Tsumagiya Tv/Redio

Tsumagiya Tv/Redio Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tsumagiya Tv/Redio, TV Channel, Gandun Gayawa Agantasa, Kano.

05/11/2025
29/09/2025

This version of Facebook uses less data and works in all network conditions.

Ranar Hausa ta Duniya. A yau Duniya ke gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda aka ware domin tunawa da harshen Ha...
26/08/2025

Ranar Hausa ta Duniya.

A yau Duniya ke gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda aka ware domin tunawa da harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa.

Masana harshen na yin kira da a ƙara amfani da Hausa a makarantu da kafafen yaɗa labarai domin kare harshen daga barazanar gushewa.

A wasu biranen Najeriya da ƙasashen waje, an saba gudanar da taruka, gasar waƙoƙi da tattaunawa don murnar wannan rana.

Ku rubuta mana karin maganar da kuka iya da Hausa…

Da Dumi-dumi:Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin shirya bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kaiGwa...
25/08/2025

Da Dumi-dumi:

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin shirya bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai

Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, ta kaddamar da kwamitin shirya bikin zagayowar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a dakin taro na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, inda manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban s**a halarta.

A yayin jawabin sa, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, jajircewa da kishin ƙasa. Ya jaddada cewa bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai ba kawai biki ba ne na murna, har ma dama ce ta tunawa da tarihin ƙasa, haɗin kai da ci gaba.

Kwamishinan ya kara da cewa dole ne a tsara bukukuwan cikin salon da zai haɗa kowa da kowa, tare da nuna bambancin al’adu, nasarori da burukan Najeriya. Ya kuma tabbatar wa da kwamitin cewa ma’aikatarsa za ta bayar da cikakken goyon baya domin ganin an samu nasara.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin kuma mukaddashin sakatare ɗin dindindin na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Inuwa Idris Yakasai, ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano da ma’aikatar bisa amincewa da su. Ya yi alkawarin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru domin tabbatar da shiryayyen biki mai ɗaukar hankali, wanda zai fito da ruhin haɗin kai da ƙaunar ƙasa.

Bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, daraktoci daga ma’aikatun gwamnati, da kuma wakilan rundunonin tsaro irin su Sojoji, ’Yan sanda, Civil Defence, Hukumar Shige da Fice, da ƙungiyoyin fararen hula.

Ya kuke kallon wannan mataki? Musulman jihar Taraba sun haramta gudanar da 'party' a yayin bukukuwan aure
25/08/2025

Ya kuke kallon wannan mataki?
Musulman jihar Taraba sun haramta gudanar da 'party' a yayin bukukuwan aure

Da alama Ruben Amorim bazai iya buga gasar premier league ba!!Lokacin da kowane kocin Manyan kungiyoyin premier league S...
25/08/2025

Da alama Ruben Amorim bazai iya buga gasar premier league ba!!

Lokacin da kowane kocin Manyan kungiyoyin premier league Shida “Big Six” ya ɗauka kafin ya fara cin wasanni biyu a jere a Premier League:

🔴 Arne Slot – wasa 2
🔵 Pep Guardiola – wasa 2
⚪️ Thomas Frank – wasa 2
🔵 Enzo Maresca – wasa 5
🔴 Mikel Arteta – wasa 9

Amma dai Ruben Amorim bai taɓa yin nasara a wasanni biyu a jere ba cikin wasanni 29 na Premier League

Shin miye matsalar Ruben Amorim a United, ko Ruben Amorim zai iya nasara a gasar premier league?

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Kwamitin Wayar da Kai Kan Rajistar Masu Kada Kuri’aAn kaddamar da Kwamitin Ɗaukar Ma...
25/08/2025

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Kwamitin Wayar da Kai Kan Rajistar Masu Kada Kuri’a

An kaddamar da Kwamitin Ɗaukar Matakai na Musamman kan Rajistar Masu Kada Kuri’a a Dakin Taro na Ma’aikatar Fadar Gwamnati (Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar).

Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, wakilan ƙungiyoyin farar hula, da kuma wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe. An gudanar da wannan mataki ne domin ƙara ƙarfafa wayar da kan jama’a tare da karfafa shiga cikin aikin rajistar masu kada kuri’a da ke gudana a halin yanzu a faɗin ƙasar.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouq Ibrahim, ya bayyana cewa an kafa wannan kwamiti ne domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin rajista da tabbatar da cewa dukkan ‘yan kasa wanda s**a cancanta sun samu damar yin rajista kafin zabubbuka masu zuwa.

Ya ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati wajen zurfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da ingantattun zabubbuka ta hanyar ƙara yawan masu kada kuri’a.

Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gode wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ba shi damar shugabantar wannan kwamiti.

Ya ce, Ina mika godiya ta musamman bisa wannan daraja da amincewar da kuka nuna a gare mu. Mun tabbatar muku cewa ba za mu baku kunya ba. Na gode ƙwarai.

A cikin jawabansu daban-daban, mahalarta taron sun yaba da wannan shiri, tare da bada tabbacin goyon bayansu domin ƙara wayar da kan jama’a a birane da karkara.

Address

Gandun Gayawa Agantasa
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsumagiya Tv/Redio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category