf domin kawo muku alheri har cikim gidajenku.
Alheri Tv farincikin Maikallo, muna marhabun da maau kawo mana tallace tallace

Wani mutum da ’yan sanda ke nema ruwa a jallo a Amurka ya sake aika musu da hotonsa da kansa, saboda bai ji daɗin yadda ...
15/09/2026

Wani mutum da ’yan sanda ke nema ruwa a jallo a Amurka ya sake aika musu da hotonsa da kansa, saboda bai ji daɗin yadda hoton da ’yan sandan s**a wallafa ya fito ba.

A shekarar 2016, ’yan sanda a jihar Ohio sun wallafa hoton Donald “Chip” Pugh, domin neman taimakon jama’a wajen gano shi. Bayan Pugh ya ga hoton, sai ya aika musu da wani sabon hotonsa sanye da tabarau da rigar kwat.

A cikin saƙonsa, Pugh ya ce: “Ga wani hoto mafi kyau, wancan hoton bai yi kyau ba.” Abin mamaki, ’yan sandan sun saka sabon hoton a cikin sanarwar neman sa, tare da yin barkwanci kan taimakon da ya ba su.

Lamarin ya bazu a kafafen sada zumunta, inda mutane s**a yi ta mamakin yadda mutumin da ake nema ya fi damuwa da kyawun hotonsa fiye da ɓoye kansa.

Yayin da yawancin waɗanda ake nema ke ƙoƙarin guje wa a gane su, Pugh kuwa ya tabbatar da cewa za a gane shi amma da hoton da yake ganin ya fi kyau.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne wanda ya kafa rukunin jami’o’in MAAUN. Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jankad...
14/09/2026

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne wanda ya kafa rukunin jami’o’in MAAUN.

Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jankado, ne ya sanar da wannan naɗi a wajen bikin Ranar Hausa ta Duniya na shekarar 2026, wanda aka gudanar a birnin Paris.

Address

No. 7 Gidan Alhaji Ado, U/Dabai Street Kano
Kano

Telephone

+2348088827172

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alheri TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share