07/12/2024
KU YAƊA AMINCI BAYIN ALLAH
Allah Subhanahu wa ta'ala Ya ce a ce wa bayinSa: "...kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah". Suratuz Zumar, aya ta 53.
Annabi Ya'aƙub a.s ya ce ga 'ya'yansa: "Kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah". Suratu Yusuf, aya ta 87.
Annabi Yusuf a.s ya ce ga ɗan'uwansa: "... kada ka damu da abinda suke aikatawa". Suratu Yusuf, aya ta 69.
Nagartaccen bawan nan baban 'yammatan nan guda biyu ya ce ga annabi Musa a.s lokacin da ya ba shi labarinshi: "kada ka ji tsoro". Suratul Ƙasas, aya ta 25.
Fiyayyen halitta sallallahu alaihi wa sallam ya ce ga sahibinsa lokacin da suke cikin kogo: "kada ka damu, lalle Allah Yana tare da mu". Suratut Tauba, aya ta 40.
Yaɗa aminci da kwantar da hankulan musulmi lokacin da ake halin damuwa da ɗar-ɗar tsari ne na shari'a kuma tarbiyya ce ta annabta.
Dan haka bayin Allah mu kwantar wa da juna hankali, mu tunatar da juna mafita, mu ba wa juna shawarwari, sannan mafi muhimmanci mu yadda da cewa Allah ne Mai yi kuma zai yi da ikonSa.
🖊 Zainab Ja'afar Mahmud
2nd Jumadal-akhir 1446A.H
4th December 2024