23/09/2022
Na Tabbata Zan Dawo Da Najeriya Cikin Hayya Cinta, Idan Na Zama Shugaban Ƙasa ~ Bola Ahmad Tinubu
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Inuwar Jamiyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana da dukkan abin da ya k**ata domin ganin Najeriya ta samu cigaba na rayuwa idan aka Zaɓe shi a matsayin shugaban Najeriya.
Tinubu ya ce yana da hanyar da za ta sake ɗaukaka Najeriya da kuma kawo ci gaba ga kowa da kowa, ya ƙara da cewa “Zan iya tafiyar da hanya zuwa wadata, na san hanyar ilimi domin na yi imani da shi, na san hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro. ƙasar."
Sai dai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba shi damar yin aiki ta hanyar ba shi kuri’unsu.
Ya ce, “Za mu yi aiki tare ne domin ba za mu koma lokacin da ake tari ba, ba za mu bari a yi mulkin k**a karya ba.”